Gwamnatin Sakkwato ta buƙaci a yi adalci a binciken da ake yi kan silar rasuwar ɗan ƙwallon ƙafan nan ɗan asalin jihar, Abubakar Lawal, wanda ya rasu a satin da ya gabata kasar Uganda inda yake taka leda.

Kwamishinan Matasa da Wasanni na jihar, Injiniya Almustafa Muhammad Kofar Marke ne ya sanar da hakan a lokacin da suke karbar gawar margayin a Nijeriya domin jana’izarsa a mahaifarsa sa ke jihar.

Injiniya Kofar Marke ya bayyana baƙin ciki da rashin Abubakar Lawal, wanda ya bayyana a matsayin ɗan kwallon ƙafa na musamman kuma jakada nagari a harkar wasanni.

“Labarin rasuwar nan abar girgiza da taba zuciya ce, domin marigayin ya bayar da gudunmuwa a harkaar ƙwallon ƙafa ta a-zo-a-gani a duniya ta hanyar ƙasashe daban-daban.

“Muna gode wa ofishin jekadancinmu da ya tabbatar da dawowar gawar margayin zuwa gida don yi mata janaza, haka ma makusantan abokansa suma sun yi kokari.”

Injiniya Mustafa ya ƙara tabbatar da goyon bayansu ga iyalan marigayin kamar yadda suka yi tsaye tun sa’adda lamarin ya faru har aka karbi gawar, bisa ga sahalewar gwamnan Sakkwato Ahmad Aliyu.

Dan kwallon Nijeriya Abdullahi Shehu ne ya rako gawar zuwa Nijeriya ya mika ta’aziyarsa ga iyalai da dangin margayin da mutanen Sakkwato da masoya kwallon kafa gaba daya.

“Abubakar Lawal ba kawai abokin hulɗa ba ne, aboki ne a gare ni, yana da karimci da sanin yakamata, ina rokon Allah Ya gafarta masa”.

Margayin ɗan kwallon Nijeriya ne da ya fara buga wasa a Sakkwato da Nasarawa kafin likafa ta ci gaba ya koma kasar Uganda, ya samu nasarori da dama a wasan ƙwallon kafa a lokacin rayuwarsa.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Abubakar Lawal Gawa Ƙwallon ƙafa Sakkwato

এছাড়াও পড়ুন:

Nazarin CGTN: Ana Kara Bayyana Rashin Gamsuwa Da Sabuwar Gwamnatin Amurka Daga Ciki Da Wajen Kasar

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Tarayya ta ayyana hutu gobe Alhamis
  • Binciken Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN: Cin Zali Ta Hanyar Kakaba Haraji Ya Illata Kimar Amurka
  • Gwamnan Sokoto Ya Amince Da Sauya Wa Manyan Sakatarori 25 Ma’aikatu A Jihar 
  • Dokta Bashir ya zama shugaban Majalisar Shari’ar Musulunci ta Nijeriya
  • Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Shirya Fara Tantance ‘Yan Fansho
  • Nazarin CGTN: Ana Kara Bayyana Rashin Gamsuwa Da Sabuwar Gwamnatin Amurka Daga Ciki Da Wajen Kasar
  • Gwamnati Ta Kafa Kwamitin Binciken Yawaitar Haɗurran Tankokin Man Fetur A Nijeriya 
  • Jihar Kebbi Ta Kammala Shirye-shiryen Aikin Hajjin 2025
  • Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci Ta Yaba Wa Gwamna Lawal Kan Matakan Yaƙi Da ‘Yan Bindiga A Zamfara
  • Uganda Ta Sanar Da Kawo Karshen Ebola Da Ta Barke A Kasar