Burkina Faso: Ba mu da bukatar Kodineta ta MDD a kasarmu
Published: 19th, August 2025 GMT
Mai magana da yawun gwamnatin Burkina Faso ya bayyana jiya litinin cewa ba su da bukatar kodinetan majalisar dinkin duniya a cikin kasarsu, biyo bayan wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya da ya zargi kasar da cin zarafin yara.
Kakakin ya ce a cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya samu kwafinta, cewa “Hukumomi a Burkina Faso ba su shiga cikin shirya rahoton na Majalisar Dinkin Duniya mai suna Rikicin Yara da Makamai a Burkina Faso ba, kuma ba a sanar da su sakamakon binciken kafin wallafa shi ba.
Gwamnatin Burkina Faso ta zargi Majalisar Dinkin Duniya da yin “zargin da ba su da tushe da kuma yin karya a cikin rahoton, ba tare da ambaton binciken da ya dace ko kuma hukuncin kotu ba.”
A baya dai Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da zargin “kisa, cin zarafi, da kuma sace yara” a yankin Sahel, da kuma daukar yara aikin soja.
Gwamnatin Burkina Faso na Kallon irin wadanann matakai matsayin wani salo na siyasa domin bakanta sunanta a duniya, wanda kuma yana da alaka ne da matsayar kasar kan batutuwa na kasa da kasa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Da Armenia sun kudiri aniyar kara bunkasa alakokinsu a dukkanin fagage August 19, 2025 Hamas da sauran bangarorin Falastinawa sun amince da shawarar tsagaita wuta August 19, 2025 DR Congo da mayakan M23 sun kasa cimma matsaya a yarjejeniyar Doha August 19, 2025 Araqchi: Iran Ba Za Ta Amince Da Sauyi A Kan Iyakokin Yankin Siyasa Ba August 18, 2025 Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Ce: Gwamnatin Mamayar Isra’ila Barazana ce Ga Tsaron Yanki August 18, 2025 Mataimakin Kwamandan Dakarun IRGC Ya Jadadda Cewa; Suna Sanya Ido Kan ‘Yan Sahayoniyya Da Magoya Bayansu August 18, 2025 Mai Ba Da Shawara Ga Kwamandan Sojojin Iran Ya Ce; Akwai Yiwuwar Sake Yaki, Don Haka Suna Cikin Shiri August 18, 2025 Shugaban Amurka Ya Ce: Yaki Tsakanin Iran Da Isra’ila Bai Kare Ba August 18, 2025 Trump Yace Zelensky Zai Kawo Karshen Yaki Da Rasha Tare Da Barin Batun NATO Da Crimea August 18, 2025 MSF Ta Ce Yawan Mutanen Da Suke Mutuwa A Gaza Sun Ninka Har Sau Uku Bayan Fara Aikin GHF August 18, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Majalisar Dinkin Duniya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Sudan Ta Ce: Babu Sulhu Da ‘Yan Tawayen Kasar Na Kungiyar Rapid Support Forces
Gwamnatin Sudan ta ce: Babu batun sasantawa da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces na kasar wadanda take daukansu a matsayin ‘yan tawaye
Gwamnatin Sudan ta yi watsi da shawarar sasantawa da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces (RSF) da kasashen kasashe masu shiga Tsakani suka gabatar, tana mai jaddada cewa, tana mutunta duk wani kokari da zai taimaka wajen kawo karshen yakin kasar, matukar dai ya mutunta diyaucin kasar da halaltattun hukumomin kasar.
Sa’o’i kadan bayan kaddamar da shirin na bangarori hudu masu shiga tsakani wanda ya hada da Masar, Amurka, Saudiyya, da Hadaddiyar Daular Larabawa, na kiran zaman lafiya a Sudan da kawo karshen yakin, dakarun kai daukin gaggawa sun kai hari kan tashar samar da wutar lantarki da ma’ajiyar man fetur da kuma filin jirgin saman Kenana na jihar White Nile da jiragen sama marasa matuka ciki.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi kira da a ba da sanarwar yin watsi da shirin, inda ta yi nuni da cewa, yaƙin na da nasaba da al’ummar Sudan, kuma za ta tunkare shi, ta kuma yanke shawara da kansa.
Wani mai sharhi kan al’amuran siyasa Youssef Abdel Manan ya shaidawa tashar talabijin ta Al-Alam cewa: “Kasashen hudu masu siga tsakani ba su da wani hakki, ko na hukuma, ko na dabi’a, ko na siyasa, ko na kasa da kasa, da zai sanya su zama masu kula da al’ummar Sudan.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kasashen Larabawa da na Musulmi na taron gaggawa kan harin Isra’ila a Qatar September 15, 2025 Hamas ta bukaci kasashen musulmi da na Larabawa su dauki mataki mai tsari kan Isra’ila September 15, 2025 Rabin Sojojin Isra’ila da suka ji rauni a yakin Gaza na fama da ciwon damuwa September 15, 2025 Sudan ta soki takunkuman da Amurka ta kakaba mata September 15, 2025 Dakarun Sojin Yamen Sun Kai Hari Kan Filin Jirgin Saman Ramon Na Isra’ila. September 14, 2025 Isra’ila Za ta Gamu Da Mummunar Martani Idan Tayi Gigin Afkawa Iran September 14, 2025 Ministocin Harkokin Wajen Kasashen Larabawa Da Na Musulmi Sun Fara Taro A Qatar. September 14, 2025 Gwamnatin Najeriya Ta Sanar Da Sabon Sharadi Na Bude Asusun Banki September 14, 2025 An Zabi Issa Tchiroma A Matsayin Dan Takara Daya Tilo A Kamaru September 14, 2025 Kasar Iran Ta Yi Fatali Da Zarge-Zargen Da Kungiyar G7 Da Kawayenta Suka Yi Kanta September 14, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci