Aminiya:
2025-11-27@22:19:05 GMT

’Yan ci-rani 26 sun nitse a teku suna ƙoƙarin tsallakawa Turai

Published: 14th, August 2025 GMT

Akalla ’yan ci-rani 26 sun mutu bayan jiragen ruwan da suke ciki guda biyu sun nitse a teku a kusa da tsibirin Lampedusa na ƙasar Italiya.

Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana hasashen ƙarin wasu mutanen kuma sun ɓace yayin da ake ci gaba da aikin ceto su.

Allah zai kunyata masu ɗaukar nauyin ta’addanci a Zamfara — Gwamna Dauda Dalilan ƙaruwar mace-mace a hanyoyin Najeriya

Galibi dai ’yan ci-ranin da suka fito daga ƙasashen Afirka na ƙoƙarin tsallakawa nahiyar Turai ne domin samun ingantacciyar rayuwa.

Ko a ranar Laraba dai ma’aikatan ceto sun ce sun ceto mutum 60 da ransu, wadanda suka hada da maza 56 da kuma mata hudu, sannan aka kai su tsibirin na Lampedusa, kungiyar bayar da agaji ta Red Cross a kasar ta Italiya ta tabbatar.

Kakakin Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (IOM), Flavio Di Giacomo, ya ce akwai mutum 95 a cikin jiragen guda biyu da suka nitse.

Ya wallafa a shafukan sada zumunta cewa, “kasancewar an ceto mutum 60 da rai, ana fargabar akwai mutum 35 da suka mutu ko kuma suka ɓace.“

Hatsarin wanda ya ritsa da ’yan ci-ranin da suka taso daga ƙasar Libya shi ne na baya-bayan nan ga mutanen da ke kokarin tsallaka teku domin shiga nahiyar Turai.

Alkaluma sun nuna daga farkon shekarar nan zuwa yanzu, akalla mutum 675 ne suka rasa ransu ta irin wannan hanyar a kan iyakokin kasashen biyu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Ci rani Hatsarin Jirgin Ruwa Italiya

এছাড়াও পড়ুন:

Real Madrid za ta yi karon-batta da Olympiacos a Gasar Zakarun Turai

A yammacin nan ne ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid za ta kece raini da Olympiacos a ci gaba da Gasar Zakarun Turai, duk da rashin wasu manyan ’yan wasanta biyu.

Babban mai tsaron ragar Madrid, Thibaut Courtois, da ɗan wasan baya Dean Huijsen, na fama da jinya, lamarin da zai hana su buga wannan muhimmin wasa.

Sojoji sun yi juyin mulki a Guinea-Bissau Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa sunayen jakadu

Yanzu haka jerin ’yan wasan Madrid da ke jinya sun haɗa da: Thibaut Courtois, Dean Huijsen, Antonio Rüdiger, David Alaba, Franco Mastantuono, da Éder Militão.

Tun bayan zuwan sabon kocin Real Madrid, Xabi Alonso, Courtois ya riƙe ragamar tsaron raga a dukkan wasanni 17 da suka buga a kakar nan.

Andriy Lunin, ɗan asalin ƙasar Ukraine mai shekaru 26, shi ne mai tsaron da ya fi samun damar buga wasanni a zamanin tsohon koci Carlo Ancelotti, lokacin da Courtois ya yi jinya mai tsawo.

Gasar Zakarun Turai dai fage ne da Real Madrid ta yi fice a duniya wadda ta lashe sau 15 a tarihi.

A bana, ƙungiyar tana da maki 9 daga wasanni 4 da ta buga zuwa yanzu da ake kece raini a matakin rukuni

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ɗan bindiga ya harbe sojoji 2 a fadar shugaban Amurka
  • Real Madrid za ta yi karon-batta da Olympiacos a Gasar Zakarun Turai
  • Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa sunayen jakadu
  • ’Yan sanda sun kama masu laifi 34 a Kaduna
  • ’Yan sanda sun kama masu laifi da 34 a Kaduna
  • Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Oyo saboda aikata kisan kai
  • ’Yan bindiga sun sake kai hari a Kwara, sun sace mutum 11
  • An ceto ’yan mata 24 d aka yi garkuwa da su a makaranta a Kebbi
  • Tinubu Ya Nuna Farin Cikinsa Bisa Bayyanar Daliban Kebbi, Ya Bukaci a Ceto Sauran
  • ’Yan bindiga sun sace mutum 8 a Kano