Kwastam ta kama jirgin ruwan Brazil ɗauke da hodar iblis a Legas
Published: 6th, December 2025 GMT
Hukumar Kwastam, ta kama kilo 25.5 na hodar iblis a wani jirgin ruwa na ƙasar Brazil mai suna MV San Anthonio a tashar jirgin ruwa ta Legas.
An ɓoye hodar cikin ƙananan jakunkuna biyar.
’Yan bindiga sun harbe ɗan sanda har lahira a Edo Ranar Sabuwar Shekara za mu rufe duk na’urar POS mara rajista —GwamnatiKwanturola Emmanuel Oshoba, ya ce an gudanar da aikin ne bayan samun bayanan sirri tare da haɗin gwiwar hukumar NDLEA.
Ya ƙara da cewa jirgin ya tsaya a ƙasashen da suka yi ƙaurin suna wajen harkar safarar miyagun ƙwayoyi kafin isowarsa Najeriya.
An tsare jirgin, sannan an miƙa hodar da aka kama ga NDLEA domin ci gaba da bincike.
Oshoba, ya ce wannan nasara tana nuna jajircewar hukumar Kwastam wajen kawar da haramtattun kasuwanci da kuma kare ƙasa, musamman lokacin bukukuwan ƙarshen shekara ke ƙaratowa.
Ya yi gargaɗin cewa hukumar ba za ta bari a yi amfani da ita wajen aikata laifuka ba, kuma duk kayayyakin da suka shigo da su sai an yi bincike a kansu.
A cewarsa, haɗin kai tsakanin Kwastam da NDLEA yana bayar da kyakkyawan sakamako, kuma zai ci gaba da karya tsarin masu safarar miyagun ƙwayoyi.
Jami’an NDLEA ƙarƙashin jagorancin CN Haliru Umar sun karɓi kayan da aka kama.
Kwastam ta kuma buƙaci masu mu’amala da tashar su kasance masu bin doka tare da kai rahoton duk wani abun zargi domin tabbatar da tsaron tashar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Brazil hodar iblis Jirgin ruwa Kwastam
এছাড়াও পড়ুন:
Ƙudirin dokar hukuncin kisa ga masu satar mutane ya tsallake karatu na biyu
Majalisar Dattawa ta amince da wani sabon ƙudiri da ke neman a gyara dokar yaƙi da ta’addanci, domin a ɗauki garkuwa da mutane a matsayin babban laifi na ta’addanci.
Ƙudirin, wanda Sanata Opeyemi Bamidele ya gabatar, ya tanadi hukuncin kisa ga duk wanda aka kama da laifin satar mutane, ba tare da wata zaɓin tara ba.
Tsaro: Gwamnatin Kano za ta fara amfani da jirage marasa matuƙa a iyakokinta Gobara ta ƙone kasuwar katako a AbujaSanata Bamidele, ya ce ƙudirin ya yi daidai da yunƙurin gwamnati da majalisa na kawo ƙarshen matsalar tsaro a ƙasar nan.
Yayin gabatar da ƙudirin, ya ce garkuwa da mutane na ƙara yawaita, kuma ƙungiyoyin miyagu na amfani da shi wajen tara k6udi, abin da ke jefa jama’a cikin tsoro da kuma daƙile karatun yara a jihohi da dama.
Sanatoci da dama sun goyi bayan hukuncin kisa, inda suka bayyana cewa hakan zai zama gargaɗi ga masu aikata wannan mummunan laifi.
Wasu kuma sun nemi a hukunta bankunan da ke taimakawa wajen aikewa ko karɓar kuɗaɗen fansa, yayin da wasu suka ce ya kamata a daina yi wa ’yan ta’adda afuwa.
Majalisar ta tura ƙudirin zuwa kwamitoci na musamman domin bincike, tare da umarnin su kawo rahoto cikin makonni biyu.