2025-06-13@12:00:05 GMT
إجمالي نتائج البحث: 908
«kayakin aikin likita»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
’Yan bindiga sun kai hari garin Garo da ke Ƙaramar Hukumar Kabo a Jihar Kano cikin daren ranar Lahadi, inda suka sace wata budurwa mai suna Zainab Auwalu, bayan sun karɓi kuɗin fansa Naira miliyan takwas daga hannun mahaifinta. Zainab, wadda ta kammala makarantar sakandare kwanan nan, an sace ta a gidan mahaifinta, Alhaji Auwalu. SERAP ta maka Tinubu da NCC a kotu kan kara kudin kiran waya da data Shin wannan ce kaka mafi muni ga Man-United a Gasar Firimiya? Shaidu sun bayyana cewa ’yan bindigar, kimanin su 10, sun shiga garin da babura ɗauke da muggan makamai. Sun shiga gidan Alhaji Auwalu da misalin ƙarfe 1:30 na dare, inda suka shafe awanni suna cin karensu ba babbaka, sannan...
Kociyan Manchester United, Ruben Amorim ya faɗa cikin fushi cewa watakila wannan ce kaka mafi muni a tarihin ƙungiyar a Gasar Firimiyar Ingila. Hakan ya biyo bayan shan kashin da ƙungiyar ta yi a gida a hannun Brighton da ci 1-3 a karawar mako na 22 na gasar Firimiyar. Hakan ya kai United matsayi na 13 a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila da maki 26. Ga jerin rashin ƙoƙarin ƙungiyar a shekarun baya: Bayan da Brighton ta yi nasara a kan United a Old Trafford, karo na shida ke nan da aka doke ƙungiyar a gida a wasa na 12 tun bayan 1893/94. United ta ƙare a ƙarshen teburi, lamarin da ya kai ga ta bar buga gasar ta...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping da sauran jagorori na kasar Sin sun ziyarci ko kuma sun gayyaci wasu su ziyarci tsoffin jami’ai da suka yi ritaya, sun mika gaisuwa gabanin bikin Bazara na al’ummar Sinawa na ranar 29 ga watan Janairun nan. Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kwamitin koli na sojan kasar, da sauran jagororin kasar, sun taya tsoffin jami’an da suka yi ritaya murnar bikin Bazara, tare da musu fatan karin lafiya da kuma tsawon rai. A nasu bangaren kuwa, tsoffin jami’an da suka yi ritaya sun yaba da ayyukan kwamitin koli na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin a shekarar da ta gabata, tare da bayyana goyon bayansu...
Majiyoyin leken asirin da suka tabbatar da harin, sun kara da cewa maharan sun kai hari sansanin ne dauke da muggan makamai, inda suka ce ‘yan ta’addan sun lalata gine-gine da dama da kuma motocin aikin soji a yayin harin.
Mutane Na Yawan Tambaya Ta Yaushe Zan Yi Aure – Firdausi Yahaya
Wakilin babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin (CMG) kwanan nan ya tattauna tare da shugaban kasar Sri Lanka Anura Kumara Dissanayake, wanda ya kawo ziyara kasar Sin a karon farko tun bayan hawansa mulki. Da yake magana game da nasarar da kasar Sin ta samu na zamanantar da kanta, Dissanayake ya bayyana cewa, yawan al’ummar kasar Sin ya kai kusan kashi daya bisa biyar na al’ummar duniya, amma kasar Sin ba ta da kashi daya bisa biyar na albarkatun duniya. Ya ce Kasar Sin ta dage kan bin hanyar ci gaba da ta dace da ita, kuma kasar ta samu ci gaba, jama’arta kuma suna rayuwa da aiki cikin kwanciyar hankali. Ya ce, ina ganin yin nazari...
Daga cikin yara ‘yan makaranta miliyan 242 da matsanancin yanayi ya raba da muhallansu a kasashe 85 a shekarar 2024, dalibai miliyan 2 da dubu 200 ne a Najeriya suka rabu da muhallansu, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin ilimi a shekarar. Rahoton wanda Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fitar a daidai lokacin da duniya ke bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025, ya nuna cewa a Najeriya baki daya dalibai miliyan 2,200,200 ne suka daina makaranta sakamakon ambaliyar ruwa. Da take gabatar da jawabi kan tasirin da sauyin yanayi ke da shi ga ilimin yara, shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Farah ya bayyana cewa, ambaliyar ruwa da ta...
Ruben Amorim ya yi amai ya lashe kan kalaman da ya yi cewar ƙungiyarsa ta Manchester United ta kakar nan ita ce mafi muni a tarihi. Sai dai ya ce ba zai yi yaudara ba da cewar ba su da manyan matsaloli ba a kasa. Amorim ya ce ya yi kuskure da ya samar da baraka lokacin da ya fuskanci ƴan wasa nan take, bayan tashi karawar da Brighton ta yi nasara 3-1 a Premier League. Hakan ya sa ya gana da ƴan jarida cikin fushi da ta kai ya faɗi wasu kalaman. An tambaye shi ko ya san cece-kucen da batunsa ya haifar kafin fuskantar Rangers a Europa League, Amorin sai ya ce yana magana da kansa ba da...