Zelensky ya je Saudiyya domin tattaunawar zaman lafiya
Published: 11th, March 2025 GMT
Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya isa kasar Saudiyya domin ganawa da yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman, gabanin wata muhimmiyar ganawa tsakanin tawagogin Ukraine da na Amurka domin share fagen shawarwarin zaman lafiya da Rasha a nan gaba.
Taron dai na nuni da wani gagarumin yunkurin diflomasiyya na magance rikicin da ke faruwa a Ukraine kuma zai iya ba da damar tsagaita bude wuta a cewar rahotanni.
Tattaunawar da za a yi a Jeddah ita ce ganawa ta farko tsakanin jami’an Ukraine da Amurka tun bayan ziyarar da Zelensky ya kai fadar White House a karshen watan Fabrairu da ya gabata, wanda ya haifar da cacar baki baki mai zafi tsakaninsa da shugaban Amurka Donald Trump.
Tun bayan hakan ne, gwamnatin Washington ta dakatar da taimakon soji ga Ukraine, lamarin da ya sa Kyiv ta nemi sulhu.
Zelenskyy ya bayyana cewa, “Muna fatan tattaunawa tare da amincewa kan shawarwari da ayyukan da suka dace,” yana mai jaddada cewa Ukraine na goyon bayan tattaunawa mai ma’ana tare da son a yi la’akari da muradunta.
Taron na ranar Talata zai mayar da hankali ne kan kafa tsarin zaman lafiya da tsagaita bude wuta tsakanin Rasha da Ukraine.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kungiyar Hamas Ta Ce Ta Amince Da Tattaunawa Don Kawo Karshen Yaki A Gaza
Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza na kasar Falasdinu da aka mamaye, ta bada sanarwan cewa da ita da sauran kungiyoyi da suke gwagwarmaya da HKI kimani shekaru biyu da suka gabata, sun amince da batun tattaunawa da kuma tsagaiuta budewa juna wuta wanda masu shiga tsakani suka gabatar.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa, shugaban kasar Amurka Donal Trump ya ce, wai HKI ta amince da shawarar budewa juna wuta da ya gabatar, amma kuma har yanzun ba’a bayyana dalla-dalla menen a cikin yarjeniyar ta kunsa ba. Har’ila yau gwamnatin kasar Masar ta ce tana kokarin ganin an samar da tsagaita budewa juna wuta na kwanaki 60.