Ukraine ta amince da ƙudurin tsagaita wuta a fafatawarta da Rasha
Published: 12th, March 2025 GMT
Ukraine ta amince da ƙudurin tsagaita wuta na wata guda a yaƙin da ta shafe shekaru uku tana fafatawa da kasar Rasha.
Matakin na zuwa ne bayan tattaunawar da wakilan ƙasar ke ci gaba da yi yanzu haka da Amurka a birnin Jedda na Saudiya.
Matashin da ke ƙera jiragen sama da bindigogi daga robobi Rikicin ƙabilanci ya yi ajalin mai juna biyu da wasu mutum 10 a NasarawaSakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio ne ya sanar da haka da maraicen Talata bayan shafe wuni guda jami’an Ukraine da na Amurka suna tattaunawa don samar da zaman lafiya tsakanin Ukraine din da Rasha.
Rubio ya ce makasudin gabatar da kudurin shi ne na dakatar da bude wuta da kashe mata da kuma kananan yara a Ukraine.
Sakataren ya kuma kara da cewa a yanzu zabi ya rage ga Rasha na ta amince da kudurin ko kuma akasin hakan.
Sakataren ya kuma kara da cewa a yanzu zabi ya rage wa Rasha, inda kowanne lokaci daga yanzu ne ake shirin miƙa mata ƙunshin matsayar da aka cimma a wannan taro na Jedda don nazartarta da kuma yiwuwar aminta da ita ko akasin haka.
Wasu majiyoyi sun bayyana yiwuwar Donald Trump ya tattauna da Vladimir Putin a cikin makon nan bayan matakin na Ukraine dangane da amincewa da tayin Washington kan tsagaita wuta a yaƙin ɓangarorin biyu.
Har ila yau, Amurkar ta kuma amince ta koma bai wa Ukraine din bayanan sirri da kuma tallafin tsaro.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Rasha Saudiyya Ukraine
এছাড়াও পড়ুন:
Mutum 6 sun rasu, 13 sun jikkata a hatsarin mota a Kogi
Aƙalla mutum shida ne suka rasu, yayin da wasu 13 suka jikkata, bayan wata bas ɗauke da nakasassu ta yi hatsari a kan hanyar Lokoja zuwa Okene.
Waɗanda abin ya shafa suna komawa Okene ne bayan halartar bikin Ranar Nakasassu ta Duniya ta 2025 a Gidan Gwamnatin Jihar da ke Lokoja.
Jirgin fadar shugaban ƙasa ya ƙi sayuwa wata 5 bayan saka shi a kasuwa ’Yan sanda sun kama mutum 28 kan zargin lalata mata da yara a YobeAn garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibitoci daban-daban a jihar, inda suke ci gaba da samun kulawa.
Kwamishinan Harkokin Sadarwa na Jihar Kogi, Kingsley Femi Fanwo, ya ce wannan hatsari abun baƙin ciki ne ga gwamnati da jama’a.
Ya ce Gwamna Ahmed Usman Ododo ya umarci gwamnatin jihar da ta biya dukkanin kuɗin maganin waɗanda suka jikkata kuma ta tura jami’ai zuwa asibitoci don tallafa wa waɗanda abin ya shafa da iyalansu.
Fanwo ya ce: “Gwamnatin Jihar Kogi tana jimami sosai tare da iyalan waɗanda suka rasu guda shida, kuma za ta tallafa musu.”