Ya soka wa budurwarsa wuka har lahira
Published: 19th, August 2025 GMT
Wani mutum ya soka wa budurwarsa mai suna “Ima” wuka har lahira a unguwar Okereke Street da ke garin Fatalkwal na Jihar Ribas.
Mutumin, wanda ake wa lakabi da “Doctor” ya daba wa budurwar tasa mai suna “Ima” wuka ne bisa zargin tana cin amanarsa.
Lamarin ya faru ne da yammacin Lahadi, wanda shaidu a unguwar suka ce ya samo asali ne daga zargin da Doctor ke yi wa Ima, wanda ya rikide zuwa tashin hankali.
Mai kula da gidan da lamarin ya faru ya kai rahoto ofishin’yan sanda na Azikiwe Division, Mile 2 Diobu, wanda hakan ya kai ga cafke wanda ake zargi.
’Yan bindiga sun yi hatsari bayan karbar kudin fansa Mutane 62 da aka sace sun tsere daga hannun ’yan bindiga a KatsinaRahotanni sun nuna cewa an kai gawar zuwa wani gidan ajiyar gawa da ba a bayyana ba a Fatakwal.
Prince Wiro, Shugaban Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam da Inganta Gaskiya, ya bukaci a gudanar da bincike mai zurfi da adalci.
Ya ce, “Mun ga yadda aka dauke gawar zuwa gidan ajiyar gawa yayin da ake tsare wanda ake zargi. Muna kira ga ’yan sanda da su gudanar da bincike mai adalci domin tabbatar da gaskiya.”
Ya kuma shawarci matasa da su guji dangantaka mai cike da tashin hankali: “Ba a bukatar mutum ya zauna cikin dangantaka mai cutarwa. Rayuwarka ta fi kowace dangantaka muhimmanci.”
Kakakin ’yan sanda na Jihar Ribas, SP Grace Iringe-Koko, ba ta amsa kiran waya ko sakon da aka tura mata dangane da lamarin ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: budurwa masoya Masoyiya zargi
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Daga Zuwa Mataki Na 10 A Jadawalin GII Na Kasashen Dake Kan Gaba A Fannin Kirkire-Kirkire
Cikin jadawalin GII na 2025, kasashe masu karanci da matsakaicin kudin shiga 17, sun taka rawar gani fiye da yadda aka yi hasashe, bisa matsayin ci gabansu, yayin da kasashen Afirka dake kudu da hamadar Sahara ke kan gaba, cikin kasashe mafiya samun ci gaban kirkire-kirkire, inda kasashen Afirka ta Kudu, da Senegal da Rwanda ke kan gaba a jerin kasashen shiyyar. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp