Aminiya:
2025-12-07@23:25:47 GMT

An gano gawar malamin Islamiyya da ya ɓace a Neja

Published: 7th, December 2025 GMT

An gano gawar wani malamin makarantar Islamiyya kuma mahaifin ’ya’ya bakwai, Malam Awwal Yakubu, a cikin wani kango da ke rukunin gidaje na Talba a birnin Minna, na Jihar Neja.

Malam Awwal, yana da makarantar Islamiyya a unguwar Barikin-Saleh, an neme shi sama ko ƙasa tun ranar Alhamis ɗin da ta gabata.

’Yan bindiga sun hallaka mutum 4, sun sace mata 4 a Sakkwato Sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin

An gano gawarsa ne da safiyar ranar Lahadi.

Rahotanni sun nuna cewa an ƙone al’aurarsa, sannan an samu kwalin ashana a gefen gawarsa.

Shugaban al’ummar yankin, Malam Mahmud Dalhatu Iya, ya shaida wa Aminiya cewa iyalan mamacin sun riga sun gano gawar kuma an riga an binne shi.

Ya ce, “An sanar da ni cewa an ga wata gawa ta lalace a wani gini da ba a kammala ba a cikin rukunin gidajenmu.

“Mun kai wa ’yan sanda rahoto. Muna nan lokacin da wani ya zo ya ce shi abokin mamacin ne, ya kuma ya ɓace tun ranar Alhamis. An yi wa gawar sutura don yi mata jana’iza a lokacin da nake magana da ku.”

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce, “A yau, 7 ga watan Disamba 2025, da misalin ƙarfe 10 na safe, an samu rahoto cewa an ga gawa a bayan rukunin gidaje na Talba da ke kan titin Kpakungu.

“Jami’an ’yan sandan Kpakungu sun je wajen kuma sun gano gawar ta lalace cikin wani gini da ba a kammala ba.

“Daga bisani iyalansa suka tabbatar da cewa Auwal Yakubu ne, mai shekaru 45, mazaunin wannan yanki.”

Ya ƙara da cewa, “Ana zargin cewa an jefar gawar ne a wajen, domin an ruwaito ya ɓace tun a ranar 4 ga watan Disamba kafin a gano shi da safiyar yau.

“An kai gawar asibiti, kuma an fara bincike don gano musabbabin rasuwarsa.”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Sanda Gawa Malamin Islamiyya

এছাড়াও পড়ুন:

Tawagar Majalisar Amurka ta iso Nijeriya Don Bincika Zargin Tauye Haƙƙin Addini

Majalisar Dokokin Amurka ya iso Abuja yayin da ƙasashen biyu ke ƙara matsa ƙaimi wajen tattaunawar diflomasiyya kan haɗin gwiwar tsaro da kuma zargin tauye haƙƙin addini.

Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan tsaro Nuhu Ribadu, ya ce ya gana da wakilan kuma zuwan tawagar na cikin abubuwan da suka amince da shi a tasu ziyarar da suka kai birnin Washington a watan Nuwamba.

“Tawagar ta ƙunshi ‘yanmajalisar wakilai Mario Díaz-Balart, Norma Torres, Scott Franklin, Juan Ciscomani, da Riley M. Moore,” in ji Ribadu cikin wata sanarwa a shafinsa na sada zumunta.

Kazalika, Jakadan Amurka a Najeriya Richard Mills na cikin tawagar.

A cewar Ribadu, tattaunawar ta mayar da hankali kan yaƙi da ta’addanci, tabbatar da zaman lafiyar yanki da kuma ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tawagar Majalisar Amurka ta iso Nijeriya Don Bincika Zargin Tauye Haƙƙin Addini
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 168
  • Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 167
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 166
  • Jirgin Sojin Saman Najeriya Ya Yi Wani  Hatsari a Neja
  • Nakiya ta hallaka yara 4 a Borno
  • Ranar Sabuwar Shekara za mu rufe duk na’urar POS mara rajista —Gwamnati
  • ’Yan sanda sun ceto yara 2 da aka yi garkuwa da su a Borno
  • Sabuwar Dokar CBN: Nawa Za a Iya Cirewa a ATM da POS?