Aminiya:
2025-11-03@05:19:43 GMT

An tara Naira 16 a taron ƙaddamar da littafin IBB

Published: 21st, February 2025 GMT

Hamshakan attajirai da ’yan siyasa sun bayar da gudunmawar sama da Naira biliyan 16 a bikin kaddamar da littafin tarihin tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida.

Taron ƙaddamar da littafin, mai suna ‘A Journey in Service’, wanda aka gudanar a Abuja ya tara manyan baƙi daga ciki da wajen Najeriya.

Mahalarta taron da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis sun bayar da gudunmawar ne domin ginin dakin karatun da tsohon shugaban ƙasan ke shirin ginawa. Attajiri mafi yawan arziki a Afirka kuma Shugaban Rukunin Kamfanonin Ɗangote, Alhaji Alikon Ɗangote ya ba da gudunmawar Naira biliyan takwas, Naira biliyan biyu a duk shekara, na tsawon shekara huɗu. Ya kuma yi alƙawarin karin biliyan biyu a duk shekara har a gama aikin. NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ba Za Mu Sauke Farashin Burodi Ba —’Yan kasuwa Ba ni da hannu a kisan Dele Giwa — Janar Babangida

A nasa ɓangaren, Shugaban Rukunin Kamfanonin BUA, ya ba da gudunmawar Naira biliyan biyar.

Tsohon Ministan Taro kuma Shugaban Gidauniyar TY, Janar Theophelus Ɗanjuma, ya bayar da Naira biliyan uku.

Babban attajiri a yankin Kudu, Arthur Eze, ya ba da Naira miliyan 500.

Sanata Sani Musa ya ba da miliyan N250 a yayin da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ba da miliyan N50.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Barau Jibrin ya ba da Naira miliyan 20 a yayin da Sanata Aliyu Wadada ya ba da miliyan 10.

Hamshakiyar ’yan kasuwa Folorunsho Alakija, da wasu fitattun ’yan Najeriya sun bayyana gudunmawa, amma ba su sanarna bainar jama’a ba.

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci tsoffin shugaban kasa na farar hula na mulkin soji irinsu Goodluck Jonathan, Yakubu Gowon, Abdulsalami Abubakar, da wasu manyan baƙi.

Tsoffin mataimakan shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar da Muhammad Namadi Sambo da Yemi Osinbajo.

Hakazalika dan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar NNPP Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da takwaransa na Jam’iyyar LP, Peter Obi, sun samu halartar.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Naira biliyan da gudunmawar

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori

Bug da kari Tinubu ya jinjina wa Shugaban jami’ar, Farfesa Wahab Olasupo Egbewole (SAN)da ‘yan tawagarsa wajen maida hankalin da suka yi na bunkasa Jami’ar da kumna kudurinta na muradun ci gaban da ake bukata.

Shi ma anashi jawabin Shugaban Jami’ar Sarkin Katsina, Alhaji. Abdulmumin Kabir Usman, wanda Wazirin Katsina, Sanata Ibrahim Idah ya wakilta, ya nuna jin dadinsa kan irin kokarin da UNILORIN saboda bunkasar ilimi da kumasamar wuraren koyon kaaratu masu kyau da kuma suka dace.

Ya yi ma kallon ayyukan da ak kaddamar a matsayin“ irin abubuwan da ake bukatar gani ke nan”da za su taimakawa lamarin koyarwa, koyo,da kuma bincike, inda ya kara da cewa yadda Jami’ar ta maida hankalinta wajen bunkasa dabarar koyon yin abubuwa zai taimakawa dalibai su tashi da sun koyi abubuwan da zasu yi baya rayuwar da suka yi cikin aji.

A nashi jawabin mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa. Egbewole ya nuna farin cikinsa da godew a Shugaban kasa Tinubu kan yadda ya amince da gaiyar da Jami’ar ta yi ma shi, da kuma taimaka mata wajen tafiyar da bunkasar abubuwan jin dadi.

“Muna nan muna sa ido saboda ci gaban samun abubwan da suke taimakawa ci gaba kwarai da gaske a kowace rana kamar yadda yace yana da amincewa da yardarm ci gaba da samun hakan’’.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna November 1, 2025 Manyan Labarai Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami November 1, 2025 Manyan Labarai Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 20, Sun Ceto Mutane 17 Da Aka Yi Garkuwa Da Su November 1, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugaban AmurkaTrump ya yi barazanar daukar matakin soji kan Najeriya
  • Rikicin PDP: Tsagin Wike ya dakatar da Damagum
  • Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori
  • Shugaban Kasar Najeriya Ya Mayar Da Martani Ga Takwaransa Na Amurka Akan Rikicin Addini
  • Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung 
  • Sanata Sunday Marshall Katung Ya Sauya Sheka Zuwa Jam’iyyar APC
  • An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3
  • An yi garkuwa da Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Kebbi
  • Kofin kofi mafi tsada a duniya ya shiga kasuwa a kan Naira miliyan 1.5m
  • Gwamnatin Yobe ta ƙaddamar da shirin amfani da ma’adanai