An ceto mutum uku da aka yi garkuwa da su a Kebbi
Published: 1st, August 2025 GMT
Rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi ta ce ta ceto wasu mutane uku da aka yi garkuwa da su, bayan sun yi artabu da wasu da ake zargin sun yi garkuwa da su a wani mummunan musayar wuta da aka yi a tsaunin Shanga.
Waɗanda aka yi garkuwan da su sun haɗa da: Muhammad Nasamu Namata mai shekara 25, da Gide Namata mai shekara 20 da Hamidu Alhaji Namani mai shekara 35.
An yin garkuwa da su ne a safiyar ranar 27 ga watan Yuli, 2025, lokacin da masu garkuwa da mutane ɗauke da makamai suka mamaye ƙauyen Sangara da ke Ƙaramar hukumar Shanga.
A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, CSP Nafiu Abubakar ya fitar a ranar Juma’a, ya bayyana cewa wannan ceton ya biyo bayan ɗaukar matakin gaggawa da jami’an ’yan sanda na yankin Shanga suka ɗauka, wanda ya haɗa tawagar jami’an tsaro da suka haɗa da jami’an sojojin Najeriya, jami’an tsaro na Civil Defence da ’yan banga na yankin da mafarauta.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Rundunar ta bi sahun masu garkuwa da mutanen ne zuwa tsaunin Shanga, inda aka yi musayar wuta a tsakaninsu, musayar wutar ta sa jami’an tsaro suka yi nasara kan masu garkuwar.
Daga nan masu garkuwan suka tsere zuwa cikin daji da raunukan harbin bindiga.
“An kuɓutar da waɗanda aka yi garkuwa da su ne ba tare da wani rauni ba, a ranar Alhamis, 31 ga Yuli, 2025 da misalin ƙarfe 3:30 na rana kuma a halin yanzu suna samun kulawar likita kafin su sake haɗuwa da iyalansu.”
Ya ce, Kwamishinan ’yan sanda, CP Bello M. Sani ya yaba wa jarumtaka da ƙwarewa na rundunar, inda ya buƙaci dukkan hukumomin tsaro su ci gaba da haɗa kai. Ya nanata ƙudirin rundunar na kare rayuka da dukiyoyi a Jihar Kebbi.
Kwamishinan ya kuma yi kira ga al’ummar yankin da su sanya ido tare da kai rahoto ga jami’an tsaro mafi kusa domin ɗaukar matakin gaggawa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: masu garkuwan da mutane da aka yi garkuwa yi garkuwa da su jami an tsaro masu garkuwa
এছাড়াও পড়ুন:
Hare-hare: ’Yan bindiga sun raba mutum 5,000 da muhallansu a Katsina
Sama da mutum 5,000 ne suka tsere daga gidajensu a Jihar Katsina, sakamakon sabbin hare-haren da ’yan bindiga suka kai a Ƙananan Hukumomin Bakori da Faskari.
Mutane daga ƙauyuka sama da 10 sun nemi mafaka a garin Bakori, inda da dama ke zaune wajen ’yan uwansu, yayin da wasu ke kwana a waje ba tare da masauki ko abinci ba.
Wasu ’yan siyasa na sukar Tinubu saboda ɗan Kudu ne — Onanuga Tallafin matar Tinubu na N1bn ga ’yan gudun hijirar Binuwai ya bar baya da kuraWasu daga cikin waɗanda abin ya shafa sun bayyana cewa, maharan sukan shiga ƙauyuka da yawa, inda suka dinga harbi, ƙone gidaje, sannan suka sace mutane ciki har da mata da ƙananan yara.
Hare-haren sun fi muni a auyuka irin su Guga, Anguwar Danmarka, Gidan Sule, da sauransu.
Wani dattijo mai shekara’u 68 daga ƙauyen Doma ya ce sama da mutum 250 aka kashe a yankinsa cikin shekaru biyar da suka wuce.
Ya ƙara da cewa ’yan bindigar sukan ƙone rumbunan abinci tare da sace dabbobi.
Wata mata da ta kuɓuta daga harin a Anguwar Galadima ta ce iyalinta su 17 sun tsere, inda ta ce an sace sama da mutum 20 a ƙauyen nasu.
Wani saurayi daga Anguwar Dan Marka ya bayyana yadda aka harbe shi sau biyu a ƙafa, kuma yanzu yana amfani da sanda wajen yin tafiya.
Wasu da dama har yanzu suna hannun maharan, yayin da suke neman fansar Naira miliyan 1.5 kan kowane mutum ɗaya.
Manoma ma na kuka da halin da suka tsinci kansu sakamakon hare-haren.
A wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, wani manomi daga Ƙaramar Hukumar Sabuwa ya koka da yadda aka lalata gonarsa.
Amma a martanin da suka bayar, shugabannin Ƙaramar Hukumar sun ce an lalata gonakin da ke kusa da manyan tituna ne domin hana ’yan bindiga amfani da su wajen ɓuya da kuma kai wa matafiya hari.
Amma manoman suna kallon wannan a matsayin wata matsala a gare su.
Shugabannin ƙauyuka da hukumomin gwamnati sun tabbatar da cewa mutane suna ƙara zuwa Bakori kowace rana don neman mafaka.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Bakori, ya ce akwai sama da mutum 3,500 da ke zaune a Bakori, yayin da wasu sama da 2,000 ke zaune a ƙauyen Guga.
An fara raba wa waɗanda suka rasa matsugunansu abinci da kayan masarufi, amma ana buƙatar samum ƙarin taimako.
Ƙungiya ta buƙaci a ayyana dokar ta-ɓaci a BakoriAn buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta jiha da kuma ƙungiyoyin agaji su kai wa waɗanda lamarin ya shafa ɗauki cikin gaggawa.
Wata ƙungiya mai zaman kanta mai suna ‘Grassroots Advocates for Peace’ ta nemi Gwamnatin Tarayya ta ayyana Bakori a matsayin yanki mai hatsari.
Sun buƙaci ƙarin jami’an tsaro, da ɗaukar mataki cikin gaggawa.
Sun kuma buƙaci a kula da lafiyar kwakwalwar waɗanda suka kuɓuta daga hare-haren da kuma hukunta masu kai hare-haren.
Gwamnatin Katsina na ƙoƙarin magance matsalarA nata ɓangaren, Gwamnatin Jihar Katsina, ta ce tana ƙoƙarin wajen magance matsalar.
Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na Jihar, Nasir Muazu, ya ce suna ƙoƙarin magance matsalolin da Ƙaramar Hukumar ke fama da su.
Ya ce akwai wasu mutane da ke ƙoƙarin yada ƙarya a kafafen sada zumunta don haifar da tsoro da ruɗani a zukatan jama’a.
Ya kuma ce an samu sauƙin kai hare-hare a wasu yankuna kamar Jibia da Batsari.
Kwamishinan, ya bayyana cewa an kafa rundunar ‘Katsina Community Watch Corps’ domin taimaka wa sojoji, ’yan sanda da ’yan sa-kai wajen shiga dazuka da ke da wuyar shiga.
Sai dai ya buƙaci jama’a da su ci gaba da jajircewa da kuma bayar da rahoton duk wani abu da su yarda da shi ba.
An samu sauƙin kai hare-hare cikin shekara 2 — RibaduA yayin da gwamnati ke cewa ana samun ci gaba, Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkar Tsaro, Nuhu Ribadu, ya ce Najeriya ta fi samun zaman lafiya a yanzu sama da shekaru biyu da suka wuce.
Ya ce an ceto da mutum sama da 11,000 da aka sace, kuma an kashe wasu daga cikin manyan shugabannin ’yan bindiga.
Ya yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, bisa jagoranci da tsare-tsaren tsaro da suka haifar da wannan sauyi.
Sai dai waɗanda ke zaune a matsuguni na wucin gadi a Bakori da wasu yankuna, rayuwa cikin tsaka mai wuya.
Wasu sun ce har yanzu ba su da ƙwarin gwiwar komawa gidajensu.
Sun tabbatar da cewar sai gwamnati ta samar da tsaro mai ɗorewa, sannan za su koma muhallansu, saɓanin haka za su ci gaba da zama a inda suke a yanzu.