INEC za ta fara rajistar ƙuri’a a ranar 18 ga Agusta
Published: 1st, August 2025 GMT
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), za ta fara rajistar ƙuri’a ta intanet a ranar 18 ga watan Agusta, 2025, domin tunkurar zaɓen 2027.
Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar ban girma da Hukumar NOA ta masa a hedikwatar INEC da ke Abuja.
Rundunar sojin ruwa za ta kafa sansaninta a Kebbi Ɗaliban da aka sace a Binuwai sun kuɓutaYa kuma ce sai a ranar 25 ga watan Agusta, 2025 za a fara rajistar ƙuri’a a zahiri.
“Za a fara rajistar ƙuri’a ta Intanet a faɗin ƙasa daga ranar 18 ga watan Agusta,” in ji Farfesa Yakubu.
“Rajistar ƙuri’ar a zahiri kuma za ta fara daga 25 ga watan Agusta, 2025,” a cewarsa.
Hukumar INEC na shirin fara wannan rajista ne domin zaɓen gwamnan Jihar Anambra da za a yi a ranar 8 ga watan Nuwamba, 2025, da kuma babban zaɓen 2027.
INEC da NOA sun amince da ci gaba da yin haɗin gwiwa a fannin wayar da kai game da harkokin zaɓe da amfani da ƙirƙirarriyar fasaha (AI) don bunƙasa harkokin zaɓe.
“Ayyukan gudanar da zaɓe ba za su yi tasiri ba sai an wayar da kan ‘yan ƙasa, kuma wannan shi ne babban aikin NOA a Najeriya,” in ji Farfesa Yakubu.
Shugaban NOA, Malam Lanre Issa-Onilu, ya ce suna kan aikin yin gyara da sabunta ayyukansu domin amfanar da dimokuraɗiyya.
Ya ce yanzu NOA na da sassa 16 da ke kula da shirye-shirye, ciki har da sabuwar Ma’aikatar Koyar da Darusan Dimokuraɗiyya.
“A yanzu muna da sassa 16, ciki har da sabuwar Ma’aikatar Koyar Darusan Dimokuraɗiyya,” in ji shi.
INEC ta buƙaci NOA ta ci gaba da amfani da kafafen watsa labarai da na zamani don jawo hankalin mata, matasa da nakasassu don shiga harkokin zaɓe.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: rajista Zaɓe a fara rajistar ƙuri a ga watan Agusta
এছাড়াও পড়ুন:
Faransa Za Ta Fara Jefa Kayan Agaji Ta Sama A Gaza
Ministan ya kuma ce ƙasarsa na shirin sanya hannu a wata takarda don neman goyon bayan sauran ƙasashe wajen ganin an kafa ƙasar Falasɗinu da Isra’ila.
A taron Majalisar Ɗinkin Duniya da aka gudanar na kwana biyu, ƙasashe 125 sun amince cewa hanyar warware rikicin Gaza ita ce kafa ƙasashe biyu, wato Falasɗinu da Isra’ila.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp