Aminiya:
2025-12-06@17:17:46 GMT

Nakiya ta hallaka yara 4 a Borno

Published: 6th, December 2025 GMT

Wata nakiya da ta fashe a garin Banki, da ke Ƙaramar Hukumar Bama, a Jihar Borno, ta yi sanadin mutuwar yara huɗu tare da jikkata wani yaro guda ɗaya.

Rundunar ’yan sandan jihar, ta tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Juma’a.

Kwastam ta kama jirgin ruwan Brazil ɗauke da hodar iblis a Legas Ranar Sabuwar Shekara za mu rufe duk na’urar POS mara rajista —Gwamnati

Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 12:40 na rana a bayan tashar motar Banki da ke yankin Wajari.

Wani mazaunin garin, Babagana Mohammed, ya kai rahoton fashewar nakiyar da misalin ƙarfe 1 na rana, wanda hakan ya sa aka tura jami’an tsaro zuwa yankin.

DPO na Banki tare da ƙwararrun sashen cire bam, sun killace wajen domin kare jama’a da kuma fara bincike.

An gano cewa wani yaro mai shekaru 12, Mustapha Tijja, ya samu munanan rauni, kuma an kai shi asibitin FHI 360 da ke Banki, inda ake kula da shi.

Rahotanni sun nuna cewa yaron da ya tsira da ransa, yana tare da abokansa huɗu a bayan tashar motar.

Sun samu wani abun fashewa da ake zargin ajiye shi aka yi a wajen, wanda ya fashe yayin da suke wasa da shi.

Yaran da suka rasu sun haɗa da Awana Mustapha mai shekaru 15, Malum Modu mai shekaru 14, Lawan Ibrahim mai shekaru 12 da Modu Abacha mai shekaru 12

Rundunar ’yan sandan jihar, ta ce al’amura sun daidaita a yankin, yayin da a gefe guda ta ke ci gaba da bincike.

Kwamishinan ’yan sandan Jihar, CP Naziru Abdulmajid, ya bayyana alhininsa kan faruwar lamarin, tare da bayyana cewa rundunar tana gudanar da bincike.

Ya gargaɗi jama’a cewa: “A guji taɓa ko wasa da duk wani abu da ba a saba gani ba. Duk abun da ake zargi, a gaggauta sanar da jami’an tsaro.”

Rundunar ta bayyana lambobin kiran gaggawa da jama’a za su yi amfani da su don kai rahoto: 0806 807 5581 da 0802 347 3293.

Kakakin rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya ce rundunar za ta ci gaba da aiki tuƙuru wajen tabbatar da tsaro da hana irin waɗannan abubuwan faruwa a gaba.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Sanda Nakiya rasuwa wasa yara mai shekaru

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan bindiga sun harbe ɗan sanda har lahira a Edo

An harbe wani jami’in ɗan sanda har lahira, yayin da yake tsaka da binciken ababen hawa a Benin a Jihar Edo.

Kakakin rundunar, CSP Moses Yamu, ya ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 12 na ranar Juma’a, lokacin da jami’an rundunar suka tsayar da wata baƙar mota ƙirar Lexus, amma ta ƙi tsayawa.

’Yan sanda sun ceto yara 2 da aka yi garkuwa da su a Borno Ƙasashen waje na taimaka wa ’yan ta’adda a Najeriya —Sheikh Gumi

Ɗaya daga cikin mutanen da ke cikin motar ya buɗe wa jami’an da ke shingen wuta, sannan suka tsere.

A dalilin haka ne suka harbe wani ɗan sanda wanda ba a bayyana sunansa ba har lahira.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Monday Agbonika, ya umarci a farauto waɗanda suka aikata laifin.

Ya roƙi jama’a su bayar da sahihan bayanai, musamman idan suka ga irin wannan motar da aka zayyana.

Rundunar ta tabbatar wa jama’a cewa an ƙara tsaurara tsaro a faɗin jihar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ’Yan bindiga sun harbe ɗan sanda har lahira a Edo
  • ’Yan sanda sun ceto yara 2 da aka yi garkuwa da su a Borno
  • Shettima Ya Taya Sarkin Gumel Murna Tare da Jinjinawa Gwamna Namadi Bisa Bunkasa Bangaren Noma
  • Gwamnatin Gombe da UNICEF sun tallafa wa yara masu fama ƙarancin abinci mai gina jiki
  • Jami’an tsaro sun kama masu garkuwa da mutane 7 a Gombe
  • An harbe manomi saboda rikici kan filin kiwo a Borno
  • ’Yan sandan Borno sun kama matashin da ake zargi da kashe makwabciyarsa da wuƙa
  • ’Yan sanda sun kama mutum 28 kan zargin lalata mata da yara a Yobe
  • Tinubu ya san dalilin da ya sa na yi murabus daga muƙamin ministan — Badaru