Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 167
Published: 7th, December 2025 GMT
167-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshin wadanda suka zo cikin al-kur’ani mai girma, ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da Littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Murtada Muttari, ko kuma cikin littafin Mathnawa na Maulana Jalaluddeen Rumi, ko kuma cikin wasu littafan.
/////….Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan al-Mujtaba(a) dan Fatimah (s) diyar manzon Allah (s) da muke kawo maku. A cikin shirimmu da ya gabata munyi maganar
Dalilin da suka sa sojojin Imam Al-Hassan (a) suka kasa yakar sojojin Mu’awiya dan Abusufyan. Daga ciki mun bayyana cewa, kha’inci da son duniya a cikin sojojin Imam (a) ya ka suna son kama shi su mikawa mu’awiya don su su Aminta su kuma samu daukaka a wajensa.
Kamar yadda dan dan’uwan Sa’adu dan Mas’ud Athaqafi ya zo yana kudaitar da Amminsa ya kama Imam Al-Hassan (a) wanda yake jinya a gidansa ya mikawa Mu’awiya saboda ya sami aminci da da kuma daukaka. Munji da Sa’adu Athaqafi ya la’anesu ya kuma nisantar da shi, yana kuma neman tsarin Allah daga sharrinsa.
Daga ciki mun ambaci yadda Mu’awiya ya yada akidun karya dangane da banu Umayya a Sham, saboda jahilcinsu. Ya kirkoro hadidan karya ya jinginawa manzon Allah (s) tare da taimakon wasu sahabban manzon Allah wadanda suke tare da shi. Daga cikin wadan nan hadisan da suka kirkiro har da cewa Banu Umayya sune dangin manzon Allah (s) wadanda suka cancanci gadonsa.
Wannan akidar ta wanzu a kasar Sham har zuwa lokacinda Abul Abbas wanda aka fi saninsa da Saffah, sarki na farko daga cikin sarakunan Abbasiyawa ya kwace kasar Sham, sannan shuwagabannin manya manyan kungiyoyi da kabilu suka zo masa, suna rantsewa da Allah kan cewa basu taba sanin cewa manzon Allah (s) yana da dangi wadanda suka cancanci gadonsa ba in banda banu umayya.
Dangane da wannan Ibrahim dan Muhajir Al-Bajali mutumin Kufa yayi wata kisida yana fada a cikinta, yana cewa
Ya ku mutane ! Ku Saurara, Zan baku labarin * Abin mamaki, wanda yafi ban mamaki .
Abin mamaki daga Abdushamsi (banu umayya), Lalle su* Sun budewa mutane Kofofin karya.
A riyawarsu, Sun gaji Ahmadu (manzon Allah(a))* Amma banda amminsa Abbas dan Abdul Muttalib.
Sun yi karya, na rantse da Allah, bamu sans hi ba* Kan cewa ba wanda zai sami gado sai sai wanda yake kusa.
Malaman tarihi sun bayyana cewa, mutanen sham- saboda wadan nan hadisan karya, wadanda Mu’awiya da abokan aikinsa suka yada a cikinsu, suna ganin sarakunan banu umayya sarakunan addinin musulunci ci, kuma Mu’awiya khalifan Allah ne a bayan kasa. Haka ma dansa Yaziz (la’anenen wanda ya kashi jikan manzon Allah (s) wato Imam Al-Hussain (a), to shi ma khalifan Allah ne a bayan kasa).
Wadan nan al-amura suka sa mutanen sham suke matukar biyayya ga Mu’awiya dan Abusufyan, haka ma sauran sarakunan banu Umayya da su zo bayansa, har saida al-amura suka bayyana bayan faduwar daularsu kimani shekaru 80 bayan da mu’awiya ya kwace iko daga hannun Imam Al-hassan (a).
Sannan mu’awiya ya yi amfani da damar da ya samu na biyayyar da mutanen sham suke masa, ya nesantar da su daga addinin musulunci na gaskiya, da gangan yake sabawa sharia ya kuma sabawa sunnar manzon Allah (s).
Sannan saboda irin biyayyar da mutanen sham sukewa Mu’awiya, Amirul muminina Aliyu dan Abitalib (a) yayi gurin, ina ma yana da Mabiya, wadanba basa sabawa umurnin shugabansu kamar yadda mutanen sham suke biyayya ga mu’awiya har yana fadawa mutanen Iraki wani lokaci, ina da za’a yi masa musayar daya daga cikinsu da mutum 10 daga cikin Irakawa. Wadanda ba abinda aka sansu da shi sai tashe tashen hankula da jayayya da shuwagabanninsu. Shugabansu ya fada su fada.
Sannan mutanen sham, kafin shigarsu addinin musulunci su kiristoci ne, karkashin daular Ruma da gabas wanda yake jagorantar yankin daga kasar Turkiya a lokacin. Don haka sun saba da gwamnatin da biyayya ga shugaba da kuma tsarin rayuwa mai nutsuwa, ba kamar larabawa kafin musulunci ba.
Don haka su mutanene masu saukin hali, amma basu da wayo ko kuma amfani da hankali a cikin al-amura don fahintar gaskiya. Danga ne da wannan malaman tarihi sun bayyana cewa, bayan yakin siffin wani mutumin Iraki ya je kasar Sham da rakuminsa, sai ya hadu da wani mutumin sham wanda yace ai rakumin nasa nasa. Ragima da shiga tsakaninsu, har suka je gaban Mu’awiya.
Mutumin sham ya kawo shaidu kimani 50 suka tabbatar da cewa rakumin na miji nasa ne, sai mu’awiya ya yanke hukunci kan cewa a mayarwa mutumin sham, rakumin.
Sai mutumin Iraki ya fadawa Mu’awiya ai wannan taguwa ce (macce ba rakumi) na mijiba!.
Amma sai mu’awiya yace masa hakunci ya rika wuce ka mayarma da damar. A lokacinda aka watse, sai mu’awiya ya aika a kira mutumin Iraki ya zo. A lokacinda ya zo, sai yace masa nawa kudin taguwarka sai ya fada, sai ya ninka masa ya kuma fada masa, idan ka je Iraki ka fadawa Aliyu dan Abitalib (a) kan cewa, na tanaji mutanen sham dubu 100 don yakarsa, ba wani daga cikinsa wanda yake iya bambata tsakanin rakumi na miji da taguwa ta mace.
Wannan ya nuna irin rashin wayewa da fahintar mutanen sham a lokacin, don haka Mu’awiya ya yi amfani da jahilcinsu ya yakar iyalan gidan manzon Allah (a) da su. Ya sauya al-amura da dama na addini, ya kuma takurawa iyalan gidan manzon Allah (a) da mabiyansu, ya sunnata kashesu da la’antarsu a kan mimbarorin musulmi na tsawon shekaru kimani 60 bayan sulhuntawa da Imam Al-Hassan kamar yadda zamu gani a nan gaba.
Don haka Mu’awiya ya barsu cikin jahilci, cikin duhu bayan duhu, suna masu dimwa a cikin al-amarinsu, baya barin wani ya zo ya farkar da su ko kuma su su je wani wuri a cikin daular musulunci inda zasu gano gaskiyan al-amari. Su gano kariyar Mu’awiya da kuma banu umayya gaba daya.
Sai kuma rarraba da hadin kai, kasar Sham bata da rarrabar kai na akidu da kuma kabilanci wanda ake da su a kasar Iraki.
Don haka su kalma guda ce ta hada su, basa da sabani a tsakaninsu, akidar Khawarijawa bata shigo masa ba. Hakama basa da matsala tsakanin shuwagabannin kabilu da Mu’awiya. Yana bawa shuwagabannin kudaden da suka gabata don su rike masa kabilunsu. Iran wannan kabilun Iraki suke nema amma Ahlul Baiti suka bayyana hakan ya sabawa adalci. Rabon shugaban kabila shi ne rabon mabiyansa. Ba’a bashi fiye da rabonsa.
Don haka hadin kan da aka samu a cikin gida yana da cikin sirrin nasarorin da Mu’awiya ya yi ta samu a kan sojojin Imam Al-Hassan (a).
A wani bangare kuma Mu’awiya ya karfafa sojojinsa ne bayan da ya sami hadin kai a cikin gida. Ya sulhunta da daular Roma da ta rage a lokacin, ya kuma bata kudade masu yawa don kada ta tada masa yaki.
Sannan a cikin gida ya na karban haraji mai yawa a wajen mutane, yana karban zakka hatta a cikin kayakin da ba’a masu zakka.
Mun san cewa dukiyoyi iri 8 ne ake masu zakka, amma Mu’awiya yana karban zakka. Kuma yana matsawa kwarai wajen karban zakka da kuma haraji. Mu’awiya ya tilasta wa mutanen sham bada abinda ake kira da Farisanci :hadayar Niruz” wanda babu a cikin addinin musulunci.
Niruz sabuwar shekara ce ta Iraniyawa da kuma kabilun da suke yankin Asiya kamar Kurdawa da sauransi, musulunci bai san da shi ba. Ya kuma halatta wasu abubuwan da shari’a ta haramta, mai yuwa bai san shari’a ta haramta su ba, amma sau da dama da gangan yake sabawa addinin musulunci yana sani da matsayinsa.
Wani lokaci yakan halatta wani abu ko ya haram tashi da gangan don ya sabawa sharia. Da kuma kuma ya sauka abubuwan adiinin, kama daga hukunce-hukunce zuwa ibada da sauranci, kuma da gangana.
Har’ila yau Imam Al-Hassan (a) ya ki mutanen kufa ne bayan sun kashe mahaifinsa Amirul muminina (a) . Muntum wanda yake rayuwa a cikinsu, cikin talaunci, sannan yana matukan kokari wajen ganin sun rayuwa cikin jin dadi, da kuma adalci a tsakaninsu. Yana rayuwa cikinsu kamar rayuwar daya daga cikinsu. Amma sai wasu daga cikinsu suka fito suka kasheshi ba tare da yayi masu laifi ba, ba tare da dauki dukiyoyinsu, ba tare da ya tsokanesu. Wannan al-amarin ya bar tabo babba a zuciyar Imam Al-Hassan (a) kuma tun lokacin yake taka tsantsan da su. Yake kuma ganin basu cancanci su zana mataimakansa ba. Saboda laifukan da suka aikata, na kashe mahaifinsa, wasiyin kakansa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 166 December 7, 2025 Rwanda Da Amurka Sun Rattaba Hannu Kan Tallafin Dalar Amurka Miliyon $228 Na Kiwon Lafiya December 7, 2025 Amurka: Mun Yi Kokarin Kifar Da Gwamnatin JMI Har Sau Biyu Ba Tare Da Samun Nasara Ba December 7, 2025 Iran Ta Gargadi Kasashen Larabawa Dangane Da Tsibiran Kasar Guda Uku A cikin Tekun Farisa December 7, 2025 Hamas Tace Zata Mikawa Gwamnatin Falasdinawa Makamanta Idan An Kawo Karshen Mamaya December 7, 2025 Venezuela: Ba Mu Tsoron Kaudin Amurka Na Wuce Gona Da Iri December 7, 2025 Iran Ta Zama Zakaran Duniya A Wasan “Taekwondo” Na Masu Shekaru Kasa Da 21 December 7, 2025 Afirka Ta Kudu: An Kashe Mutane 11 A Wani Bude Wuta Na Kan Mai Uwa Da Wabi December 7, 2025 Dubban Mutane Suna Guduwa Daga Gabashin DRC Saboda Barkewar Sabon Fada December 7, 2025 Mutane Biyar Ne Suka Mutu A Wata Musayar Wuta Tsakanin Sojojin Afghanistan Da Pakistan December 6, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: wadanda suka mu awiya ya da mu awiya banu umayya Mu awiya ya da Mu awiya Mu awiya da
এছাড়াও পড়ুন:
Sabuwar Dokar CBN: Nawa Za a Iya Cirewa a ATM da POS?
Yanzu ƴan Najeriya za su iya cire naira 100,000 ta na’urar cire kuɗi ta ATM a rana, haka ma abin yake a ɓangaren cire kuɗi ta na’urar POS.
A ɓangaren ma’aikatu kuma, za su iya cire kuɗi har naira miliyan biyar ne a duk mako.
Wannan na ƙunshe ne a cikin sabbin tsare-tsaren da Babban Bankin Najeriya CBN ya fitar bayan garambawul da ya yi kan dokokin cire kuɗi ta na’urar ATM da POS a Najeriya.
Bankin ya ce wannan sabuwar dokar za ta fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2026.
A cikin wata sanarwa da daraktan tsare-tsare na bankin, Dr Rita Sike ta fitar a ranar Talata 2 ga watan Disamba, ta ce babban bankin ya yi gyara ne a kan dokokin kuɗin da za a iya cirewa.
Amma idan mutum ya cire kuɗi sama da ƙa’idar da aka ƙayyade a mako, mutum zai biya wani adadi na kuɗin.
Ya kamata ƴan Najeriya su fahimci cewa ida suka shiga cikin banki suka cire naira 100,000, shi ma yana cikin kuɗin da suka cire a rana.
Hakan na nufin za a ƙirga shi a cikin kuɗin da mutum ya cire a makon, kamar ya cire ta ATM ko POS.
Me ya sa aka yi canjin?Kamar yadda sanarwar ta nuna, an tsara tsohuwar dokar ce domin rage ta’ammali da tsabar kuɗi da magance matsalolin tsaro da ma daƙile sama da faɗi da kuɗaɗe da sauran abubuwan da ake tunanin ba su da sauƙi sai da tsabar kuɗi.
Sauran dokokin sun haɗa da:
Cire kuɗi mai yawa – Idan ka cire kuɗi sama da adadin da ƙayyade, za ka biya kashi uku, idan kuma ma’aikata ce za ta biya kashi biyar na kuɗin.
Amfani da takardar karɓar kuɗi a banki – Idan ka tura wani da takardar karɓar kuɗi wato ‘check’, shi ma za a ƙirga a cikin adadin kuɗin da ka cire a mako.
Yadda aka fara dokarA watan Disamban 2022 ne babban bankin Najeriya ya sanar da cewa daga ranar 9 ga wata Janairun 2023, ɗaiɗaikun mutane ba za su cire kuɗi sama da naira 100,000 ba, ma’aikatu kuma naira 500,000.
Sannan a lokacin bankin ya ce adadin kuɗin da za a iya cirewa ta na’urar POS shi ne naira 20,000.
Haka kuma a lokacin bankin ya ƙayyade cewa ƙananan takardun kuɗi irin su naira 200 zuwa ƙasa ne za a riƙa sakawa a ATM.
Bankin ya fitar da tsare-tsaren ne bayan fitar da sababbin takardun kuɗi a Najeriya.
Idan mutum zai cire sama da adadin, zai biya kashi biyar, ma’aikatu kuma za su biya kashi 10.
A baya, kuɗin da mutum zai iya cirewa ta na’urar ATM naira 100,00 ne a mako, amma mutum naira 20,000 kawai zai iya cira a kullum, amma a POS kuma, naira 20,000 kawai za a iya cirewa.