Fadar Shugaban Kasar Benin ta ce Har Yanzu Talon Ne a Kan Mulki
Published: 7th, December 2025 GMT
Gwamnatin Jamhuriyar Benin ta bayyana cewa ta dakile wani yunkurin juyin mulki, bayan da wasu sojojin ƙasar suka sanar da cewa sun hambarar da shugaba Patrice Talon a gidan talabijin na kasar.
Talon, mai shekaru 67, tsohon dan kasuwa ne wanda aka yiwa lakabi da “Sarkin Auduga na Cotonou”, zai mika mulki a watan Afrilun shekara ta 2025 dake ƙaratowa, bayan shafe shekaru 10 a kan karagar mulki wanda ke nuna samun ci gaban tattalin arziki mai inganci.
Da sanyin safiyar Lahadi ne sojojin da ke kiran kansu da suna “Kwamitin Soji na sake farfado da ƙasa” (CMR), suka gabatar da wata sanarwa a gidan talabijin na kasar cewa sun gana kuma sun yanke shawarar cewa “An tsige shugaba Patrice Talon daga mukamin shugaban jamhuriyar”.
Sai dai jim kadan bayan sanarwar, wata majiya da ke kusa da Talon ta shaida wa kamfanin dillacin labaru na AFP cewa shugaban yana cikin koshin lafiya tare da yin Allah wadai da masu yunkurin juyin mulkin.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
An harbe manomi saboda rikici kan filin kiwo a Borno
Rikici kan filin kiwo tsakanin wani makiyayi da wani manomi ya yi sanadin mutuwar wani manomi mai shekaru 32 a kauyen Muva da ke cikin karamar hukumar Askira/Uba a jihar Borno.
Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa, a ranar 2 ga watan Disamba, 2025, da misalin karfe 4:00 na yamma, Alhaji Usman, wanda ke kiwon shanu, ya samu rashin jituwa da Jauro Ishaya mai shekaru 43, kan rikicin filin kiwo.
A cewar majiyar, yayin takaddamar ne aka zargi Jauro Ishaya da harba bindigar gida wadda ta sami Alhaji Usman a ciki, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa.
An garzaya da wanda abin ya shafa zuwa babban asibitin Askira, amma likitoci suka tabbatar da mutuwarsa nan take.
Rundunar ’yan sandan jihar ta ce ta kama wanda ake zargi, kuma tana ci gaba da kokarin kwato bindigar da aka yi amfani da ita a lamarin.
Majiyoyi sun kara da cewa, sashen binciken manyan laifuka (CID) na rundunar ’yan sanda a Maiduguri ya fara gudanar da bincike kan lamarin.