Allah Zai Kunyata Masu Ɗaukar Nauyin ’Yan Ta’adda – Gwaman Zamfara
Published: 14th, August 2025 GMT
A yayin ziyarar, Gwamna Lawal ya jajantawa iyalan waɗanda suka rasa ‘yan uwansu tare da tabbatar wa al’ummar yankin ƙudurinsa na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi.
A nasa jawabin, gwamnan ya yi kakkausar suka ga hare-haren da ’yan bindiga ke kai wa a baya-bayan nan, yana mai cewa da gangan maƙiya ke nufin waɗannan munanan ayyuka don yaɗa tsoro a tsakanin al’umma.
“Na ziyarci garin Banga ne domin jajanta wa jama’a game da harin da ‘yan bindiga suka kai a kwanakin baya.
“Lokacin da abin takaicin ya faru, na kasance ba na kusa, amma daga samun labarin, na umarci mataimakin gwamna da ya jagoranci wata babbar tawaga domin ziyarar jaje.
“A jiya ne na dawo Gusau bayan tafiya, kuma na ga ya dace na fifita ziyarar al’ummar da abin ya shafa a yau.
“Ina so in jaddada kudirin gwamnatina na ƙara ƙoƙari wajen yaƙi da ’yan bindiga.”
“Allah ya tona asirin waɗanda suke da hannu wajen kai waɗannan munanan hare-hare da kashe-kashen rashin hankali, ya kuma kunyata su. Ina kira ga kowa da kowa da ya dage da addu’a domin kawo ƙarshen duk wani nau’in ta’addanci a jiharmu mai albarka.”
Mai Martaba Sarkin Kauran Namoda, Dakta Sunusi Ahmad, a madadin jama’a, ya yaba wa ƙoƙarin Gwamna Lawal na ɗaukar matakan gaggawa kan matsalolin da suka shafi tsaro.
“Waɗannan ziyarce-ziyarcen abin yabo ne ga al’ummar da abin ya shafa da kuma ƙaramar hukumar Kauran Namoda, kuma muna godiya, Allah ya ci gaba da yi maka jagora.”
Gwamnan ya kuma yi alƙawarin inganta ababen more rayuwa kamar hanyoyin sadarwa, wutar lantarki, ruwan sha, da ayyukan wayar salula a cikin al’ummomin da abin ya shafa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Allah Ya yi wa Sheikh Dahiru Bauchi rasuwa
Fitaccen malamin addinin Musulunci nan daga Jihar Bauchi, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya rasu.
Ɗansa, Sayyadi Ali Dahiru Usman Bauchi ne, ya tabbatar wa Aminiya rasuwar malamin.
Juyin mulki ya rutsa da Jonathan a Guinea-Bissau Ɗan bindiga ya harbe sojoji 2 a fadar shugaban AmurkaYa ce sun karɓi wannan ƙaddara tare da gode wa Allah bisa rayuwar da malamin ya yi.
“Tabbas Sheikh ya koma ga Mahaliccinsa. Daga Allah muke, kuma gare Shi za mu koma,” in ji Sayyadi.
“Lokacin Sheikh ya yi. Mun gode wa Allah Maɗaukaki. Ya bai wa Sheikh tsawon rai, kuma rayuwarsa ta yi kyau. Alhamdulillah,” in ji shi.
Sayyadi, ya ce zuwa yanzu ba su yanke inda za a yi jana’izar malamin ba.