Aminiya:
2025-12-07@23:26:06 GMT

Mutum 5 sun rasu sanadin gobara da faɗa wa rijiya a Kano

Published: 7th, December 2025 GMT

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ta tabbatar da rasuwar wasu mutum biyar sakamakon haɗura uku da suka auku a jihar.

Kakakin hukumar, Saminu Yusif Abdullahi, ya ce hatsrin farko ya faru ne da safiyar ranar Alhamis a unguwar Badawa Layin Day by Day ca Ƙaramar Hukumar Nassarawa.

Sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin Jirgin sojin sama ya yi hatsari a Neja

Lamarin ya faru ne a wani gida mai faɗin kafa 25 da 20 wanda ya kama da wuta.

Ma’aikatan kashe gobara sun ceto wata yarinya mai shekara 10 daga a cikin gidan, amma daga baya ta rasu a asibiti.

An bai wa iyayenta gawarta.

Hatsari na biyu ya faru ne a Ƙauyen Badume Kanawa da ke Karamar Hukumar Bichi.

Wani mutum mai shekara 65, Sa’idu Gada, yana aiki a cikin rijiya lokacin da igiyar da ta ke riƙe da shi ta tsinke, ya faɗa ciki.

Ɗansa mai shekara 20, Sani Isyaku, ya shiga rijiya domin ceto shi, shi ma ya maƙale.

Wani mutum na uku, Yakubu Abdullahi mai shekara 60, ya shiga domin taimakonsu, shi ma daga bisani ya faɗa cikin rijiyar.

Ma’aikatan hukumar sun fito da su daga rijiyar, amma sun riga sun rasu.

An miƙa wa ’yan sandan Badume gawarwakinsu.

A wani lamari na daban kuma, wani yaro mai shekara 10, Hassan Iliyasu Haruna, ya zame tare da faɗa wa rijiya a Ƙaramar Hukumar Danbatta.

Ma’aikatan hukumar kashe gobara sun ceto shi, amma daga baya ya rasu.

An miƙa wa mahaifinsa gawar yaron.

Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Kano, Sani Anas, ya ja hankalin jama’a da su daina shiga rijiya domin ceto mutane, domin a cewarsa hakan na da hatsari.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Gobara Hatsari rijiya mai shekara

এছাড়াও পড়ুন:

Fyaɗe ga ’yar shekara 12 ya ja wa matashi ɗaurin rai-da-rai a Yobe

Kotu ta yanke wa wani wanda ya yi wa wata yarinya ’yar shekara 12 fyaɗe hukuncin ɗaurin rai-da-rai a Ƙaramar Hukumar Guba ta Jihar Yobe.

Babbar Kotun Jihar Yobe da ke zaune a ƙaramar hukumar Gujba ta yanke wa mutumin mai shekaru 31 mai suna Ali Kwano.

An gurfanar da shi ne a kan zargin ya kai yarinyar cikin aji a ƙaramar makarantar sakandare ta je-ka-ka-dawo da ke garin Bumsa, inda ya yi lalata da ita da ƙarfi.

Ya yaudari yarinyar ce bayan ya gaya mata cewa ta jira shi a cikin aji bisa cewar zai sayi ƙosai.

Bayan da ta shiga ajin sai ya kama hannunta, ya rufe bakinta ya danne ta a ƙasa sannan ya yi lalata da ita da ƙarfi.

Ƙasashen waje na taimaka wa ’yan ta’adda a Najeriya —Sheikh Gumi ’Yan sanda sun kama tsohon shugaban PCACC, Muhuyi Rimin Gado a Kano

Alƙaliyar da ke jagorantar shari’a, Mai Shari’a Amina Shehu, ta same shi da laifi, don haka ta yanke masa hukuncin ɗaurin rai-da-rai bisa ga sashe na 3 na dokar haramta cin zarafin mutane, ta Jihar Yobe ta Shekarar 2020.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kwastam ta kama jirgin ruwan Brazil ɗauke da hodar iblis a Legas
  • Ranar Sabuwar Shekara za mu rufe duk na’urar POS mara rajista —Gwamnati
  • ’Yan sanda sun ceto yara 2 da aka yi garkuwa da su a Borno
  • Mutum 3 sun mutum yayin haƙar rijiya a Kano
  • Fyaɗe ga ’yar shekara 12 ya ja wa matashi ɗaurin rai-da-rai a Yobe
  • Yan Sanda Sun Kama Muhuyi Magaji, Tsohon Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci a Kano
  • Dorinar Ruwa ta Yi Ajalin Mutane Biyu, ta Raunata Shida a Gombe
  • ’Yan sanda sun kama tsohon shugaban PCACC, Muhuyi Rimin Gado a Kano
  • Matashi ya rasu yayin rikici a wajen radin suna a Bauchi