MDD: Yaran Gaza 2,500 na fuskantar mutuwa matukar ba a yi gaggawar kwashe marasa lafiya ba
Published: 31st, January 2025 GMT
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira da a gaggauta kwashe yara 2,500 da suka jikkata a yakin da Isra’ila ta kwashe watanni 15 tana yi a Gaza domin samun kulawar gaggawa.
Rokon nasa ya biyo bayan ganawar da ya yi da likitocin Amurka ne wadanda suka yi gargadin cewa yaran na fuskantar barazanar mutuwa a makonni masu zuwa.
Likitocin hudu, wadanda suka yi aikin sa kai a Gaza sun bayyana mummunan halin da yanayin kiwon lafiyar yankin ke ciki, wanda yakin ya yi wa illa.
Guterres ya ce ya ji dadin matuka bayan tattaunawarsa da likitocin Amurka ranar Alhamis. Ya kuma”Dole ne a kwashe yara 2,500 ba tare da bata lokaci ba, tare da ba da tabbacin cewa za su iya komawa ga iyalansu bayan sun samu lafiya, kamar yadda ya rubuta a shafukan sada zumunta.
Kwanaki kadan kafin a fara tsagaita wuta a ranar 19 ga watan Janairu, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ba da rahoton cewa sama da Falasdinawa 12,000 ne ke jiran kulawar likitoci, kuma ana zaton cewa za a samu karuwar masu bukatar irin kulawa bayan tsagaita bude wuta.
Daga cikin wadanda ke bukatar agajin gaggawa akwai yara 2,500, a cewar Feroze Sidhwa, wani likitan tiyata daga California wanda ya yi aiki a Gaza daga ranar 25 ga Maris zuwa 8 ga Afrilun bara.
Bayanin ya ce daga cikin yaran 2,500 wasu sun fara mutuwa, kuma za su ci gaba da mutuwa matukar ba a gagaguta dake sub a a cewar Guterres.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sama Da Masu Sayayya Daga Ketare 220,000 Ne Suka Halarci Bikin Baje Kolin Canton Karo Na 137
Bikin baje kolin na wannan karo da ake gudanarwa a birnin Guangzhou dake kudancin kasar Sin daga ranar 15 ga watan Afrilu zuwa ranar 5 ga watan Mayu, an shirya shi ne cikin matakai uku. Matakin farko ya mayar da hankali ne kan masana’antu masu ci gaba, na biyu a kan ingantattun kayayyakin gida, na uku kuma a kan kayayyakin dake sa kaimi ga inganta rayuwa. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp