Dalilan ƙaruwar mace-mace a hanyoyin Najeriya
Published: 14th, August 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Duk da kara wayar da kan direbobi da fasinjoji da Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) ta ce tana yi, ana kara samun ƙaruwar wadanda ke rasa rayukansu sakamakon hadura a titunan kasar nan.
A shafinta na internet, FRSC ta ce a watanni uku na farkon 2024, mutane 1,471 ne suka rasa rayukansu sakamakon hatsarin mota.
Kazalika, a watanni uku na farko na wannan shekara ta 2025, adadin ya haura zuwa mutane 1,593 — karin mutum 122, ko kuma kashi 8.3 cikin dari.
NAJERIYA A YAU: Yadda matasa ke bayar da gudunmawa ga ci-gaban al’umma DAGA LARABA: Yadda sinadaran dandanon abinci ke yin illa ga lafiyaShirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa ake kara samun karuwar rasa rayuka a titunan kasar nan.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: hatsarin mota hukumar kiyaye haddura Rasa Rayuka
এছাড়াও পড়ুন:
Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 236 A Jihohi 27 Da Birnin Tarayya
A cewar NEMA, mutane 135,764 ne suka rasa matsugunansu, yayin da 115 aka bayyana bacewarsu, yayin da wasu 826 suka samu raunuka sakamakon ambaliyar. Bugu da kari, gidaje 47,708 sun lalace, yayin da gonaki 62,653 suka lalace a fadin jihohin da abin ya shafa.
Hukumar ta kara da cewa, daga cikin wadanda abin ya shafa sun hada da yara 188,118, mata 125,307, maza 77,423, tsofaffi 18,866, da kuma nakasassu 2,418.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA