2025-10-20@10:45:15 GMT
إجمالي نتائج البحث: 226
«yan awaren IPOB»:
Hamshakan attajirai da ’yan siyasa sun bayar da gudunmawar sama da Naira biliyan 16 a bikin kaddamar da littafin tarihin tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida. Taron ƙaddamar da littafin, mai suna ‘A Journey in Service’, wanda aka gudanar a Abuja ya tara manyan baƙi daga ciki da wajen Najeriya. Mahalarta...
“A watannin da suka gabata, masu ruwa da tsaki a cikin dillalan sun nuna damuwa game da hauhawar farashin kayayyakin abinci. Yanzu da farashin ya ragu, kamar garin da ya fadi daga naira 81,000 a kowace buhu zuwa kasa da naira 60,000, da taliya wanda ya fadi daga naira 20,000 zuwa naira 15,000. “Adalci ne...

Babban Jami’i A Kungiyar JIhadul-Islami Ya Ce: Gudumawar Marigayi Sayyid Hasan Nasrullahi Ba Zai Fadu Ba
Jimi’in ofishin siyasa na kungiyar jihadul-Islami ya bayyana cewa: Marigayi Sayyid Hasan Nasrallah ya baiwa Falastinu da gwagwarmaya abin da harshe ba zai iya siffanta shi ba Mamba a ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmaya ta Jihadul-Islami ta Falasdinu Ihsan Ataya ya yaba da irin tsayin dakan da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi a...
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yabawa tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) bisa irin gudunmawar da ya bayar ga ci gaban Najeriya. Shugaban kasar a bayyana hakan ne a lokacin kaddamar da tallafin, tarihin rayuwar Janar Babangida da gwagwarmayarsa yayin aiki, wanda aka gudanar a Abuja. A yayin da...
An yi zaman farko na tattaunawar sulhu a tsakanin kasashen Habasha da Somaliya a birnin Ankara wanda kasar Turkiya take a matsayin mai shiga tsakani. Ministan harkokin wajen kasar Turkiya Hakan fidan ya yi ganawa da daban-daban da ministocin harkokin wajen kasashen na Habasha da Somaliya. Bayan wannan ganawar minstan harkokin wajen na Turkiya ya...
Taron dai na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da majalisar dattawan kasar a ranar Laraba ta gayyaci shugabannin hukumar leken asiri don gudanar da bincike kan zargin da dan majalisar dokokin Amurka, Perry Scott ya yi na cewa, hukumar bayar da tallafi ta kasa da kasa ta Amurka, USAID na tallafa wa kungiyoyin ta’addanci ciki...
Kasar Sin na maraba da duk kokarin da ake yi cikin lumana don warware rikicin kasar Ukraine, ciki har da tattaunawa tsakanin Amurka da Rasha, kuma Sin na fatan dukkan bangarori da masu ruwa da tsaki za su shiga cikin shawarwarin samar da zaman lafiya in lokaci yayi. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo...
Hukumar Ƙididdiga ta Nijeriya NBS ta ce alƙaluman hauhawar farashi sun koma kashi 24.48 daga 34.8 cikin 100 a watan Janairun da ya gabata. Wannan ne karon farko da hukumar ta NBS ta fitar da rahoton bisa sabon tsarin tattara alƙaluma da ta fara amfani da shi, abin da ke nufin da wuya a iya...
Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar NNPP ita ma ta shiga cikin rikici, inda ake zargin Kwankwaso ne ke jagorantar daya daga cikin bangarorin jam’iyyar. A makon da ya gabata ne wani bangare na jam’iyyar NNPP karkashin jagorancin wanda ya assasa jam’iyyar, Dakta Boniface Aniebonam ya gudanar da babban taro a...
Gwamnatin jihar Kano, KNSG, ta ce ta tanadi hanyoyin dakile mace-macen mata masu juna biyu maimakon rage yawan mace-macen. Kwamishinan lafiya na jihar Dr Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a wajen taron hadin gwiwa na Partners Coordination Forum (PCF) da aka gudanar a Kano. A wata...
Ma’aikatar harkokin wajen Sin ta sanar a yau Alhamis cewa, firaministan kasar Li Qiang, zai halarci bikin rufe gasar wasannin lokacin hunturu ta kasashen Asiya karo na 9, wanda za a yi gobe Juma’a a Harbin, babban birnin lardin Heilongjiang na kasar Sin. Li Qiang zai kuma shirya liyafar maraba da shirye shiryen da suka...
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya jaddada buƙatar samar da manyan gonakin gudanar da noman rani domin yaki da matsalar karancin abinci a Yankin Tafkin Chadi. Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin taron Gwamnonin Tafkin Chadi da aka gudanar makon da ya gabatar a garin Maiduguri fadar Jihar Borno karo na biyar,...

Jaridar Telegraph Ta Ce; Shugabannin Sojojin Iran Sun Bukaci Jagora Da Ya Soke Fatawar Haramci Kera Makamin Nukiliya
Jaridar Daily Telegraph ta watsa labarin cewa: Shugabannin Iran sun bukaci Jagoran juyin juya halin Musulunci Sayyid Khamenei da ya janye fatawarsa kan haramcin mallakar makamin nukiliya Jaridar Daily Telegraph ta kasar Birtaniya ta watsa rahoton cewa: Shugabannin sojojin Iran sun bukaci Jagoran juyin juya halin Musulunci Sayyid Ali Khamenei ya yi watsi da haramcin...
Wani Mataimakin Sufeton ’Yan Sanda (ASP), Shafi’u Bawa, da ke aiki da Rundunar 61 Police Mobile Force a Kontagora da ke Jihar Neja, ya hallaka kansa har lahira. Wani jami’in dan sanda ya shaida wa Aminiya cewa, lamarin ya faru ne a ranar Asabar. Gwamnatin Kano ta dakatar da wani fim mai suna Zarmalulu Aisha...
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya sha alwashin gyara wa da faɗaɗa sansanin horas da matasan maus yi wa ƙsa hidima (NYSC) na dindindin a jihar. Da yake karɓar babban Daraktan NYSC, Birgediya Janar Yusha’u Ahmed a Maiduguri, Zulum ya ce gwamnatinsa za ta gaggauta gina sansanin dindindin domin karɓar ƙarin ‘yan bautar ƙasa....
Gwamnan ya bayyana haka a yayin wata ziyarar ta’aziyya da ya kai yankin na Rimin Zakara a yammacin ranar Alhamis 06, ga watan Febarairun 2025. A yayin ziyarar l, gwamnan ya yi alkawarin gina wa jama’ar yankin na Rimin Zakara katafaren Masallacin Juma’a a matsayin sadaka jariya ga wadanda suka rasu a dambarwar filayan...
An tsinci gawar mai shari’a Azuka, Ɗan Majalisa mai wakiltar mazaɓar Onitsha ta Arewa a Majalisar Dokokin Jihar Anambra. An gano gawar Azuka da aka sace a jajibirin Kirsimeti a shekarar 2024 a kan gadar 2nd Niger Bridge, a cikin Anambra, ranar Alhamis. Uwa ta fusata ta jefa ’yarta cikin kogi a Bayelsa Yadda matar...
Wasu ma’aurata sun tsinci gawarwakin kananan ’ya’yansu uku a boye a cikin wani firinji a yankin Nnewichi da ke Nnewi a Jihar Anambra. Iyayen yaran, Mista Udochukwu da Misis Chikazor Ejezie, sun tsinci gawar ’ya’yan nasu a cikin firinji ne bayan da suka dawo gida daga wurin aiki. Bayan dawowarsu ne suka samu gidan a...
Wasu ma’aurata sun tsinci gawarwakin kananan ’ya’yansu uku a boye a cikin wani firinji a yankin Nnewichi da ke Nnewi a Jihar Anambra. Iyayen yaran, Mista Udochukwu da Misis Chikazor Ejezie, sun tsinci gawar ’ya’yan nasu a cikin firinji ne bayan da suka dawo gida daga wurin aiki. Bayan dawowarsu ne suka samu gidan a...

Mutanen Amurka Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Goyin Bayan Falasdinawa Bayan Tattaunawar Trump Da Natanyahu Dangane Da Gaza
Mutanen kasar Amurka sun fito zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da korar Falasdinawa daga Gaza ne, bayan taron da yan jaridu na Trump Da Natanyaho a birnin washintong a jiya Talata. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto masu zanga-zangar su na rera taken cewa “gaza ba na sayarwa bane”. Maganganun Trump a baya-bayan...
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) a Jihar Kano ta gargaɗi al’umma kan wata alawar yara mai da sanya maye, da ke yawo a gari. Hukumar ta gargaɗi, musamman iyaye da su yi hattara da alawar da sauran kayan tanɗe-tanɗe da ke ɗauke da sinadarai masu sanya maye. Kakakin Hukumar a jihar, ASN...
A hannu guda kuma, Gwamnan ya yi kira ga sojoji da sauran bangarorin jami’an tsaro da su kara kaimi wajen fadada yin sintiri a yankunan da ke kan iyakokin jihar, domin dakile shigowar yan ta’adda cikin jihar. A nashi bangaren, Babban Hafsan Sojojin Nijeriya, ya sake baiwa Gwamnan tabbacin cewa sojoji za su ci gaba...
A cewar wani rahoto da kamfanin nazarin al’amuran yau da kullun da siyasa a Najeriya (SBM Intelligence) ya gabatar, tsakanin shekara ta 2011 zuwa 2020, an biya akalla dala miliyan 18.34, wanda ya yi daidai da Naira biliyan 23; ga masu garkuwa da mutane a matsayin kudin fansa. Ko shakka babu, garkuwa da mutane ya...
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira da a gaggauta kwashe yara 2,500 da suka jikkata a yakin da Isra’ila ta kwashe watanni 15 tana yi a Gaza domin samun kulawar gaggawa. Rokon nasa ya biyo bayan ganawar da ya yi da likitocin Amurka ne wadanda suka yi gargadin cewa yaran...
Tinubu ya gode wa shugaban Bankin Duniya, Ajay Banga, da shugaban Bankin Raya Ƙasashen Afirka, Akinwumi Adeshina, saboda ƙoƙarinsu na samar da karin wutar lantarki a Afirka. Ya kuma ce yadda masu zuba jari ke gamsuwa da shirye-shiryen gwamnatinsa ya sa aka samu jarin dala biliyan shida a ɓangaren samar da makamashi a shekarar da...
Ya kuma yi gargadi cewa rashin ɗaukar matakai na gyara tattalin arziƙi zai ci gaba da haifar da asara mai yawa, inda tallafin man fetur da na musayar kuɗaɗe ke laƙume kashi biyar cikin ɗari na GDP na ƙasar. Wannan, in ji shi, babban ƙalubale ne ga cigaban tattalin arziƙin Nijeriya.