Aminiya:
2025-12-07@23:25:38 GMT

Yadda muka daƙile yunƙurin juyin mulki a Benin — Sojin Saman Najeriya

Published: 8th, December 2025 GMT

Rundunar Sojin Saman Najeriya (NAF), ta ce ta taka muhimmiyar rawa wajen daƙile yunƙurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin, bayan wasu sojoji sun bayyana hamɓarar da Gwamnatin Shugaba Patrice Talon.

Gungun sojojin, sun bayyana cewa ta rushe gwamnati tare da dakatar da kundin tsarin mulki, da rufe iyakokin ƙasar.

An gano gawar malamin Islamiyya da ya ɓace a Neja Mutum 5 sun rasu sanadin gobara da faɗa wa rijiya a Kano

Sun kuma ayyana Laftanar Kanar Tigri Pascal a matsayin Shugaban gwamnatin soja.

Daga baya gwamnatin Benin ta sanar da cewa sojojin ba su yi nasarar yin juyin mulkin ba.

Rahotanni sun nuna cewa jiragen yaƙin Najeriya sun shiga ƙasar domin kare dimokuraɗiyya, duk da cewa babu cikakkun bayanai ba.

NAF, ta tabbatar da cewa ta yi aiki a Benin bisa yarjejeniyar tsaro ta ECOWAS.

“Sojojin Saman Najeriya sun yi aiki a Jamhuriyar Benin bisa ƙa’idojin ECOWAS da umarnin Rundunar Tsaro ta Yanki,” in ji Air Commodore Ehimen Ejodame.

ECOWAS, ta yi Allah-wadai da yunƙurin juyin mulkin, tare da cewa za ta kare dimokuraɗiyyar ƙasar idan buƙatar hakan ta taso.

“ECOWAS za ta tallafa wa gwamnati da al’ummar Benin, har da tura rundunar tsaro ta yankin, domin kare kundin tsarin mulki da ikon ƙasar,” in ji sanarwar ECOWAS.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Dalilin da ya sa ’yan sanda suka kama ni — Muhuyi

Tsohon Shugaban Hukumar Kaɓar Koke-koke da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano (PCACC), Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya bayyana dalilin da ya sa ’yan sanda suka kama shi.

Ya ce an kama shi ne saboda jagorantar shari’ar almundahanar biliyoyin Naira na Dala Inland Dry Port, wadda ta shafi tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, da iyalinsa.

Jirgin sojin sama ya yi hatsari a Neja Nakiya ta hallaka yara 4 a Borno

Muhuyi, ya shaida wa DCL Hausa cewa an tafi da shi Abuja cikin dare.

“Da aka kama ni, suka sanya jami’ai biyu ɗauke da bindiga a gefena, sai wasu uku a gaba. Haka muka tafi daga Kano zuwa Abuja cikin dare,” in ji shi.

Ya ce ’yan sandan sun ƙi nuna masa takardar izinin kama shi har sai da suka isa Abuja.

“Da muka isa, suka gabatar min da sabbi  tuhume-tuhume na ɓatanci da kutse.

“A ina ne wanda ake zargi zai ki kare kansa ya kuma umarci ’yan sanda su kama babban lauya mai shigar da ƙara?” ya tambaya.

An bayar da belinsa, amma an umarce shi da ya koma Abuja a ranar Laraba tare da miƙa fasfo d5insa.

Ganduje da ’ya’yansa na fuskantar shari’a kan zargin canja mallakar kaso 20 a aikin Dala Inland Dry Port ba bisa ƙa’ida ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Benin : Har yanzu Shugaba Patrice Talon ne a kan mulkin_fadar shugaban kasa
  • Tawagar Majalisar Amurka ta iso Nijeriya Don Bincika Zargin Tauye Haƙƙin Addini
  • Fadar Shugaban Kasar Benin ta ce Har Yanzu Talon Ne a Kan Mulki
  • Jirgin Sojin Saman Najeriya Ya Yi Wani  Hatsari a Neja
  • Sojoji sun yi juyin mulki a Jamhuriyar Benin
  • Dalilin da ya sa ’yan sanda suka kama ni — Muhuyi
  • Ranar Sabuwar Shekara za mu rufe duk na’urar POS mara rajista —Gwamnati
  • Akwai hannun ƙasashen waje a rashin tsaron Najeriya —Sheikh Gumi
  • DSS ta kama likitan da ke duba ’yan bindiga a dazukan Kwara