Daga Usman Muhammad Zaria

Ma’aikatar Ayyuka da Sufuri ta Jihar Jigawa ta yi kiyasin kashe kudade miliyan dubu 161 da milyan 336 domin gudanar da ayyukan hanyoyin mota da harkokin yau da kullum a sabuwar shekara ta 2026.

Babban sakataren ma’aikatar, Malam Ahmad Isah, ya bayyana haka lokacin da ya ke kare kiyasin kasafin kudin ma’aikatar a gaban kwamatin ayyuka da sufuri na majalisar dokokin jihar Jigawa.

Babban Sakataren ya yi bayanin cewar, za a yi amfani da mafi yawan kudaden ne wajen gudanar da ayyukan hanyoyin mota tsakanin gariruwa da hanyoyin burji da kuma titunan cikin gari.

Yana mai cewar, haka kuma za a gudanar da ayyukan hanyoyi a manyan makarantun jihar ciki har Jami’ar Sule Lamido da ke Kafin Hausa da kwalejin fasaha da ke Dutse da cibiyar binciken aikin gona ta Kazaure, da kwalejin koyon aikin lafiya matakin farko da ke Jahun da sauransu.

Sai dai kuma babban sakataren ya koka dangane da bukatar daukar injiniyoyi domin aiki a ma’aikatar da hukumar gyaran hanyoyin mota JIRMA da kuma daukar sabbin jami’an duba lafiyar ababen hawa wato V.I.O, idan aka yi la’akari da karancin ma’aikata saboda masu yin ritaya.

Alhaji Ahmad Isah ya kara da cewar ma’aikatar tana kokarin cimma yarjajjeniya da makarantar koyon tukin jirgin sama ta kasa da ke Zaria domin amfani da filin jirgin sama na Dutse a matsayin sansanin koyon tukin jirgin sama.

Kazalika, ya ce makarantar koyon tukun mota da ke karamar hukumar Birnin Kudu za ta amfana da wasu ayyuka a sabuwar shekara.

A nasa jawabin, shugaban kwamatin ayyuka da sufuri na majalisar dokokin jihar Jigawa kuma wakilin mazabar Bulangu Alhaji Yusuf Ahmad Soja, ya yi addu’ar Allah Ya sa kasafin kudin ya karfafa cigaban jihar nan a sabuwar shekara.

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Jigawa Kare Kasafi

এছাড়াও পড়ুন:

Kwastam ta kama jirgin ruwan Brazil ɗauke da hodar iblis a Legas

Hukumar Kwastam, ta kama kilo 25.5 na hodar iblis a wani jirgin ruwa na ƙasar Brazil mai suna MV San Anthonio a tashar jirgin ruwa ta Legas.

An ɓoye hodar cikin ƙananan jakunkuna biyar.

’Yan bindiga sun harbe ɗan sanda har lahira a Edo Ranar Sabuwar Shekara za mu rufe duk na’urar POS mara rajista —Gwamnati

Kwanturola Emmanuel Oshoba, ya ce an gudanar da aikin ne bayan samun bayanan sirri tare da haɗin gwiwar hukumar NDLEA.

Ya ƙara da cewa jirgin ya tsaya a ƙasashen da suka yi ƙaurin suna wajen harkar safarar miyagun ƙwayoyi kafin isowarsa Najeriya.

An tsare jirgin, sannan an miƙa hodar da aka kama ga NDLEA domin ci gaba da bincike.

Oshoba, ya ce wannan nasara tana nuna jajircewar hukumar Kwastam wajen kawar da haramtattun kasuwanci da kuma kare ƙasa, musamman lokacin bukukuwan ƙarshen shekara ke ƙaratowa.

Ya yi gargaɗin cewa hukumar ba za ta bari a yi amfani da ita wajen aikata laifuka ba, kuma duk kayayyakin da suka shigo da su sai an yi bincike a kansu.

A cewarsa, haɗin kai tsakanin Kwastam da NDLEA yana bayar da kyakkyawan sakamako, kuma zai ci gaba da karya tsarin masu safarar miyagun ƙwayoyi.

Jami’an NDLEA ƙarƙashin jagorancin CN Haliru Umar sun karɓi kayan da aka kama.

Kwastam ta kuma buƙaci masu mu’amala da tashar su kasance masu bin doka tare da kai rahoton duk wani abun zargi domin tabbatar da tsaron tashar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Jirgin sojin sama ya yi hatsari a Neja
  • Jirgin NAF ya yi hatsari a Neja
  • Kwastam ta kama jirgin ruwan Brazil ɗauke da hodar iblis a Legas
  • Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Jigawa ta Kare Kasafin Kudin 2026 a Gaban Majalisa
  • Sabuwar Dokar CBN: Nawa Za a Iya Cirewa a ATM da POS?
  • Shugaban Majalisar Dattawan Akpabio ya Nemi Sanata Natasha ta Biya Shi Diyyar Biliyan 200
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Samar da Wutar Lantarki a Yankunan Kananan Hukumomin Jihar
  • Mutum 6 sun rasu, 13 sun jikkata a hatsarin mota a Kogi
  • Jirgin fadar shugaban ƙasa ya ƙi sayuwa wata 5 bayan saka shi a kasuwa