An rage kuɗin wankin koda da kashi 76% a asibitocin tarayya
Published: 19th, August 2025 GMT
Gwamnatin Tarayya ta rage farashin jinyar ciwon ƙoda daga kimanin N50,000 zuwa N12,000 a Asibitocin Tarayya — ragin da ya kai kashi 76 cikin 100.
Wannan saukin farashi ya samu ne bayan amincewar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, kamar yadda mai ba shi shawara kan harkokin sadarwa da manufofi, Daniel Bwala, ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.
Bwala ya ce hakan zai kawo saukin rayuwa ga dubban ’yan Najeriya da ke fama da cutar, wadda ke bukatar yin jinya sau da dama a kowane mako.
“Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da tallafin tarihi domin rage farashin jinyar ciwon koda ga ’yan Najeriya. An rage farashin kowace wankin ƙoda daga N50,000 zuwa N12,000 kacal, wanda zai kawo sauki ga dubban masu fama da cutar koda,” in ji Bwala.
Sanarwar ta bayyana cewa sabon farashin ya fara aiki a manyan cibiyoyin lafiya guda goma da ke fadin Najeriya, wadanda suka hada da:
Bwala ya kara da cewa, “Za a ƙara wasu cibiyoyin lafiya da asibitocin koyarwa kafin ƙarshen shekara domin faɗaɗa damar a faɗin ƙasa.”
Ya kuma tuna cewa a bara, Shugaba Tinubu ya amince da haihuwa ta hanyar tiyata kyauta ga mata masu juna biyu a asibitocin tarayya — domin inganta lafiyar iyaye mata da rage mace-macen da za a iya kaucewa.
Bwala ya jaddada cewa waɗannan matakai na nuna cikakken kudurin Shugaban Ƙasa na tabbatar da cewa babu ɗan Najeriya da za a hana jinya saboda rashin kuɗi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: wankin ƙoda
এছাড়াও পড়ুন:
Yan Nijeriya Na Ɗanɗana Kuɗarsu Kan Jinkirta Cire Tallafin Mai – Sarki Sanusi
“A lokacin, mun yi lissafin adadi a Babban Bankin. Na tashi na kafa sharuda bisa ga ka’idodi, inda na ce a cire tallafin yau. Farashin kaya zai tashi daga kashi 11 zuwa kashi 13, zan rage shi a cikin shekara guda. Ba za mu samu hauhawar farashin kaya na kusan kashi 30 ba,” in ji shi.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA