Aminiya:
2025-12-06@21:20:53 GMT

Dalilin da ya sa ’yan sanda suka kama ni — Muhuyi

Published: 6th, December 2025 GMT

Tsohon Shugaban Hukumar Kaɓar Koke-koke da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano (PCACC), Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya bayyana dalilin da ya sa ’yan sanda suka kama shi.

Ya ce an kama shi ne saboda jagorantar shari’ar almundahanar biliyoyin Naira na Dala Inland Dry Port, wadda ta shafi tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, da iyalinsa.

Jirgin sojin sama ya yi hatsari a Neja Nakiya ta hallaka yara 4 a Borno

Muhuyi, ya shaida wa DCL Hausa cewa an tafi da shi Abuja cikin dare.

“Da aka kama ni, suka sanya jami’ai biyu ɗauke da bindiga a gefena, sai wasu uku a gaba. Haka muka tafi daga Kano zuwa Abuja cikin dare,” in ji shi.

Ya ce ’yan sandan sun ƙi nuna masa takardar izinin kama shi har sai da suka isa Abuja.

“Da muka isa, suka gabatar min da sabbi  tuhume-tuhume na ɓatanci da kutse.

“A ina ne wanda ake zargi zai ki kare kansa ya kuma umarci ’yan sanda su kama babban lauya mai shigar da ƙara?” ya tambaya.

An bayar da belinsa, amma an umarce shi da ya koma Abuja a ranar Laraba tare da miƙa fasfo d5insa.

Ganduje da ’ya’yansa na fuskantar shari’a kan zargin canja mallakar kaso 20 a aikin Dala Inland Dry Port ba bisa ƙa’ida ba.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Sanda Zarge zarge

এছাড়াও পড়ুন:

DSS ta kama likitan da ke duba ’yan bindiga a dazukan Kwara

Hukumar Tsaro ta DSS ta kama wani likita da ake zargin yana ba da magunguna tare da kula da ’yan bindiga masu garkuwa da mutane da ke wasu sassan jihar Kwara.

An kama wanda ake zargin, wanda ba a iya gano sunansa ba a lokacin rahoton, a yankin Jebba bayan rahotannin sirri sun nuna cewa wasu masu safarar kaya suna kai magunguna daga Sakkwato domin kula da ’yan fashin daji da suka samu raunuka a dazukan jihar.

Kakakin majalisar dokokin Ribas da takwarorinsa 16 sun fice daga PDP zuwa APC An kashe matashi yayin rikici a wajen raɗin suna a Bauchi

Majiyoyin tsaro sun ce da dama daga cikin waɗannan ƙungiyoyin masu laifi sun samu raunukan harbin bindiga a fafatawar da suka yi da jami’an tsaro a baya-bayan nan.

“Saboda haka muna ba da shawarar ƙara tsaurara matakan tsaro a cibiyoyin lafiya da ke cikin dazuka, domin masu garkuwa da mutane na iya kai hari a wuraren,” in ji wani jami’in tsaro.

Mai magana da yawun gwamnan jihar ta Kwara, Rafiu Ajakaye, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa kamun wata babbar nasara ce a ƙoƙarin da ake ci gaba da yi kan ’yan fashin daji.

“Wannan babban mataki ne daga DSS. Ya ƙara tabbatar da cewa hukumomin tsaro suna matsawa wa waɗannan ’yan ta’adda, suna kuma toshe hanyoyin tallafi da ke ba su damar gudanar da ayyukansu,” in ji shi.

Ajakaye ya ƙara da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da ƙarfafa haɗin gwiwa da hukumomin tsaro domin rufe dukkan hanyoyin da ke taimaka wa ayyukan garkuwa da mutane.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kwastam ta kama jirgin ruwan Brazil ɗauke da hodar iblis a Legas
  • ’Yan bindiga sun harbe ɗan sanda har lahira a Edo
  • ’Yan sanda sun ceto yara 2 da aka yi garkuwa da su a Borno
  • Mutum 3 sun mutum yayin haƙar rijiya a Kano
  • Yan Sanda Sun Kama Muhuyi Magaji, Tsohon Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci a Kano
  • ’Yan sanda sun kama tsohon shugaban PCACC, Muhuyi Rimin Gado a Kano
  • Jami’an tsaro sun kama masu garkuwa da mutane 7 a Gombe
  • DSS ta kama likitan da ke duba ’yan bindiga a dazukan Kwara
  • NAPTIP ta daƙile yunƙurin safarar mutum 7 daga Kano zuwa Saudiyya