Rashin Tsaro A Nijeriya: Gazawar Masu Mulki Ce Da Cin Amanar Kasa
Published: 2nd, February 2025 GMT
A cewar wani rahoto da kamfanin nazarin al’amuran yau da kullun da siyasa a Najeriya (SBM Intelligence) ya gabatar, tsakanin shekara ta 2011 zuwa 2020, an biya akalla dala miliyan 18.34, wanda ya yi daidai da Naira biliyan 23; ga masu garkuwa da mutane a matsayin kudin fansa.
Ko shakka babu, garkuwa da mutane ya fi aikin gwamnati ko siyasa riba.
Tambayoyin Da Ke Bukatar Amsa Da Matsalolin Da Ke Bukatar Warwarewa
A cikin wannan rudani, ka da mu manta da irin yadda gwamnati ta yi biris da kokarin ganin an magance matsalar rashin tsaron da ke addabar al’ummar wannan kasa, tun daga bangaren zartarwa zuwa na majalisa da kuma na na tsaro. Har wa yau, babban makasudin aikin wadannan mutane shi ne samar da ingantaccen shugabanci tare da tsare rayukan mutane da dukiyoyinsu ba wani abu daban ba.
Bugu da kari, wane kokari kamfanonin sadarwa ke yi don taimakawa wajen dakile wannan matsala? Mene ne tasirin bin diddigin masu aikata laifukan? Gano kudaden haram da kuma sa ido a kan zirga-zirgar ababen more rayuwa kamar babura da wayoyin hannu, wadanda masu aikata laifuka ke amfani da su? Duk wadannan na nuna babbar gazawar tattara bayanan sirri da kuma amfani da fasaha ne.
Shin mene ne amfanin katin shedar zama dan kasa (NIN), da kuma lambar tantancewa ta banki (BBN)? Ko amfaninsu shi ne bude asusun banki ko samun lasisin tuki da fasfo na kasashen waje kadai?
Rashin Adalci Da Tausayi
Dangane da irin wannan ta’asa, ’yan kasa ne wadanda ba su ji ba; ba su gani ba ke daukar nauyin wannan sakaci, wadanda laifinsu kawai shi ne na zama ‘yan Nijeriya, ke fama da wahalhalu da cin zarafin da ba zai iya misaltuwa ba a hannun miyagu marasa tausayi da kuma gwamnatin da ta yi biris da hakkinsu da ke kanta.
Duk da irin wahalhalu da rashi da kuma asarar da aka yi musu, halin da suke ciki ya ta’azzara; sakamakon rashin ingantattun dokoki ko hanyoyin da za a bi don dakile ko hukunta wadannan masu laifi ko kuma samun diyya da tallafi daga gwamnati. A yayin da kukansu na neman adalci da taimako ya fada a kunnen uwar shegu tare da ci gaba da zaman dar-dar, kazalika su kuma masu aikata wannan aika-aika na nan suna yawo cikin walwala, su kuma wadanda hakkinsu ne kama masu aikata wadannan laifuka, sun shagaltu da neman karin albashi tare da yin sharholiya da kudaden gwamnati.
Gazawar Gwamnati Da Hukumomi
Shugabannin Nijeriya, na fuskantar wata muhimmiyar jarrabawa; wanna kuwa ita ce gazawarsu. ‘Yan majalisar dokokin kasar da aka dora wa alhakin wakilcin jama’a, sun yi biris ko kunnen uwar shegu da hakkokin jama’a da ke kansu. Yayin da hukumomin tsaron da suka hada da ma’aikatar tsaron kasar, ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro da kuma rundunar ‘yan sanda; ga dukkanin alamu ba za su iya tinkarar barazanar da ke kara kamarin matsalar tsaron ba.
Har ila yau, an kwashe shekaru da dama ana gudanar da shugabanci na rashin adalci a Nijeriya, wanda wannan alama ce da za a iya gani ko a wannan gwamnati, domin kuwa bangaren zartarwa a halin yanzu na ci gaba da sayen motocin hawa, gina sabbin dakunan zama na shugaban kasa a filin jirgin sama na Abuja da gyaran gidajen gwamnati da ke Legas da Abuja, yayin da kuma sauran ‘yan Nijeriya da dama ba su da matsugunan da za su sanya duwawunsu. Wannan hali na rashin ko in kula na gwamnati, babu shakka ya bar ‘yan kasa a cikin wani mawuyacin hali.
A wannan halin da ake ciki, su kuma ýan majalisun maimakon su kafa dokoki masu tsauri don magance rashin tsaro; sai suka buge da neman a saya musu motocin alfarma kirar ‘Prado jeeps’ kowace daya a kan kudi har Naira miliyan160, motocin da ba za su iya kare su daga sharrin wadannan ‘yan ta’adda masu garkuwa da mutane ba. Yayin da su kuma jami’an tsaro suka kasa samo bakin zaren. Babu shakka, wannan babban abin takaici ne kwarai da gaske.
Kin Amfani Da Na’urorin Fasaha
Gwamnatoci da majalisu daban-daban da suka hada da na yanzu, sun yi ta faman farfaganda a kan batun tsaro tare da bukatar karin kudaden tsaron da kuma batun sayen jiragen ‘Tucano’ da sauran makamantansu, maimakon kalubalen tsaron da ake fuskanta ya ragu, sai ci gaba aka samu ta fuskar ta’adanci, wanda a zahiri ya nuna cewa a gaskiyar magana Nijeriya ta shafe shekaru masu yawa ta na gudanar da shugabanci maras kan-gado da adalci, wanda shi ne ya haifar da wannan yanayi na rashin tsaro da ake fama da shi a halin yanzu.
Shin zai iya yiwuwa gwamnati da sauran hukumomin tabbatar da doka da oda a ce ba su da masaniya game da sahihancin sa ido tare da samar da na’urorin bin diddigin da ka iya taimakawa wajen kawo karshen wannan ta’adanci? Ko kuwa sun yi tsada ne ko kuma Nijeriya ba ta da ma’aikatan da za su tunkari wannan aikin ne?
A Karshe
Tabarbarewar rashin tsaro, wata alama ce ta gazawar gwamnati da hukomomi. Don haka, ya kamata wadanda ke kan madafun iko su amince da gazawarsu tare da gyarawa ko kuma su yi murabus daga mukamansu. Yanzu lokaci ya yi da ya kamata jama’a su fara bin kadin yadda ake gudanar da mulki a kansu. Domin kuwa, jin dadin al’umma da tsaron lafiyarsu shi ne a kan gaba cikin Kudin Tsarin Mulkin Nijeriya, ba siyasa mara ma’ana irin ta wannan kasa ba.
Alhaji Adamu Rabiu ya rubuto daga Kaduna
কীওয়ার্ড: garkuwa da mutane rashin tsaro gwamnati da
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Tsaron Kasar venezuela Ya Gargadi Amurka Dangane Da Kokarin Juyin Mulki A Kasar
Ministan tsaro na kasar Venezuela Vladimir Padrino López ya gargadi gwamnatin Amurka dangane da duk wani kokari na kaiwa kasar Venuzuela hare hare saboda kifar da gwamnatin shugaba Nicolas Madoro. Tare da fakewa da fasakorin kwayoyi.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Vladimir yana cewa take-taken gwamnatin Amurka na sojojin da ta kawo a teken carebian ya yi kama da takalar yaki ne da kasar Venezuela , kuma idan haka ne, to sojojin sa a shirye suke su fuskance su, su kumakare kasarsu.
Kamfanin dillancin labaran IP nakasar Iran ya bayyana cewa, Amurka ta fara kai ruwa rana da gwamnatin shugaba Madoro ne tun lokacinda shugaban Amurka Donal Trump ya bayyana shugaban kasar ta Venezuela a matsayin dan kwaya kuma mai fasa korin kwayoyi.
A halin yanzu dai gwamnatin Trump ta tura sojojinta zuwa tekun Carabian kusa da kasar ta Venezuela da nufin kifar da gwamnatin Nicolas Madoro.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Taron Doha: Daga matakin Allawadai zuwa matakan kalubalantar laifukan Isra’ila September 16, 2025 Pezeshkian: Ya kamata kasashen musulmi su yanke alaka da gwamnatin sahyoniya September 16, 2025 Bayanin Bayan Taron Doha Ya Yi Kira Da A Kafa Rundunar Hadin Gwiwa Ta Kare Kai September 15, 2025 Fira Ministan Spain: Bai Kamata A Rika Barin “Isr’ila” Tana Shiga Gasar September 15, 2025 Shugaban Kasar Iran Ya Gana Da Sarkin Kasar Qatar A Birnin Doha September 15, 2025 Dan Kasar Iran Mai Kirkira Ya Sami Kyautar Yabo A Kasar China September 15, 2025 Fizishkiyan: Wajibi Ne Musulmi Su Hada Kai Domin Dakatar Da Laifukan HKI September 15, 2025 Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Gana Da Takwarorinsa Na Qatar, Turkiyya, Pakistan Da Labanon A Doha September 15, 2025 Kwamitin Kolin Tsron Kasar Iran Ya Amince Da Yarjejeniyar Da Aka Cimma Da Hukumar IAEA September 15, 2025 Jami’in Kasar Yemen Ya Aike Da Sako Ga Mahalarta Taron Birnin Doha Na Kasar Qatar September 15, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci