HausaTv:
2025-07-12@10:20:09 GMT

Saudiyya Za Ta Karbi Bakuncin Tattaunawar Amurka Da Ukiraniya

Published: 7th, March 2025 GMT

Shugaba Zelensky   na Ukiraniya zai kai ziyara kasar Saudiyya a ranar Litinin, gabanin bude tattaunawar da za a yi tsakanin kasarsa da kuma Amurka da zummar kawo karshen yaki da Rasha.

Shugaban na kasar Ukiraniya ya wallafa wani sako a shafinsa na X cewa; Manufar ziyarar tashi ita ce haduwa da yarima mai jiran gado Muhammad Bin Salman, sannan kuma tawagar da zai je da ita, za ta ci gaba da zama a can Saudiyya din saboda yin aiki tare da mutanen Saudiyya da kuma Amurka.

Zelensky ya kara da cewa; Kasarsa Ukiraniya tana son ganin an sami zaman lafiya mai dorewa.

Bugu da kari shugaban na kasar Ukiraniya ya ce; Matakin farko da kasarsa ta gabatar a matsayin shawarar kai wa ga zaman lafiya, shi ne dakatar da yaki a lokaci mafi kusa, da hakan zai zama share fage ne na warware sabanin da ake da shi baki daya,kuma Ukiraniya a shirye take ta yi aiki da Amurka a turai domin shimfida zaman lafiya”

Dangane da taron da za a yi a kasar Saudiyya, wani babban jami’in gwamnatin kasar ta Ukiraniya ya ce, a ranar Talata mai zuwa za a yi ganawa a tsakanin tawagar kasarsa da kuma ta Amurka a Saudiyya.

Jami’in na Ukiraniya ya ce ganawar za a yi ta ne a kokarin kyautata alaka a tsakanin kasashen biyu, bayan abinda ya faru na cacar baki a tsakanin Donald Trump a Zylenisky.

A gefe daya ministan tsaron Birtaniy John Healey ya furta cewa; Da akwai kyakkyawar dama ta tarihi domin shimfida zaman lafiya a Ukiraniya” sannan ya kara da cewa: “ Shugaban kasar Ukiraniya a shirye yake ya rattaba hannu akan yarjejeniya da Amurka, amma yana da bukatuwa da a ba shi lamuni.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: Ukiraniya ya zaman lafiya a Ukiraniya

এছাড়াও পড়ুন:

Bafarawa Ya Kaddamar Da Wata Kungiya Mai Suna “Arewa Cohesion Initiative” Don Maganin Kalubalen Da Yankin Arewa Ke Fuskanta

 

Ganin irin yawan kalubalen tattalin arziki da siyasa a Arewacin kasan nan ya sanya Tsohon Gwamnan Jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya kaddamar da wata sabuwar kungiya mai taken Arewa Cohesion for Peace, Unity and Development Initiative.

 

An kaddamar da wannan kungiyoyi ce a wajen wani babban taro da aka gudanar a Arewa House, Kaduna, inda manyan baki da mahalarta daga sassa daban-daban na Arewa suka halarta.

 

A yayin taron, Bafarawa wanda shi ne Shugaban Kwamitin Amintattu na tafiyar, ya bayyana wannan mataki a matsayin sabon hanyar da za ta yi maganin baraka da inganta fahimtar juna da kuma karfafa ci gaban mai dorewa a yankin Arewa.

 

Ya ce Arewacin Najeriya na fuskantar kalubale da dama da suka hada da rikice-rikicen al’umma, rashin tsaro, zaman kashe wando a tsakanin matasa da wariyar tattalin arziki da kuma lalacewar dabi’u da da suka hade mutanen yankin a da.

 

Tsohon Gwamnan jihar Sokoton, yace manufar tafiyar ita ce samar da zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin al’ummomi daban-daban a Arewa, tare da samar da hanyoyi na tattaunawa da sulhu da kuma warware rikice-rikice.

 

Bafarawa ya jaddada cewa tafiyar za ta maida hankali kan matasa, da aiki tare da gwamnatoci da Sarakuna da Malaman addini da kungiyoyin masu zaman kansu da abokan hulɗa na kasa da kasa, don gina Arewa mai aminci da karfi da kuma adalci ga kowa.

 

Ya bayyana cewa tafiyar ba ta da nasaba da siyasa, kuma babu niyyar mayar da ita jam’iyyar siyasa ko goyon bayan kowace jam’iyya. Ya ce burinsu ya wuce siyasa, domin suna son aiki da kowa muddin yana da burin ciyar da Arewa da Najeriya gaba. Ya kara da cewa su na bude wajen aiki da kowace kungiya da ke da manufofi irin nasu.

 

Duk da kasancewar tafiyar ba ta siyasa ba ce, Bafarawa ya bayyana cewa ’yan tafiyar na da ’yancin shiga harkokin siyasa a matsayin kansu ba tare da nasaba da tafiyar ba.

 

Bafarawa ya kuma sanar da cewa an kammala tsara wata cikakkiyar tsarin taswira (blueprint) da ke kunshe da hanyoyin farfado da Arewacin Najeriya, wadda aka samo daga bincike da nazari mai zurfi kan damar yankin.

 

A nasa jawabin, Darakta Janar na tafiyar, Dr. Abdullahi Idris, ya bayyana cewa an kirkiro tafiyar ne sakamakon tabbacin cewa kalubalen da ke fuskantar yankin ba za su warware sai da hadin gwiwa da fahimtar juna da tsare-tsaren ci gaba da zaman lafiya.

 

Dr. Idris ya bayyana tafiyar Arewa Cohesion Initiative a matsayin mafita mai muhimmanci da dacewa da lokaci, wacce ta ta’allaka ne a kan ginshikai uku: gina zaman lafiya, dunkulewar Arewa da ci gaban da za a iya jurewa.

 

Ya shawarci masu ruwa da tsaki su kasance masu hangen nesa wajen magance matsalolin yankin, yana mai jaddada cewa wadannan matsaloli ba a haifar da su cikin dare daya ba, kuma ba za su warware cikin dare daya ba. Sai dai da hakuri, hadin kai da jajircewa, ana iya samun sauyi mai ma’ana.

 

Shugaban taron kuma Janar mai murabus, Jon Temlong, ya jinjinawa Bafarawa bisa jajircewarsa wajen ci gaban kasa bayan barin siyasa. Ya ce wannan tafiya tana dauke da dabi’u na gaskiya da ke bayyana Arewacin Najeriya — zumunci, adalci da hadin kai.

 

Janar Temlong ya ce shugabancin tafiyar yana dauke da fatan al’umma da dama, yana mai bayyana cewa wannan kaddamarwa na iya zama sauyi mai muhimmanci a kokarin Arewacin Najeriya na neman zaman lafiya da ci gaba mai dorewa.

 

Taron ya samu halartar jama’a da dama daga sassa daban-daban na Arewacin Najeriya, alamar goyon baya da hadin kai ga wannan tafiya.

COV: Adamu Yusuf

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • HKI Ta Roki Amurka Ta Taimake Ta A Fada Da Kasar Yemen
  • Najeriya Ba Za Ta Karbi ‘Yan Ci Ranin Kasar Venezuela Da Amurka Za Ta Kora Ba
  • An Koka Kan Yadda Tsafi Da Jariran Da Aka Haifa Da Tsagaggen Lebe Ke Karuwa
  • Bafarawa Ya Kaddamar Da Kungiyar Hada Kan Arewa Da Samar Da Zaman lafiya A Kaduna 
  • Bafarawa Ya Kaddamar Da Wata Kungiya Mai Suna “Arewa Cohesion Initiative” Don Maganin Kalubalen Da Yankin Arewa Ke Fuskanta
  • Manazaecin Kasar Amurka Ya Ce; Isra’ila Ta Sha Kashi A  Yakinta Da Jamhuriyar Musulunci Ta Iran
  • Zagaye na 5 A Tattaunawar Gaza da HKI  Ya tashi ba tare da Sun Dai-daita ba A Doha
  • Aragchi Ya Tattauna Da Bin Salman Kan Karfafa Zumunci Tsakanin Kasashen Biyu
  • Trump Ya Kakabawa Wata Jami’in MDD Takunkumi Bayan Ta Fallasa Laifukan HKI Da Hannun Amurka A Ciki
  • An Yi Hasashen Karuwar Tattalin Arzikin Kasar Sin Za Ta Zarce Yuan Tiriliyan 35 Tsakanin 2021 Zuwa 2025