NAJERIYA A YAU: Halin Da Muke Ciki Bayan Rasa ‘Yan Uwanmu A Hadarin Kwale-Kwale A Sakkwato
Published: 19th, August 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
‘Yan uwan wadanda suka rasa rayukansu a hatsarin jirgin ruwa da ya faru a garin Kojiyo dake karamar hukumar Goronyo a jihar sakkwato sun samu kansu cikin damuwa.
Yayin da kalilan daga cikin wadanda abun ya rutsa dasu suka tsira da ransu, wasu da dama sun mutu, a gefe guda kuma an kasa gano inda sauran da abun ya rutsa dasu suke.
Wannan lamari ya tayar da hankulan jama’a, musamman ‘yan uwan waɗanda abin ya shafa, waɗanda yanzu ke cikin damuwa, jimami da rashin sanin makoma.
NAJERIYA A YAU: Dalilan Karyewar Farashin Hatsi A Kasuwanni DAGA LARABA: Yadda sinadaran dandanon abinci ke yin illa ga lafiyaShirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan irin halin damuwa da wadanda suka rasa ‘yan uwansu sakamakon kifewar kwale-kwale a garin Kojiyo dake jihar Sakkwato ke ciki.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: hadarin jirgi Hadarin jirgin ruwa Sakkwato
এছাড়াও পড়ুন:
Microsoft ya ƙwace shafukan wasu kamfanoni 340 a Najeriya
Kamfanin Microsoft ya sanar da ƙwace shafukan yanar gizo na wasu kamfanoni 340 a Najeriya bayan samunsu da laifin sarrafa fasahohin kamfanin ba bisa ƙa’ida ba, musamman satar bayanan mutane.
Sanarwar da Microsoft ya fitar ta ce matakin ya biyo bayan wani umarni da wata kotu a Amurka ta bayar tun a farkon wannan wata, wadda ta bai wa kamfanin damar ɗaukar matakin ladabtarwa ga waɗanda ke amfani da fasaharsa ba tare da izini ba.
An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB An tattauna yadda za a inganta walwalar malamai a GombeSteven Masada, mataimakin shugaban sashen lauyoyi na Microsoft da ke kula da laifukan intanet, ya bayyana cewa waɗannan kamfanoni sun ɗauki bayanan abokan hulɗarsu sama da 5,000, inda suka yi amfani da shafukan kutse domin samun bayanan sirri.
A cewarsa, ɗaya daga cikin shafukan da suka fi haddasa damuwa shi ne wani da ake kira Raccoon0356, wanda ke da mabiya fiye da 850 a manhajar Telegram. Wannan shafi ne ke bai wa wasu damar samun kayan aikin kutse don shigar bayanan sirri na Microsoft da wasu hukumomi.
Microsoft ya bayyyana Joshua Ogundipe, mazaunin Najeriya a matsayin wanda ke jagorantar wannan shafi da ke kan manhajar Telegram, kuma bai bayar da amsa a saƙon da aka aike masa ba, don ya kare kanshi game da ayyukan da kamfanin ya ce yana aikatawa.
Kamfanin na Microsoft ya ce ya gano yadda Joshua ya jima tare da ƙwarewa wajen satar bayanan mutane, inda a tsakanin 12 zuwa 28 ga watan Fabrairun wannan shekara, ya yi kutse a shafukan hukumomi sama da 2,300, mafi yawansu na Amurka.