Larijani a Beirut: Iran A Shirye take ta taimaka ma Lebanon
Published: 14th, August 2025 GMT
Shugaban majalisar dokokin kasar Lebanon Nabih Berri ya tarbi Ali Larijani, sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran a hedikwatar shugaban kasa ta biyu dake Ain al-Tineh. Larijani ya tabbatar da cewa bayan ganawar da aka yi tsakanin kasashen Labanon da Iran lamarin ya yi kyau da armashi.
Ya jaddada cewa Iran ba ta da niyyar yin katsalandan a cikin harkokin cikin gidan kasar Labanon, yana mai cewa bai kamata wasu kasashe su ba da umarni ga gwamnatin Lebanonba, musamman kan wasu batutuwa masu sarkakiya wadanda al’ummar Lebanon ne tare da gwamnatinsu kawai za su iya yanke shawarar a kansu.
Larijani ya jaddada cewa Iran ba ta zo da wani shiri a Labanon ba, sai dai Amurkawa sun zo ne da takardarsu da ke neman jefa Kasara cikin yamutsi.
Larijani ya jaddada cewa Iran na mutunta duk wani matakin da gwamnati za ta dauka tare da hadin gwiwa da sauran bangarori daban-daban na kasar Lebanon.
Kafin nan Larijani ya gana da shugaba Joseph Aoun a babbar fadar shugaban kasa da ke Baabda.
A wata sanarwa da fadar shugaban kasar Labanon ta fitar bayan ganawar ta bayyana cewa, Larijani ya sake sabunta gaisuwar shugaban kasar Iran ga shugaba Aoun tare da gayyatarsa zuwa birnin Tehran, inda ya kara da cewa “Larijani ya tabbatar da cewa Iran a shirye take ta taimaka wa kasar Lebanon idan har gwamnatin Lebanon tana bukatar hakan so”, inda Aoun ya sanar da Larijani cewa “sha’awar kasar Lebanon na yin hadin gwiwa da kasar Iran a kan dangantakar da ke tsakaninta da Iran abu ne tabbatace.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Masar ta yi Allawadai da ikirarin Netanyahu game shirinsa na kafa Isra’ila Babba August 14, 2025 Hamas ta aike da wasikar yabo ga Yemen kan goyon bayan Gaza August 14, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 130 August 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 129 August 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 128 August 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Imam Hassan (a) 127 August 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 126 August 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 125 August 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 124 August 13, 2025 Iran: Babu Mika Kai Ga Takurawar kasashen Yamma har sai An Kawo Karshen Barazana August 13, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Lebanon da cewa Iran Larijani ya
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Bukaci HKI Ta Aiwatar Da Yarjeniya Da Gaza Kamar Yadda Take
Masu zanga-zanga a nan Iran a jiya jumma’a a manya-manyan garuruwan kasar bayan sallar Jumma’a sun bayyana goyon bayansu ga al-ummar Falasdinu a Gaza, sannan sun bukaci HKI ta aiwatar da yarjeniyar da ta cimma da kungiyoyi masu gwagwarmaya. Har’ila yau sun bukaci a gaggauta shigo da abinci da magungunacikin zirin Gaza.
Tashar talabijin talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto masu zanga zangar wadanda suka hada da mata da maza, malaman addini, daliban jami’o’i da sauransu suna tattaki daga dandalin inkilab zuwa dandalin azadi.
Har’ila yau sun rera wakoki na goyon bayan masu gwagwarmayar, dauke da hotunan shahidai da kuma shuwagabannin kawancen masu gwagwarmaya a yankin.
An gudanar da jerin gwanon a cikin manya manyan biranen kasar wadanda suka hada da Tabriz, Ahvaz, Shiraz, Bandar Abbas, Isfahan, da Gorgan.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka HKI Ta Kashe Mutane 19 A Gaza Duk Tare Da Tsagaita Wuta October 11, 2025 Iran Tana Goyon Bayan Duk Wani Shirin Zaman Lafiya Da Ya Hada Da Kawo Karshen Kisan Kiyashi A Gaza October 11, 2025 Faransa Da Jamus Da Kuma Birtaniya Sun Bayyana Aniyarsu Ta Ganin An Farfado Da Tattauna Da Iran October 11, 2025 Kungiyoyin Falasdinawa Sun Fitar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Kan Tsagaita Bude Wuta A Gaza October 11, 2025 Venezuala Ta Bukaci Kwamitin Sulhun M.D.D Da Ya Tabbatar Da Cewa: Amurka Tana Barazana Ga Zaman Lafiya October 11, 2025 Pakistan Ta Kai Hari Kan Kasar Afganistan, Inda Ake Rade-Radin Kashe Shugaban Taliban Na Kasarta October 11, 2025 Putin: Natanyahu Yana Son Warware Matsaloli Da Iran Cikin Lumana Ba Tare Da Yaki Ba October 10, 2025 Majalisar Turai Ta Bukaci Kasashen Nahiyar Su Kakkabo Jiragen Yakin Rasha October 10, 2025 Sa’o’ii Da Fara Janyewar Sojojin HKI A Gaza An Fara Gano Gawakin Falasdinwa October 10, 2025 Falasdinawa Daga Kudancin Gaza Sun Fara Komawa Gidajensu Da Aka Rusa A Arewacin Yankin October 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci