Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yabawa tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) bisa irin gudunmawar da ya bayar ga ci gaban Najeriya.

Shugaban kasar a bayyana hakan ne a lokacin kaddamar da tallafin, tarihin rayuwar Janar Babangida da gwagwarmayarsa yayin aiki, wanda aka gudanar a Abuja.

 

A yayin da yake jawabi a matsayin babban bako na musamman, Tinubu ya bayyana ga  irin jagoranci  Babangida  a yayin mulkinsa, wanda ya ce ya abin koyi ne ga kowa.

Ya kuma yaba da rawar da IBB ya taka wajen kafa sabbin bankuna na zamani, wanda ya kawo kyakkyawa sauyi a fannin hada-hadar kudi na Najeriya.

Tinubu ya kuma yabawa manufofin Babangida da salon shugabancinsa da suka yi tasiri a nasa salon siyasar, inda ya jaddada kokarin Babangida wajen inganta  dimokuradiyya da kawo sauyi a tattalin arziki.

 

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, wanda ya gabatar da jawabi mai ma’ana, ya yabawa Babangida bisa rubuta tarihin rayuwarsa da irin gudunmawar da ya bayar a tarihin Najeriya.

Obasanjo ya jaddada mahimmancin adana bayanan tarihi don taimakawa al’umma masu zuwa, domin gano kura-kurai da suka gabata, da yadda za a gyara, da kuma taimako wajen gina kasa.

A wani muhimmin jawabi, tsohon shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo, ya yaba da shugabancin Babangida a Najeriya, inda ya jinjina  gudunmawar da ya bayar wajen tabbatar da dimokuradiyya a yammacin Afirka.

Kazalika shi ma tsohon shugaban kasa Yakubu Gowon ya tuna irin jajircewa da Babangida ya nuna a lokacin da yake aikin soja.

Ya lura da biyayyar Babangida da kokarin daidaita gwamnatin Najeriya a lokacin yunkurin juyin mulki da sauran kalubalen siyasa.

A nasa jawabin, tsohon mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya yi nazari mai zurfi game da littafin, inda ya yaba da abin da ya kunsa, da kuma yadda Babangida ya karrama wadanda suka yi aiki tare da shi.

A nasa jawabin, Babangida ya bayyana godiya ga dukkan wadanda suka halarci taron da suka hada da gwamnoni, da sanatoci, da sarakunan gargajiya, da wakilan kamfanoni masu zaman kansu.

Ya yi waiwaye kan kalubale da sadaukarwar da aka yi a lokacin gwamnatinsa, ya kuma bayyana irin matsalolin da al’ummar Najeriya ke fuskanta.

Babangida ya fito karara ya yi magana kan soke zaben shugaban kasa da aka yi a ranar 12 ga watan Yunin 1993, inda ya dauki cikakken alhakin wannan mataki.

Ya bayyana cewa an dauki dukkan matakan ne da domin gujewa tashin hankali, da kuma tabbatar da zaman lafiyar Najeriya.

Duk da cece-kucen da ake yi, Babangida ya jaddada cewa tsarin dimokuradiyya ya ci gaba da wanzuwa, wanda ya sa Najeriya ta samu ci gaba a dimokuradiyya.

An kammala taron ne da kaddamar da dakin karatu na Ibrahim Badamasi Babangida na fadar shugaban kasa, inda baki da dama suka bayar da gudunmawa domin tallafawa aikin.

Daga Bello Wakili

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Babangida ya

এছাড়াও পড়ুন:

Shugaba Xi Ya Aike Da Sako Ga Taron Wanzar Da Zaman Lafiya Na Matasan Kasa Da Kasa

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu ya tsawaita wa’adin aikin shugaban hukumar Kwastam
  • Tinubu ya tsawaita wa’adin shugaban hukumar Kwastam
  • An Yaba Da Kwazon Shugaba Bola Ahmad Tinubu
  • NAJERIYA A YAU: Tinubu ya yi wa Arewa adalci a ayyuka da mukamai — Bayo Onanuga
  • Kwamandan NDA Ya Bukaci Dalibai Su Dage da Karatu a Taron FGC Malali
  • Majalisa ta ba NNPCL mako uku ya yi mata bayanin inda tirilyan 210 ta shiga
  • Shugaban SUBEB Yayi Alkawarin Bayar Da Tallafin Ilimi A Jihar Nasarawa
  • Gwamnatin Tinubu ta mayar da Arewa saniyar ware – ACF
  • Shugaba Xi Ya Aike Da Sako Ga Taron Wanzar Da Zaman Lafiya Na Matasan Kasa Da Kasa
  • Ambaliyar Ruwa: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Ya Ƙaru Zuwa 23 A Jihar Adamawa