HausaTv:
2025-09-17@23:08:33 GMT

DR Congo da mayakan M23 sun kasa cimma matsaya a  yarjejeniyar Doha

Published: 19th, August 2025 GMT

Kungiyar M23 da ke dauke da makamai a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, ta yi watsi da tattaunawar zaman lafiya da gwamnatin kasar, tana mai cewa ba za ta koma tattaunawa ba, sai dai idan hukumomi sun cika sharuddan yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma a baya.

Rikicin da aka gwabza tsakanin dakarun gwamnati da mayakan na M23 a watan Janairu ya kara kamari, yayin da kungiyar mai  dauke da makamai ta kwace iko da yankuna masu yawa a yankin gabashin kasar mai arzikin ma’adinai, kafin dukkan bangarorin biyu su cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a tattaunawar da aka yi a Qatar a watan da ya gabata, wanda ke da nufin share fagen samar da zaman lafiya mai dorewa.

Kungiyar ta M23 ta sanar a ranar Litinin cewa tawagarta ba ta koma kasar Qatar ba kamar yadda aka tsara za a ci gaba da tattaunawar zaman lafiya, yayin da kakakin kungiyar Lawrence Kanyuka ya shaidawa wasu kafofin yada labarai cewa matakin da gwamnatin Kongo ta dauka na nuna cewa “ba ta son zaman lafiya”, wanda hakan ke nuna shakku kan makomar shawarwarin.

Kanyuka ya zargi mahukuntan Kongo da karya sharuddan yarjejeniyar tsagaita bude wuta, yana mai cewa dakarun gwamnati sun ci gaba da kai hare-hare kan wuraren da ‘yan tawayen suke, duk da yarjejeniyar da ta tanadi cewa bangarorin biyu su dakatar da yakin, yayin da sojojin DR Congo suka yi watsi da wadannan zarge-zargen, tare da bayyana cewa babu kamshin gasiya a cikinsu.

A gefe guda kuma, Kongo ta zargi dakarun M23 da kai hare-hare a kusan kowace rana a lardin Kivu ta Arewa da Kivu ta Kudu.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Da Armenia sun kudiri aniyar kara bunkasa alakokinsu a dukkanin fagage August 19, 2025 Hamas da sauran bangarorin Falastinawa sun amince da shawarar tsagaita wuta August 19, 2025 Burkina Faso: Ba mu da bukatar Kodineta ta  MDD a kasarmu August 19, 2025 Araqchi: Iran Ba Za Ta Amince Da Sauyi A Kan Iyakokin Yankin Siyasa Ba August 18, 2025 Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Ce: Gwamnatin Mamayar Isra’ila Barazana ce Ga Tsaron Yanki August 18, 2025 Mataimakin Kwamandan Dakarun IRGC Ya Jadadda Cewa; Suna Sanya Ido Kan ‘Yan Sahayoniyya Da Magoya Bayansu August 18, 2025 Mai Ba Da Shawara Ga Kwamandan Sojojin Iran Ya Ce; Akwai Yiwuwar Sake Yaki, Don Haka Suna Cikin Shiri August 18, 2025 Shugaban Amurka Ya Ce: Yaki Tsakanin Iran Da Isra’ila Bai Kare Ba August 18, 2025 Trump Yace Zelensky Zai Kawo Karshen Yaki Da Rasha Tare Da Barin Batun NATO Da Crimea August 18, 2025 MSF Ta Ce Yawan Mutanen Da Suke Mutuwa A Gaza Sun Ninka Har Sau Uku Bayan Fara Aikin GHF August 18, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: zaman lafiya

এছাড়াও পড়ুন:

Fizishkiyan:  Wajibi Ne Musulmi Su Hada Kai Domin Dakatar Da Laifukan HKI

Shugabgan kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan wanda ya gana da fira ministan kasar Iraqi Muahmad Shi’a Sudani a taron Doha na kasashen musulmi ya bayyana cewa; Wajibi ne kasashen musulmi su hada kai idan har suna son kawo karshen laifukan da HKI take tafkawa.

Bugu da kari, shugaban kasar ta Iran ya kuma tattaunwa wasu hanyoyin da ya kamata a yi aiki da su, matukar ana son kawo karshen ta’addancin ‘yan sahayoniya.

Shugaba Fizishkiyan ya kuma ce, laifukan da HKI take tafkawa akan fararen hula a Gaza, da kashe yara da mata ta hanyar yunwa, wani lamari ne da hankali bai iya daukarsa, kuma idan musulmi su ka hada hannu da karfe wuri daya za su kawo karshensa.

A nashi gefen Fira ministan kasar Iraki ya bayyana abinda HKI take yi da cewa, isgili ne da dokokin kasa da kasa,don haka nauyi ne da ya doru a wuyan kasashen musulmi da su yi aiki domin ganin dukar matakan da suka dace.

Haka nan kuma ya ce, taron na birnin Doha dama ce ta daukar irin wadannan matakan.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Qatar, Turkiyya, Pakistan Da Labanon A Doha September 15, 2025 Kwamitin Kolin Tsron Kasar Iran Ya Amince Da Yarjejeniyar Da Aka Cimma Da Hukumar IAEA September 15, 2025 Jami’in Kasar Yemen Ya Aike Da Sako Ga Mahalarta Taron Birnin Doha Na Kasar Qatar September 15, 2025 Yawan Mutanen Da Suka Yi Shahada Sakamakon Kisan Kiyashin ‘Yan Sahayoniyya A Gaza Ya Kusaci 65,000 September 15, 2025 Gwamnatin Sudan Ta Ce: Babu Sulhu Da ‘Yan Tawayen Kasar Na Kungiyar Rapid Support Forces September 15, 2025 Kasashen Larabawa da na Musulmi na taron gaggawa kan harin Isra’ila a Qatar September 15, 2025 Hamas ta bukaci kasashen musulmi da na Larabawa su dauki mataki mai tsari kan Isra’ila September 15, 2025 Rabin Sojojin Isra’ila da suka ji rauni a yakin Gaza na fama da ciwon damuwa September 15, 2025 Sudan ta soki takunkuman da Amurka ta kakaba mata September 15, 2025 Dakarun Sojin Yamen Sun Kai Hari Kan Filin Jirgin Saman Ramon Na Isra’ila. September 14, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Za A Kada Kuri’ar Raba Gardama Akan Sabon Tsarin Mulki A Kasar Guinea
  • Hukumar Tarayyar Turai Ta Gabatar Da Shawarar Jingine Aiki Da Yarjejeniyar KAsuwanci Da HKI
  • Iran Ta Bayyana Abubuwan Da Bata Amince Da Su Ba A Jawabin Bayan Taro Na Kungiyar OIC A Birnin Doha
  • Iran Ta Bukaci Musulmi Su Goyi Bayan Yunkurin Kasa da Ka Na Kauracewa Isra’ila
  • Bayanin Bayan Taron Doha Ya Yi Kira Da A Kafa Runduwar Hadin Gwiwa Ta Kare Kai
  • Shugaban Kasar Iran Ya Gana Da Sarkin Kasar Qatar A Birnin Doha
  •  Dan Kasar Iran Mai Kirkira Ya Sami Kyautar Yabo A Kasar China
  • Fizishkiyan:  Wajibi Ne Musulmi Su Hada Kai Domin Dakatar Da Laifukan HKI
  • Kwamitin Kolin Tsron Kasar Iran Ya Amince Da Yarjejeniyar Da Aka Cimma Da Hukumar IAEA
  • Sudan ta soki takunkuman da Amurka ta kakaba mata