Iran Ta Zama Zakaran Duniya A Wasan “Taekwondo” Na Masu Shekaru Kasa Da 21
Published: 7th, December 2025 GMT
Kungiyar ‘yan wasan ” Taekwondo” Iran dake kasa a shekaru 21 sun zama gwarazan duniya da aka yi a birnin Nairobi, bayan da su ka sami zinariya 3 da azurfa 1 sai kuma tagulla biyu.
Kamfanin dillancin labarun “Irna” ya nakalto cewa; a jiya Asabar ne aka kawo karshe gasar wasan na ” Taekwondo” wanda ya sami halartar ‘yan wasa 452 daga kasashe 75.
A ranar ta karshe ta wasan, dan wasan Iran Muhammad Aizadeh, ya sami azurfa, sai kuma wani dan wasan “Matin Rizayi wanda ya sami tagulla.
Wadanda su ka sami zinariya kuwa su ne Abul Fadl Zandi, da Radin Zinalu sai kuma Amir Riza Gulami.
Kasar Turkiya ta zo ta biyu da ta sami zinariya biyu da azurfa daya, sai kasar Khazakistan wacce ta zo ta uku da ta sami zinariya biyu da tagulla daya. Kasar da ta biyo bayanta ita ce Masar da da Bulgaria sai India.
A fagen mata kuwa, Iraniyawa 6 ne su ka sami kyautuka, inda kungiyarsu ta zo ta hudu.
An kuma zabi Majid Afkali na Iran a matsayin mai bayar da horo na daya, sai kuma Abul Fadl Zandi wanda aka zaba a matsayin dan wasa na farko.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Afirka Ta Kudu: An Kashe Mutane 11 A Wani Bude Wuta Na Kan Mai Uwa Da Wabi December 7, 2025 Dubban Mutane Suna Guduwa Daga Gabashin DRC Saboda Barkewar Sabon Fada December 7, 2025 Mutane Biyar Ne Suka Mutu A Wata Musayar Wuta Tsakanin Sojojin Afghanistan Da Pakistan December 6, 2025 Iran Da Masar Sun yi Kira Da Kawo Karshen Keta Hurumin Gaza da Labanon da Isra’ila ke yi December 6, 2025 Qatar Tayi Gargardi Game Da Gakiyar Yarjejeniyar Gaza Matukar Isra’ila Bata Janye Ba December 6, 2025 Gwamnatin Najeriya Za ta Karbi Sabon Bashin Dala Miliyan 500 A Bankin Raya Kasashen Afrika December 6, 2025 Kungiyoyin Kare Hakkin Bil Adama Sun Yi Gargadi Game Da Yunkurin Isra’ila Na Kashe Barghusi December 6, 2025 Gasar FIFA: Iran Ta Fada Cikin Group Mai Sauki A Gasar Kwallon Kafa Ta FIFA 2026 December 6, 2025 Kasashen Musulmi 8 Sun Ki Amincewa Da Korar Falasdinawa Daga Gaza December 6, 2025 Sojojin Afganistan Da Pakistan Sun Yi Musayar Wuta A Tsakaninsu Duk Tare Da Tsagait Wuta December 6, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: sami zinariya
এছাড়াও পড়ুন:
An Kira Yi Gwamnatin Canada Da Ta Kama Olmert Da Livini Na “Isra’ila
Kungiyoyin kare hakkin bil’adama na kasar Canada sun shigar da kara ga jami’an ‘yan sandan kasar, da kuma ma’aikatar shari’a da su kama tsohon Fira ministan haramtacciyar kasar Isra’ila Ehud Olmert da kuma ministan harkokin waje Tzipi Livni bisa rawar da su ka taba a baya a laifukan yaki a Gaza a tsakanin 200-2009.
Kungiyoyin sun bukacin ganin an fitar da sammacin kamo ‘yan sahayoniyar biyu a bisa dogaro da dokokin kare hakkin dan’adama da laifukan yaki na kasar Canada, saboda kasar tana karkashin yarjejeniyar Geneva ta 4 da ta bukaci kasashe su hukunta masu irin wadannan laifukan.
Bugu da kari, kungiyoyin sun ce Olmert wanda ya yi fira minista daga 2006 zuwa 2009, shi ne mai rike da mukami na koli a lokacin hare-haren soja da su ka kashe fararen hula da lalata muhimman cibiyoyi. Haka nan kuma a wancan tsakanin sojojin Haramtacciyar kasar Isra’ila sun yi amfani da makamin Phosphorus mai fitar da farin hayaki da aka haramta amfani da shi a yake-yake. Sojojin na mamaya sun kuma rusa gidaje da lalata tsarin magudanan ruwa na kiwon lafiya, kamar kuma yadda su ka yi wa fararen hula da dama kisa ba tare da shari’a ba. Bugu da kari, sun hana shigar da kayan agaji zuwa yankin Gaza a wancan lokacin.
Ita kuwa Livini ta kasance memba a cikin karamar majalisar tsaro wacce ta taka rawa wajen shatawa sojoji ta’asar da su ka yi, ta kuma furta cewa, martanin da ya kamata “Isra’ila” ta mayar wa Falasdinawa ya kamata ya zama ” Na Hauka.”
Dama dai mutanen biyu suna da wata shari’ar da aka kai su kara a gaban kotuna daban-daban na kasashen turai. Kuma a 2009 ne wata kotu a Birtaniya ta fitar da sammaci a kamo su.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka An Kashe Shugaban ‘Yan Dabar Gaza “Abu Shabab” Da Isra’ila Ke Goyon Baya December 4, 2025 Iran : Jagora Ya Bayyana Ra’ayin Musulunci Kan Hakkokin Mata December 4, 2025 Taron IMO : Tehran Ta Yi Watsi Da Zarge-zargen Isra’ila Marasa Tushe December 4, 2025 MDD ta nemi a kawo karshen mamayar Isra’ila a Falasdinu da kuma Tuddan Golan December 4, 2025 Rundunar Ruwa ta IRGC na Gudanar Da Atisayen Soja a Tekun Fasha December 4, 2025 Dan wasan Taekwando Na kasar Iran Ya Samua Lambar Yabo Ta Zinariya December 4, 2025 Hamas Za ta Mikawa Isra’ila Samfurin Da Aka Samu A Karkashin Burabutsai A Gaza December 4, 2025 Iran: Tsaron Yankin Tekun Fasha Jan Layi Ne Da Za’a Fuskanci Mayar Da Martani Adan Aka Taba Shi December 4, 2025 Kungiyoyin Kare Hakkin Dan Adam Sun Kira Ga Kasar Kanada Ta Kama Olmert Da Livni December 4, 2025 Majalisa Ta Tabbatar Da Janar Christopher Musa A Matsayin Ministan Tsaro December 4, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci