Zulum Ya Yi Alƙawarin Gyara Sansanin NYSC Na Borno
Published: 8th, February 2025 GMT
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya sha alwashin gyara wa da faɗaɗa sansanin horas da matasan maus yi wa ƙsa hidima (NYSC) na dindindin a jihar.
Da yake karɓar babban Daraktan NYSC, Birgediya Janar Yusha’u Ahmed a Maiduguri, Zulum ya ce gwamnatinsa za ta gaggauta gina sansanin dindindin domin karɓar ƙarin ‘yan bautar ƙasa.
Shugaban NYSC ya gode wa gwamnatin Borno bisa tallafin da take bai wa ‘yan bautar ƙasa, ciki har da alawus na musamman, da abinci, da motocin aiki.
কীওয়ার্ড: Gwamna Zulum
এছাড়াও পড়ুন:
Tsaro: Taimakonmu Amurka ya kamata ta yi maimakon barazana — Kwankwaso
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana damuwarsa kan kalaman da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi game da Najeriya.
Kwankwaso, ya yi wannan magana ne bayan Trump ya yi barazanar ɗaukar matakin yaƙi game da zargin kisan kiyashi da ake yi wa Kiristoci.
Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka Kisan Kiristoci: Lauyoyi sun nemi Gwamnatin Tarayya ta tattauna da AmurkaA cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kwankwaso, ya ce Najeriya ƙasa ce mai cikakken ’yanci, wadda ke fama da matsalar tsaro daga miyagu a sassa daban-daban na ƙasar.
“Matsalar tsaron da muke fuskanta ba ta bambanta tsakanin addini, ƙabila ko ra’ayin siyasa,” in ji shi.
Ya buƙaci gwamnatin Amurka da ta tallafa wa Najeriya da sabbin fasahohi domin yaƙar matsalar tsaro maimakon yin kalaman da za su iya raba kan ’yan ƙasa.
“Amurka ya kamata ta taimaka wa hukumomin Najeriya da ingantattun fasahohi don magance matsalolin tsaro, maimakon yin barazanar da za ta ƙara raba ƙasar,” in ji Kwankwaso.
Haka kuma, ya shawarci Gwamnatin Najeriya da ta naɗa jakadu na musamman domin inganta hulɗar diflomasiyya da Amurka da kare muradun ƙasar a matakin duniya.
Ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su zauna lafiya, inda ya bayyana cewa wannan lokaci ne da ya dace a fifita haɗin kan ƙasa ba abin da ke raba ta ba.
“Wannan lokaci ne da ya kamata mu mayar da hankali kan abin da zai haɗa kanmu ba wanda zai raba mu ba. Allah Ya albarkaci Najeriya,” in ji shi.