Majalisar Zartaswa ta dakatar da ƙirƙirar sabbin manyan makarantu a Nijeriya
Published: 14th, August 2025 GMT
Gwamnatin Tarayya ta yanke shawarar dakatar da ƙirƙirar sabbin manyan makarantu har na tsawon shekaru bakwai masu zuwa a duk faɗin Nijeriya.
Dakatarwar ta shafi ƙirƙirar sabbin jami’o’i, kwalejojin ilimi da kuma kwalejojin kimiyya da fasaha na tarayya kamar yadda Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta tabbatar.
Wannan mataki, a cewar Ministan Ilimi Dakta Olatunji Alausa, an ɗauke shi ne domin rage yawan makarantun da ba a amfani da su yadda ya kamata, lamarin da zai ba da damar mayar da hankali wajen gyara da inganta waɗanda ake da su yanzu.
Da yake zantawa da manema labarai bayan taron na FEC a fadar shugaban ƙasa ranar Laraba, Alausa ya bayyana cewa binciken da aka gudanar ya nuna cewa samun damar shiga jami’a a Nijeriya “ba ita ce matsala ba” a halin yanzu.
Sai dai ministan ya ce yawan kafa makarantu marasa inganci da maimaita su ne ke jawo matsaloli irin su gine-ginen da ba su dace ba, ƙarancin ma’aikata, da raguwar ɗalibai.
Ya ce “akwai wasu jami’o’in gwamnatin tarayya da ke aiki ƙasa da yadda ya dace da su, inda wasu ke da ɗalibai da ba su haura 2,000 ba. A wata jami’a ma, ma’aikata 1,200 ne ke kula da ɗalibai ƙasa da 800.
“Wannan asarar kuɗin gwamnati ne, saboda a yanzu muna da jami’o’i 199, amma ƙasa da ɗalibai 100 ne suka nemi shiga kowace ta hanyar JAMB. Har ma akwai jami’o’i 34 da babu wanda ya nema gaba ɗaya,” in ji shi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Majalisar Zartarwa Majalisar Zartaswa ta Tarayya manyan makarantu
এছাড়াও পড়ুন:
Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 236 A Jihohi 27 Da Birnin Tarayya
A cewar NEMA, mutane 135,764 ne suka rasa matsugunansu, yayin da 115 aka bayyana bacewarsu, yayin da wasu 826 suka samu raunuka sakamakon ambaliyar. Bugu da kari, gidaje 47,708 sun lalace, yayin da gonaki 62,653 suka lalace a fadin jihohin da abin ya shafa.
Hukumar ta kara da cewa, daga cikin wadanda abin ya shafa sun hada da yara 188,118, mata 125,307, maza 77,423, tsofaffi 18,866, da kuma nakasassu 2,418.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA