JAN KUNNE: Ɗan Atiku Abubakar ya mayar wa ɗan gwamnan Bauchi zazzafan martani
Published: 16th, April 2025 GMT
Muhammad Atiku wanda ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasa ne, ya ce, gwamnna Bauchi, Bala Mohammed, bai taɓa mara wa mahaifinsa baya ba a zaɓukan 2019 da 2023 da aka yi.
Ɗan Atiku na wannan kalamai ne a matsayin martani ga ɗan gwamnan Bauchi, Shamsu Bala wanda ya zargi ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasa da yi wa mahaifinsa maƙarƙashiya a zaɓen 2023.
A ranar Asabar ce, Shamsu ya ce Atiku ba ma ya tunanin zuwa ya nemi gafarar mahaifinsa duk kuwa da shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027 da yake yi.
“Bambancin da ake akwai yanzu shi ne Shamsu ya fito fili ya nuna mana cewa ka da mu sa ran samun goyon mahaifinsa (gwamnan Bauchi),” ya faɗa.
Ɗan Atiku Abubakar ya yi wannan martanin ne cikin wani saƙo da ya aiko wa da Premium Times a ranar Litinin, yana mai jaddada cewa gwamnan Bauchi ne ya yi wa mahifinsa zagon ƙasa a zaɓen 2023.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: gwamnan Bauchi
এছাড়াও পড়ুন:
Ba mu da tabbas na ci gaba da rijistar kaɗa ƙuri’a a Borno – INEC
Hukumar Zaɓe Mai zaman kanta ta Ƙasa a Jihar Borno ta bayyana cewa, babu tabbas na gudanar da aikin rijistar masu kaɗa ƙuri’a na shekarar 2025/2026 a wasu Ƙananan hukumomin Jihar huɗu don matsalar tsaro.
Ƙananan hukumonin sun haɗa da: Ƙaramar Hukumar Abadam da Guzamala da Marte da Kala-Balge
Ambaliya: Magidanta da dama sun rasa muhallinsu a Yobe An sake ceto matafiya 10 da aka sace a KogiBayanin hakan dai ya fito ne daga bakin Kwamishinan zaɓe na Jihar Borno, Abubakar Ahmad Ma’aji a jawabinsa ga manema labarai a Maiduguri, a wani ɓangare na shirye-shiryen fara gudanar da aikin rijistar masu kaɗa kuri’a a ranar Litinin da ke tafe.
Kamar yadda Kwamishinan Hukumar zaɓen ke bayyanawa, INEC ta mayar da rijistar masu kaɗa ƙuri’a na ci gaba da gudana a Ƙaramar hukumar Abadam zuwa kan hanyar Baga daura da ofishin Yerwa Peace.
Haka nan shi kuma aikin rijistar masu kaɗa ƙuri’a na Ƙaramar hukumar Guzamala an mayar da shi a sashen kashe gobara na rukunin gidaje 1,000.
Sauran Ƙananan hukumomin kamar Ƙaramar hukumar Kala-Balge an mayar da aikin ya zuwa makarantar firamare ta Goni Kachalari da ke birnin na Maiduguri.
Shi kuma aikin rijistar masu kaɗa ƙuri’a na Ƙaramar hukumar Marte an mayar da shi ya zuwa Kachamai, waɗanda dukkansu suna cikin birnin Maiduguri ne.
Don haka Kwamishinan ya yi kira ga mutanen waɗannan ƙananan hukumomin da su yi haƙuri da wannan canji da aka samu an yi ne da kyakkyawar manufar da duk wanda abin ya shafa zai samu rijistar katinsa na kaɗa ƙuri’a cikin kwanciyar hankali.