Mamakon ruwa ya lalata gidaje 70 a Jigawa
Published: 19th, August 2025 GMT
Aƙalla gidaje 70 ne suka ruguje wasu da dama suka lalace sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da ya haddasa ambaliya a Ƙaramar Hukumar Malam Madori ta Jihar Jigawa.
Yankunan da ibtila’in ya shafa sun haɗa da Tonikutara, Gandun Sarki, Gandun Bundugoma da rukunin gidajen Shagari Quarters, bayan ruwan sama da aka kwashe sa’o’i da dama a ranar ya mamaye kwalbatoci da magudanan ruwa a yankin.
Dan-Ummah Abba, wani magidanci da lamarin ya shafa a Gandun Sarki ya bayyana cewa gidansa da yake zaune a ciki sama da shekara 30 ya rushe a sakamakon lamarin.
Daga nan ya roƙi Gwamnatin Jihar Jigawa da ta kawo musu ɗaukin gaggawa.
NAJERIYA A YAU: Halin Da Muke Ciki Bayan Rasa ‘Yan Uwanmu A Hadarin Kwale-Kwale A Sakkwato An rage kuɗin wankin koda da kashi 76% a asibitocin tarayyaRuwan saman da aka fara tun ranar Asabar har zuwa safiyar Lahadi, da ya tilasta wa mazauna yankin yin ƙaura tare da neman mafaka a wuraren ’yan uwa.
Bulama Jamilu, wani basarake a yankin, ya ce: “Yawancin waɗanda abin ya shafa suna fakewa a gidajen ’yan uwansu saboda an bar gidaje da yawa a lalace.”
Shugaban Ƙaramar Hukumar Malam Madori, Salisu Sani Garun-gabas ya jajanta wa waɗanda abin ya shafa tare da yin alƙawarin tallafin da ake buƙata ga waɗanda bala’in ya shafa .
Ya kuma sanar da kwamitin kula da agajin gaggawa na jihar da ya tantance tare da bayar da rahoton ɓarnar da aka yi a Gandun Bundugoma, Gandun Sarki, Tonikutara da Shagari Quarters.
Shugabar kwamitin agajin gaggawa na ƙaramar hukumar, Hajiya Amina Haruna Dokajo ta ce “Ɗan majalisar mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Malam Madori Hamza Adamu Babayaro ya bayar da gudunmawar motar yashi da sauran kayan agaji ga waɗanda abin ya shafa.”
Ta kuma yi bayanin cewa shugaban ƙaramar hukumar ya umlaurci kwamitin da ya kafa injin fanfo a Gandun Sarki wanda zai kwashe ruwan zuwa karkara.
Tun da farko wata tawagar gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin babban mai ba da shawara ta musamman kan ambaliyar ruwa, Hamza Muhammad Hadejia ta isa wurin da lamarin ya faru tare da yin alƙawarin ɗaukar matakin gaggawa don daƙile aukuwar hakan a nan gaba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jigawa ruwan sama Gandun Sarki
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Neja Ta Musanta Rahoton Hana Da’awa A Jihar
Rahoton rashin fahimtar da aka fara yadawar, ya biyo bayan taron kwamitin zaman lafiya da kwantar da tarzoma na jihar, wanda Darakta Janar ya jagoranta a ranar 4 ga watan Satumba.
Rashin fahimtar sahihin sakamakon taron ya sa wasu suka rahoto cewa, kwamitin ya dakatar da Malamai daga yin wa’azi.
Sanarwar ta kara da cewa, “Hukumar ba ta da hurumin haramtawa Malaman Addinin Musulunci yin wa’azi sai dai in ya bayyana a fili an taka ƙa’idojin hukumar da ta shimfiɗa”.
A cewar Hukumar, an kira taron ne domin gabatar da fom din rijistar yin wa’azi ko Da’awah da kuma bin tsarin tantancewa.
Ta bayyana shirin a matsayin wani yunkuri na wayar da kan jama’a don “hana rashin fahimtar juna da kuma daƙile yaɗuwar wa’azin yaudara” a faɗin jihar Neja.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp