Jaridar Telegraph Ta Ce; Shugabannin Sojojin Iran Sun Bukaci Jagora Da Ya Soke Fatawar Haramci Kera Makamin Nukiliya
Published: 12th, February 2025 GMT
Jaridar Daily Telegraph ta watsa labarin cewa: Shugabannin Iran sun bukaci Jagoran juyin juya halin Musulunci Sayyid Khamenei da ya janye fatawarsa kan haramcin mallakar makamin nukiliya
Jaridar Daily Telegraph ta kasar Birtaniya ta watsa rahoton cewa: Shugabannin sojojin Iran sun bukaci Jagoran juyin juya halin Musulunci Sayyid Ali Khamenei ya yi watsi da haramcin mallakar makaman nukiliya da ya fitar da fatawa kanta a farkon takaddamar Shirin makamashin nukiliyar Iran na zaman lafiya.
Jaridar ta ruwaito a cikin wani rahoton da wakilinta na musamman Akhtar Muhammad Makoy ya fitar cewa: Manyan jagororin sojojin Iran sun ce dole ne Jagoran juyin juya halin Musulunci ya soke fatawar da ta haramta kera makaman nukiliya matukar gwamnatin Iran na son ci gaba da rayuwa da kare cikakken ‘yancinta na rayuwa.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Pezeshkiya: Iran A Shirye Take Don Mu’amala Amma Bazata Bar Hakkinta Ba
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa Iran a shirye take ta fadada hulda da kasashen turai, amma kuma wannan ba zai sa ta saryar da hakkinta na sarrafa makamashin nukliya karshen dokokin kasa da kasa wadanda suka amince mata ta yi haka ba.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a yau Litinin a lokacinda yake ganaw da sabon jakadan kasar Faransa a Tehran pierre Cochard wanda ya mika masa tarkardun fara aikinbsa.
Shugaban ya kara da cewa an takurawa kasar Iran dangane da shirinta na makamashin nukliya a bayan. Amma daga yanzun kuma ba zata amince da irin takurawa ta bay aba.
Ya kuma bayyana cewa tattaunawa tsakanin Iran da kasashe uku na turai wato Faransa da Jamus da kuma Burtaniya, saboda samun fahintar juna da kuma daukewa kasar takunkuman tattalin arzikinn da turawan suka dora mata.