Hauhawar farashi ya koma kashi 24 a Nijeriya — NBS
Published: 18th, February 2025 GMT
Hukumar Ƙididdiga ta Nijeriya NBS ta ce alƙaluman hauhawar farashi sun koma kashi 24.48 daga 34.8 cikin 100 a watan Janairun da ya gabata.
Wannan ne karon farko da hukumar ta NBS ta fitar da rahoton bisa sabon tsarin tattara alƙaluma da ta fara amfani da shi, abin da ke nufin da wuya a iya gane haƙiƙanin raguwa ko hauhawa a yanzu.
Alƙaluman sun nuna cewa hauhawar farashin kayan abinci ta kai 26.08 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.
Da yake yi wa manema labarai jawabi shugaban hukumar, Prince Adeyemi Adeniran, ya faɗa ranar Talata cewa sun sauya tsarin ne saboda “daidaita shi da irin na sauran ƙasashen duniya.”
Ya ce karo na ƙarshe da Nijeriya ta sauya tsarin ƙididdigar shi ne a shekarar 2009, inda ake ƙididdige farashin kayan da aka fi amfani da su a wannan tsakanin.
Hakan na nufin yanzu za a riƙa kwatanta farashin kayayyakin da aka ƙididdige daga shekarar 2024, maimakon 2009 da aka riƙa amfani da ita a baya.
“A sabon tsarin, ba matso da alƙaluman kusa da halin da ake ciki kawai muka yi ba, mun kuma ƙaddamar da sabuwar hanyar tattara bayanai don inganta yadda muke adana su da kuma sahihancinsu,” in ji shi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Hauhawar Farashi
এছাড়াও পড়ুন:
Trump Ya Ayyana Nijeriya A Matsayin Ƙasar Da Rayuwar Kiristoci Ke Cikin Hatsari
“Amurka ba za ta tsaya kawai tana kallo ba yayin da irin waɗannan ta’addancin ke faruwa a Nijeriya da sauran ƙasashe.
“Mun shirya, muna da ƙarfi da niyyar kare Kiristoci a faɗin duniya,” in ji Trump.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA