Aminiya:
2025-12-06@15:49:08 GMT

Ranar Sabuwar Shekara za mu rufe duk na’urar POS mara rajista —Gwamnati

Published: 6th, December 2025 GMT

Hukumar Kula da Rajistar Kamfanoni (CAC) ta ba wa  dukkan masu gudanar da harkar kuɗi ta PoS a fadin Najeriya, wa’adin ranar 1 ga Janairu, 2026, su yi cikakken rajista ko ta rufe su.

A ranar Asabar, Hukumar ta sanar cewa yawaitar masu PoS marasa rajista a sassan ƙasar nan ya yawaita. Don haka ta jaddada cewa gudanar da PoS ba tare da rajista ba ya saɓa wa Dokar Kamfanoni ta 2020 da kuma ka’idojin Babban Bankin Najeriya (CBN).

Hukumar ta kuma zargi wasu kamfanonin fasahar kudi (fintech) da daukar wakilai ba tare da rajista ba, tana bayyana wannan dabi’a a matsayin da sakaci kulawa da kuma barazana ga daidaiton tsarin kuɗi na ƙasar.

Ta ce hakan na jefa miliyoyin ’yan Najeriya, ciki har da ’yan kasuwa ƙanana da masu aiki a karkara, cikin haɗarin tattalin arziki da asarar jari.

Ɗa da mahaifi sun mutu a cikin rijiya a Kano Ƙasashen waje na taimaka wa ’yan ta’adda a Najeriya —Sheikh Gumi

“Duk fintech da ke ba da damar ayyukan da ba bisa ƙa’ida ba za a saka su cikin jerin waɗanda ake sa wa ido, sannan za a kai rahotonsu ga CBN. Duk masu PoS an umurce su da su yi rajista nan da nan. Bin doka wajibi ne.

“Daga ranar 1 ga Janairu, 2026, ba wani mai PoS da zai ci gaba da aiki a Najeriya ba tare da cikakken rajista ba,” in ji CAC.

Wannan daiba shi ne karo na farko da aka yi kira kan buƙatar tsaurara dokokin sa ido kan harkar PoS ba.

An sha yin kira ga CBN da ya ɗauki matakan gaggawa wajen daƙile yawaitar damfara da ke addabar harkar PoS a faɗin ƙasar.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Yan Sanda Sun Kama Muhuyi Magaji, Tsohon Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci a Kano

Gwamnatin Kano ta tabbatar da kama Muhuyi Magaji Rimingado, tsohon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci ta jihar ranar Juma’a, inda ta yi zargi wasu ‘yansiyasa da hannu a kamen nasa.

Wata sanarwa daga ofishin Kwamashinan Shari’a Abdulkarim Maude ta ce jami’an ‘yansanda ne suka kama lauyan a ofishinsa da ke kan titin Zariya da misalin ƙarfe 5:30 na yamma, kuma suka tafi da shi hedikwatarsu da ke Bompai.

Kwamashinan ya siffanta kamen da “abin damuwa sosai” wanda “ya yi kama da yanayin aikin soja”. Ya yi iƙirarin cewa dakaru kusan 40 ne ɗauke da makamai suka je kama Muhuyi.

“Kwamashinan ya nuna cewa akwai yiwuwar lamarin yana da alaƙa da binciken da ake yi wa wasu manyan ‘yansiyasa,” in ji sanarwar.

Abdulkarim Maude ya kuma yi kira ga rundunar ‘yansandan Najeriya ta yi cikakken bayani game da dalilin kama Muhuyi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Mutum 3 sun mutum yayin haƙar rijiya a Kano
  • Sabuwar Dokar CBN: Nawa Za a Iya Cirewa a ATM da POS?
  • Fyaɗe ga ’yar shekara 12 ya ja wa matashi ɗaurin rai-da-rai a Yobe
  • Yan Sanda Sun Kama Muhuyi Magaji, Tsohon Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci a Kano
  • Amurka ta Faɗaɗa Jerin ƙasashen Afrika Da ta Sanya wa Takunkumin Visa
  • Cikakken jadawalin rukunin Gasar Kofin Duniya ta 2026
  • Jami’an tsaro sun kama masu garkuwa da mutane 7 a Gombe
  • Iran Ta Raya Ranar Haramta Takunkuman Bangare Guda A Duniya
  • NAJERIYA A YAU: Abun Da Masu Ruwa Da Tsaki Ke Yi Na Dakile Laifuka A Wurin Matasa