’Yan sanda sun ceto yara 2 da aka yi garkuwa da su a Borno
Published: 6th, December 2025 GMT
’Yan sanda sun ceto yara 2 da aka yi garkuwa da su, masu shekaru hudu da biyar, a Jihar Borno.
An ceto yaran ne a yayin wani samame da ’yan sanda suka kai a Ƙaramar Hukumar Jere, inda masu garkuwar suka je karbar kuɗin fansa.
Sanarwa da ASP Nahum Kenneth Daso, kakakin rundunar ya fitar ta ce, bayan sun sami rahoto a ranar 4 ga Disamba cewa yara uku sun bace, washegari masu garkuwar suka sako ɗaya daga cikin yaran da takardar neman naira miliyan 10 domin sakin sauran biyun.
A ranar ce jami’an rundunar suka kai samame a wurin da aka ware don karɓar kuɗin fansar.
Ganin hakan masu garkuwa da mutanen, suka farga da wannan tarko da aka musu nan da nan suka yi watsi da yaran suka gudu cikin duhu.
An ceto yaran ba tare da wani rauni ko biyan kuɗin fansa ba, kuma sun sake haɗuwa da iyalansu, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin gano waɗanda ake zargi.
Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Yobe, Naziru Abdulmajid, ya ba da umarnin zurfafa bincike kuma ya umurci jami’an rundunar da su qarfafa sintiri, su gudanar da ayyukan bincike mai tsauri, da kuma ci gaba da gudanar da ayyukansu don rage yawaitar aikata laifuka a baya-bayan nan.
Hukumar tsaron ta kuma yi kira ga mazauna yankin da su kasance cikin shiri da kuma bayar da rahoton ayyukan da ake zargi, tare da samar da lambobin tuntuɓar gaggawa don hanzarta kai xauki.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda ceto yara garkuwa da mutane
এছাড়াও পড়ুন:
Na’im Kassim Ya Yi Suka Akan Shigar Kasar Cikin Kwamitin Tattaunawa Da “Isra’ila” Kai Tsaye
Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kassim wanda ya gabatar da jawabi a jiya Juma’a da marece ya yi suka akan yadda aka shigar da farar hula dan kasar Lebanon a cikin kwamitin dake sa ido akan tsagaita wutar yaki da Haramtacciyar kasar Isra’ila, yana mai bayyana hakan da cewa; ya sabawa dukkanin bayanan da su ka rika fitowa a hukumance na fada ganin an daina kawo wa Lebanon hari sannan ayi hakan.
Jawabin na Sheikh Na’im ya yi shi ne adaidai lokacin da ake tunawa da kuma girmama malaman addini da su ka yi shahada, yana mai cewa abinda aka yi na tura wakilin Lebanon farar hula a cikin wannan kwamitin tsagaita wutar, tamkar bai wa Isra’ila kyauta ne da kuma ja da baya, kuma duk da hakan ba zai sauya matsayar abokan gaba ba, ya daina kai hare-hare ko ya janye daga inda ya mamaye.
Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce; Wakilin Lebanon farar hula ya shiga cikin kwamitin amma babu abinda ya karu sai matsin lamba daga “Isra’ila” tare da Amurka da ci gaba da kai wa Lebanon hare-hare.
Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kuma ce; Wannan abinda ya faru wani Karin koma baya ne, kuma mai makon a dauki matakan da za su bai wa Lebanon karfi, sai ake daukar matakan da ba su ne su ka dace da Isra’ila ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Gwamnatin Iraki Ta Kore Saninta Da Shigar Da Sunayen Hizbullah Da “Ansarullah” A Cikin Na ‘Yan Ta’adda December 6, 2025 Limamin Tehran: Idan Abokan Gaba Su Ka Sake Yin Kuskure Akan Iran Za Su Sake Cin Kasa December 6, 2025 Iran Da Pakisatan Sun Amince Da Farfado da Layin Dogo Tsakanin Istambul, Tehran Zuwa Islamabad December 5, 2025 Iran Ta Raya Ranar Haramta Takunkuman Bangare Guda A Duniya December 5, 2025 Trump Ya Yabawa Rwanda Da Kongo DMK Kan Sulhuntawa A Yakin Gabancin Kongo December 5, 2025 Najeriya: Tinubu Ya Nada Wasu Karin Jakadu 65, Sanatoci Da Tsoffin Gwamnoni Na Daga Cikinsu December 5, 2025 Shin Ziyarar Putin a Indiya alama ce da ke nuna cewa New Delhi na yin watsi da gargadin Trump? December 5, 2025 Iran Ta Mayar Da Martani Kan Sanarwar Bayan Taron Majalisar Kasashen Yankin Tekun Fasha December 5, 2025 Afirka ta Kudu Za Ta Dauki Hutu Daga Halartar Tarukan G20 A Karkashin Shugabancin Trump December 5, 2025 Microsoft Za Ta Fuskanci Hukunci Kan Taimaka Wa Laifukan Isra’ila A Kan Falasdinawa December 5, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci