Alawar yara mai sanya maye ta shiga gari —NDLEA
Published: 3rd, February 2025 GMT
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) a Jihar Kano ta gargaɗi al’umma kan wata alawar yara mai da sanya maye, da ke yawo a gari.
Hukumar ta gargaɗi, musamman iyaye da su yi hattara da alawar da sauran kayan tanɗe-tanɗe da ke ɗauke da sinadarai masu sanya maye.
Kakakin Hukumar a jihar, ASN Sadiq Muhammad Maigatari, ya kuma yi kira ga iyaye da suka riƙa lura da irin kayan tanɗe-tanɗe da ’ya’yansu ke saya.
Ya bayyana cewa alawar tana kama da cakulet, amma a cikinta an sanya abin da ke bugarwa, kuma yawanci an fi sayarwa a makarantu.
NHIS: Kotu ta tsare Farfesa Usman Yusuf a Gidan Yarin Kuje Gwamnatin Najeriya za ta sake ƙara kuɗin lantarki NAJERIYA A YAU: Dalilin Da Za Mu Kashe Biliyan N2.5 Kan Auren Zawarawa —Gwamnatin KanoDon haka ya buƙaci iyaye da su riƙa sanya ido, musamman idan suka ga wani sauyi a yanayin ’ya’yan nasu.
Ya ce, “sauyin ya haɗa da na yanayin cin abinci da na barcin yara.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: alawa alawa mai sanya maye
এছাড়াও পড়ুন:
An Tsare Wani Mutum A Gidan Yari Kan Zargin Kashe Matarsa Saboda Ƙuli-Ƙuli A Kano
Mai shari’a Dahiru ya amince da buƙatar, ya kuma ɗage shari’ar zuwa ranar 12 ga watan Disamba, 2025, domin ci gaba da sauraron shari’ar.
Ƙuli-ƙuli dai nau’in abin ci ne mai taushi da ake yi da gyaɗa, ana soyawa har sai ya zama ƙura-ƙura ta yadda za a ci cikin nishaɗi.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA