Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Jigawa ta Kare Kasafin Kudin 2026 a Gaban Majalisa
Published: 6th, December 2025 GMT
Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Jigawa ta ce za ta gudanar da aikin shigar da sabbin dokokin jihar cikin kundin bayanan dokoki da aka yi a jihar.
Babban Sakataren ma’aikatar, Barrister Lawan D. Baba, ya bayyana haka lokacin da ya ke kare kiyasin kasafin kudin sabuwar shekara ta 2026 a gaban kwamatin harkokin shari’a na majalisar dokokin jihar Jigawa.
Barrister Lawan D. Baba ya bayyana cewa ma’aikatar ta yi kiyasin kashe naira milyan 311 da dubu 847 a kasafin kudin sabuwar shekara.
Babban sakataren yace za su mayar da hankali ga batun kawar da jinkiri wajen gudanar da shari’o’i domin karfafa matakan samun shari’a cikin sauri ga al’ummar jihar.
A nasa jawabin, Shugaban kwamatin harkokin shari’a na majalisar dokokin jihar Jigawa kuma wakilin mazabar Hadejia, Barrister Abubakar Sadiq Jallo, ya jaddada bukatar wanzuwar dangantakar aiki tsakanin kwamatin da bangaren shari’a domin inganta aikin shari’a a kotu.
Kazalika, magatakardar Babbar kotun jihar da sakataren hukumar kula da ma’aikatan shari’a da kuma sakataren hukumar bada tallafin shari’a su ma sun kare na su kiyasin kasafin kudaden a gaban kwamatin.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa Ma aikatar Shari a jihar Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisa Ta Tabbatar Da Janar Christopher Musa A Matsayin Ministan Tsaron kasar
Majalisar Dattawa a najeriya ta amince da tsohon hafsan sojin
kasa, Janar Christopher Musa (mai ritaya), a matsayin sabon Ministan Tsaro bayan tantance shi da aka dauki kusan awanni biyar.
A lokacin tantancewar, Musa ya ce zai inganta tsaro ta hanyar hada kai tsakanin sojoji, ’yan sanda, sauran hukumomin tsaro da al’ummomi.
Ya yi gargaɗin cewa ’yan ta’adda na kai hare-hare a Nijeriya ne saboda suna ganin kasar tana da arziki, Ya kuma yi alkawarin magance gibin tsaro da aka samu da kuma kara hadin gwiwa da kasashen makwabta.
Ya yi nuni da cewa sojoji kadai ba za su iya magance matsalar tsaro ba, ya jaddada bukatar kyakkyawar gwamnati da goyon bayan al’umma.
Sanatoci sun yaba da kwarewarsa kuma suka amince da shi baki daya. Musa zai jagoranci harkokin tsaro a Nijeriya yayin da ake ci gaba da fama da hare-haren ta’addanci, satar mutane da kuma hare-haren ’yan bindiga.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Jagora: Musulunci Ya Daukaka Mata Matukar Dauka December 3, 2025 MDD Ta Amince Da Kudurori Biyu Masu Yin Tir Da HKI December 3, 2025 An Ga Sojojin Ruwa Na Amurka A Kasar Puerto Rico A Shirinta Na Mamayar Venezuela December 3, 2025 Kamfanonin jiragen Sama Na Kasashen Yamma Na Neman Izinin Amurka Don Komawa Iran December 3, 2025 Kungiyar Guinness Ta Rigistan Ayyukan Bajinta Ta Duniya Ta Dakatar Da Karban Daga HKI December 3, 2025 An tsare tsohuwar shugabar kula da manufofin ketare ta EU Mogherini bisa badakalar cin hanci December 3, 2025 Nijar ta maka kamfanin hakar uranium na Faransa Orano kotu December 3, 2025 Amurka ta soke bada mafaka ga ‘yan kasashen Afirka 10 December 3, 2025 Masar Ta Sanar Da Tattaunawa Da Amurka Don Shirya Sake Gina Gaza December 3, 2025 Isra’ila Ta Hana Motocin Agaji 6000 Shiga Gaza Duk Da Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta December 3, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci