Majalisar Dokokin Sokoto Ta Aike Wa Kwamishina Sammaci, Duba Dalili
Published: 1st, August 2025 GMT
Majalisar Dokokin Jihar Sokoto ta umarci Kwamishinan harkokin makamashi da albarkatun man Fetur, Hon. Sanusi Danfulani, da ya bayyana a gabanta ranar Talata, 5 ga watan Agusta, saboda gazawarsa wajen halartar ziyarar duba aiki da kwamitin majalisar mai kula da kimiyya da fasaha ya gudanar.
Ziyarar da aka shirya a ranar Alhamis ta sami tsaiko sakamakon rashin halartar Danfulani da wasu manyan jami’an ma’aikatarsa, lamarin da shugaban kwamitin, Awaisu Aliyu, ya bayyana a matsayin “wulakanci da sakaci da aiki da ga rashin mutunta majalisar dokoki.
Aliyu ya ce, “An aika musu da sanarwa cikin lokaci game da ziyarar, amma babu wani jami’i daga ma’aikatar da ya halarta, sannan babu wani bayani na rashin zuwa daga gare su.”
Ya ƙara da cewa irin wannan sakaci yana tauye ikon da kundin tsarin mulki ya bai wa majalisar wajen gudanar da aikinta na sa ido. Don haka, ya umurci Danfulani da ya halarci zaman majalisar a ranar 5 ga Agusta ko kuma ya fuskanci hukunci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Rashin Nasarar DPP A Zagayen Farko Na Kuri’ar Kiranye Ya Nuna Rashin Amincewar Al’ummar Taiwan Da Salon Mulkin Jami’yyar
Kakakin ofishi mai lura da harkokin yankin Taiwan a majalisar gudanarwar kasar Sin Chen Binhua, ya ce kalaman da aka jiyo jagoran yankin Taiwan na kasar Sin Lai Ching-te na yi dangane da sakamakon zagayen farko na kuri’ar kiranye da al’ummar Taiwan suka kada, ya nuna rashin gamsuwarsu da salon mulkin jam’iyyar DPP mai mulkin yankin.
Chen Binhua, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a Larabar nan, ya ce kalaman Lai na cike da yaudarar kai, sun kuma fayyace manufar da ya dage a kanta ta “neman ’yancin kan Taiwan”. Kazalika, mummunan kayen da DPP ta sha a kuri’un da aka kada ranar Asabar din karshen makon jiya, ya fayyace ajandarta ta yin fito-na-fito da Sin, tare da fafutukar neman ’yancin kan Taiwan, matakin da ya yi hannun riga da ra’ayoyin al’ummun Taiwan, kuma zai fuskanci turjiya daga akasarin al’ummun yankin na Taiwan. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp