An Kaddamar Da Shirin Kawar Da Mace-Macen Mata Masu Juna Biyu a Kano
Published: 14th, February 2025 GMT
Gwamnatin jihar Kano, KNSG, ta ce ta tanadi hanyoyin dakile mace-macen mata masu juna biyu maimakon rage yawan mace-macen.
Kwamishinan lafiya na jihar Dr Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a wajen taron hadin gwiwa na Partners Coordination Forum (PCF) da aka gudanar a Kano.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar lafiya ta jihar Kano Ibrahim Abdullahi, ta bayyana cewa, Dakta Abubakar Labaran ya bayyana cewa gwamnati ta himmatu sosai wajen kawo sauyi a fannin kiwon lafiya a karkashin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf, da niyyar ganin ba macen da ta mutu a lokacin haihuwa.
Ya yi karin haske kan gyare-gyaren da aka yi a cibiyoyin kula da lafiya na sakandare da kuma bayar da kwangiloli na inganta cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko sama da 200 a wani bangare na dabarun karfafa kiwon lafiyar mata masu juna biyu.
Ya nuna damuwarsa kan alkaluman da ke nuna cewa sama da kashi 70% na mata a Kano sun fi son haihuwa a gida da taimakon masu haihuwa na gargajiya maimakon neman magani a asibitoci.
Ya danganta hakan da rashin kwarin gwiwa kan ayyukan kiwon lafiya.
“Mata da yawa sun yi imanin cewa haihuwa a dakunan aurensu ya fi zuwa asibiti lafiya saboda sun daina amincewa da samun kulawar da ta dace. Don haka ne muke gyara asibitocinmu tare da karfafa cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko. Manufarmu ita ce a samar da akalla cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko guda daya a kowace Unguwa ta Jihar Kano.”
An kammala taron tare da abokan hadin gwiwa da suka yi alkawarin bayar da goyon bayansu ga kokarin jihar Kano wajen cimma wannan gagarumin buri.
Khadijah Aliyu/Wababe
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Haihuwa Lafiya kiwon lafiya
এছাড়াও পড়ুন: