2025-10-15@12:11:45 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3340
«Takara»:
A Italiya mutane da dama sun jikkata yayin arangama tsakanin ‘yan sanda da masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinu. Rahotanni sun ce kimanin mutane 10 ne suka jikkata yayin zanga-zangar ta nuna goyon bayan Falasdinu bayan da ‘yan sanda suka yi kokarin hana masu zanga-zangar da ruwan zafi da hayaki mai sa hawaye a ranar Asabar....
Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Sakandare a Nijeriya (NECO) ta jaddada cewa Jihar Kano ce ta fi kowace jiha samun nasara a sakamakon jarrabawar bana, tana mai ƙaryata rahoton da jaridar Premium Times ta fitar, wanda ya ce Jihar Abia ce ke kan gaba. A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta bayyana cewa rahoton...
Kasashen Afirka ta Kudu da Sin sun kaddamar da wani sabon yunkuri na zurfafa dangantakar tattalin arziki, inda Beijing ta yi alkawarin zuba jari a fannin hakar ma’adinai, makamashi, da ababen more rayuwa. Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da Pretoria ke fuskantar matsanancin matsin lamba daga sabbin harajin da Amurka ta sanya mata...
Gwamnatin Jamhuriyyar Nijar ta zargi Faransa da ɗaukar shekaru tana haifar da rikice-rikice da rashin tsaro a ƙasar da maƙotanta na yankin Sahel, tun daga shekarar 1899. Firaministan Nijar, Ali Lamine Zeine, ne ya yi wannan furuci ranar Asabar yayin gabatar da jawabi a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 (UNGA 80) da...
Ko za ka fadawa masu karatu dan takaitaccen tarihinka? An haife ni a unguwar Tudun Nufawa dake Kano Municipal, na yi karatun firamare a jakara ‘Special Pramary School’, na yi sakandare a Gwammmaja 2. Sannan babban Sakandare a ‘GSS Dala’. Na yi karatun ‘Diploma’ a fannin ‘computer’, sannan na yi ‘National Diploma’ akan lafiyar hakori...
Gwamnatin Jamhuriyyar Nijar ta yi zargin cewa tun daga shekarar 1899 Faransa take fafutikar tayar da rikici da haddasa rashin tsaro a ƙasar da maƙotanta na yankin Sahel. Firimanistan Jamhuriyyar Nijar, Ali Lamine Zeine, ya yi wannan caccakar ce kan Faransa a ranar Asabar yayin da yake gabatar da jawabi a Babban Taron Majalisar Dinkin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Yawan ribar da manyan kamfanoni na kasar Sin suke samu ta karu da kashi 0.9 cikin 100 a mizanin shekara-shekara a cikin watanni takwas na farkon shekarar 2025, lamarin da ya farfado da raguwar da aka samu da kashi 1.7 cikin 100 a tsakanin watannin Janairu zuwa Yuli, kamar yadda alkaluman hukuma suka nuna a...
Ƙungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta Najeriya, reshen Jihar Zamfara, ta ce sun shiga yajin aiki na kwanaki shida a matsayin gargaɗi. Shugaban ƙungiyar, Sani Shehu, ya ce sun ɗauki wannan mataki ne domin tunatar da gwamnati batun sabon tsarin albashi na ma’aikatan lafiya. AGILE ta raba kayan karatu da sana’o’i a cibiyoyi 54 a...
Ƙungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta Najeriya, reshen Jihar Zamfara, ta ce sun shiga yajin aiki na kwanaki shida a matsayin gargaɗi. Shugaban ƙungiyar, Sani Shehu, ya ce sun ɗauki wannan mataki ne domin tunatar da gwamnati batun sabon tsarin albashi na ma’aikatan lafiya. AGILE ta raba kayan karatu da sana’o’i a cibiyoyi 54 a...
Da yake bayani a wajen taron na tunawa da shahadar sayyid Hassan Nasrullah da kuma sayyid hashim safiyyudden , babban sakatare janar din kungiyar Hizbullah, shaikh Naim qasem,yace tsayin daka da marigayi sayyid hassan nasrullah yayi ya zarce bangaranci, kuma ya zaburar da musulmi da kirsitoci da duk masu kishin addini , Yace tunani da...
Yunkurin kasashen rasha da china na jirkinta dawowa da iran takunkumi har na tsawon wata 6 bai yi nasara ba a kwamitin tsaro na MDD saboda kasashe 4 ne suka nuna goyon bayansu da suka hada da kasashen China Rasha Pakistan da kuma Aljeriya, yayin da kasashe 9 kuma suka nuna rashin amincewa da shirin...
Shirin AGILE, ya raba kayan koyarwa da na sana’o’i ga cibiyoyin karatun boko na wucin gadi guda 54 a faɗin Jihar Gombe. Kwamishiniyar Ilimi ta jihar, Dakta Aishatu Umar Maigari, ce ta ƙaddamar da rabon kayan a cibiyar Community Education Resource Centre da ke Gombe. HOTUNA: An kai gawar Arase Benin domin yi mata jana’iza...
A jawabinsa na maraba da mahalarta taron, Shugaba kuma Wakilin ofishin hukuma da ke Abuja wanda har ila yau wakilin UNESCO, na Nijeriya, Mista Mendy Albert, wanda Misa Manish Joshi ya wakilta, ya ce tsarin da akwai kwas na mako 10- ta kafar sadarwa ta zamani wanda aka kammala a watan Yuli, an shirya shi...
Wane irin farin ciki za ku ji a matsayinku na iyaye, a cewa ’ya’yanku biyu sun kammala jami’a da Digiri Mai Daraja ta Ɗaya (First Class) a lokaci guda kuma daga wani kwas mai farin jini a wannan zamani na kimiyyar zamani? Wani labari mai sha’awa shi ne yadda wasu ’yan uwa biyu suka kammala...
Kamfanin Matatar Man Ɗangote ya sanar da dakatar da sayar da manta ga kwastomomi a kan farashin Naira. Kamfanin ya ce daga ranar Lahadi 28 ga watan nan na Satumba da muke ciki, zai koma sayar da tataccen mansa a kan farashin Dala. Wata samarwa da ya aike wa kwastomominsa ta ce, yin hakan ya...
Gwamnatin Jihar Gombe ta haramta amfani da littattafan karatu da ba sa iya amfani sau biyu da kuma bukukuwan ‘sign-out’ da dalibai ke gudanarwa a bayan jarrabawar kammala karatu. Daraktan Kula da Ingancin Ilimi na Ma’aikatar Ilimi ta jihar, Sa’idu Dauda Gadam, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Juma’a....
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta kirayi jakadun kasarta a kasashen Biritaniya, faransa da kuma jamus domin tuntuba, a daidai lokacin da takun tsaka tsakaninta da kasashen ke kara kamari sanadin yunkuinsu na ganin an sake dawo ma Iran da takunkuman MDD. A cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar yau Asabar ta ce “Bayan matakin...
Ya kara da cewa wadanda ake zargin suna nan a gidan yari kuma nan ba da jimawa ba za a gurfanar da su a gaban kotu domin hukunci. Kwamishinan ’Yansandan Jihar, CP Bello M. Sani, ya yaba wa kwazon da DPO da ’yan banga suka yi da gaggawa, inda ya jaddada muhimmancin hadin kan ‘yansanda...
Hukumar jin daɗin Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta sanar da farashin aikin Hajjin 2026, inda aka samu ragin kaso 9.7% cikin ɗari idan aka kwatanta da farashin Hajjin bara 2025. A cewar sanarwar da shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Sale Usman, ya fitar ranar Juma’a da daddare, alhazai daga gundumar Maiduguri–Yola (Borno, Yobe, Adamawa da Taraba)...
MDD ta kara yawan sunayen kamfanonin da su ka yi aiki tare da HKI wajen keta hakkokin al’ummar Falasdinu, ta hanyar ayyukan da suke aiwatarwa a cikin sansanonin yahudawa ‘yan share wuri zauna. A cikin rumbun bayanan MDD dai an fara zayyana sunayen kamfanoni 11, da a halin yanzu sun karu zuwa 158. Tun a...
Haka kuma, ya fadi zaben shugaban kasa na 2015 ga dan takarar jam’iyyar APC, Marigayi Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a watan Yuli na wannan shekara. Akwai zazzafar muhawara kan dokar da ta bai wa Jonathan damar sake tsayawa takarar shugaban kasa a 2027, tsohon gwamnan Jihar Jigawa kuma daya daga cikin shahararrun jiga-jigan jam’iyyar...
Wanda duk zai gaya maka gaskiya musamman wanda yake zaune ko ya ke zuwa wuraren da aka samu matsalar tsaro a wasu kananan hukumomi na jihar Katsina zai fada maka cewar an samu zaman lafiya fiye da lokutan baya. An sha ruwaito wadanda wannan bala’i ya shafa suna maida martani ga masu suka sulhu da...
Gwamnatin Jihar Kano ta miƙa ƙorafe-ƙorafen da aka yi a kan Malam Shu’aibu Abubakar, wanda aka fi sani da Triumph, ga Kwamitin Shura na Jihar don ɗaukar matakin da ya dace. Sakataren Gwamnatin Jihar ne, ya tura ƙorafe-ƙorafen a ranar Juma’a, inda kwamitin ya fara zama domin sauraronsu. ’Yan Najeriya da tauraronsu ya haska a...
Jami’an ’yan sanda a Jihar Ondo sun kuɓutar da wata yarinya ’yar shekara huɗu da ta ɓace tare da gano wasu masu fataucin yara da ke gudanar da ayyukan su a yankunan Jihohin Ondo, Delta da Anambra. An fara shari’ar ne a ranar 3 ga Fabrairu, 2025, lokacin da Sunday Kingsley da ke yankin Alagbaka...
Gwamnatin Tarayya ta amince da sabuwar dokar haraji wadda za ta bai wa ’yan haya damar samun ragin har Naira dubu ɗari biyar. Dokar ta amince da yi wa ’yan haya ragin kashi 20% daga harajin kudin shiga a kan kuɗin hayar da suke biya a shekara. Sojoji sun kashe ’yan ta’adda tare da ƙwato...
Reform ya kuma ce yana shirin hana wani wanda ba dan Biritaniya ba damar samun walwala. Jam’iyyar ta yi ikirarin cewa shirin nasu zai yi tanadin fam biliyan 234 cikin shekaru da dama. Chancella Rachel Reebes ta ce tanadin da aka ba da shawarar “ba shi da tushe a zahiri” kuma tuni gwamnati ta fara...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Aƙalla mutum biyar ne suka rasu lokacin da ’yan bindiga suka kai hari wani Masallaci, yayin da ake tsaka da sallar Asuba a garin Yandoto da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe a Jihar Zamfara. Harin ya faru ne da safiyar ranar Juma’a, lamarin da ya girgiza al’ummar yankin. ‘Da albashin aikin masinja na fara kasuwancin Sahad...
Duk wani bangaren wayewa da kimiyya da fasaha za ka ga asali malaman Musulunci ne suka zo da shi, babu lokaci isasshe da mun kawo misalai masu yawa. yana daga cikin wayewar nan: tashi a sama zuwa duniyar wata, da duk “technology” din nan na zamani, harkar zane-zane, kade-kade, bushe-bushe. Amma duk aka kwashe wadannan...
Sahad Store sanannen suna ne a fadin Nijeriya, wanda yawancin wanda ya ji sunan, abin da ke fara zuwa ransa shi ne manyan shagunan sayar da kaya. Amma ba kowa ne ya san tarihin yadda ya faro ba, balle mallakinsa. Alhaji Ibrahim Mijinyawa, dan kasuwa, haifaffen unguwar Mandawari da ke birnin Kano. A cikin wata...
Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce ba su da matsala da yunkurin da aka ce tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso na yi na komawa jam’iyyar. Sai dai Ganduje ya ce suna da sharadin da dole sai Kwankwason ya amince da shi kafin ya shiga jam’iyyar. Aminiya ta rawaito...
Sojojin Yemen sun kaddamar da mummunan farmaki kan yankin Jaffa da makami mai linzami Sojojin Yemen sun sanar a yammacin jiya Alhamis cewa; Sun kai hari da makami mai linzami kan yankin Jaffa da aka mamaye. A cikin wata sanarwa da rundunar sojin Yemen ta fitar ta tabbatar da cewa: Rundunar sojinta ta kai wani...

Yadda Sauye-Sauyen Da Aka Yi A Fannin Mai Da Iskar Gas Suka Samar Da Gagarumin Ci Gaba A Wannan Shekarar
Shugaban a kasidar da ya gabatar a wajen taron mai taken: “Ingantattun Sauye-Sauyen da Nijeriya ta kirkiro da su domin cin gajiyar albarkatun da ke a Man Fetur da Iskar Gas”, ya jaddada mahimmancin da ke a fannin Makamashi, musamman wajen kara bunkasa tattalin arzikin kasa da kuma yadda Afirka, za ta amfana. Ya ci...
A yau Juma’a Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo zai mika sandar sarauta ga sabon Olubadan na Ibadan na 44, Oba Rashid Adewolu Ladoja. Ana sa ran Shugaba Bola Ahmed Tinubu da tsohon mataimakin Shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar za su halarci wannan gagarumin biki da aka shirya yi a Ibadan babban birnin Jihar Oyo....
Tashar ta jihar Legas na da natukar mahimmanci a tsarin jigilar shofar da kaya a kasar nan wadda kuma ta kasance a kan gaba wajen kara bunkasa fannin tattalin arzikin kasar nan. A hirar da da manema labarai Manajin Darakta na TTP Jama Onwubuariri ya bayyana cewa, wasu daga cikin nasarorin da aka samu a...
Daga karshe,mahalarta taron sun meni a samar da wata kungiya da za ta jagoranci isar da sakon akidojin Bala Usman ga al’umma domin bai kamata a bar irin wannan kyawawan fata na Bala Usman su tafi a banza ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai...
Alkaluma sun nuna cewa, a yankin Arewa Maso Gabas, kalubalen rashin tsaro ya dakatar da akalla yara miliyan 20, daga zuwa Makarantar Boko tare tare da kuma yadda hare-haren, suka lalata Makarantun Boko da dama da ke a yankin, wanda hakan ya janyo gagarumar tazara a tsakain yankin da kuma Kudancin kasar, tare da kuma...
Dakarun Yaman sun sanar da cewa, sun kai wani harin soji mai inganci ta hanyar amfani da makami mai linzami na “Falasdinawa 2” mai dauke da kawuna da dama, kan wasu hare-hare da Isra’ila ta kai a yankin Jaffa da ta mamaye. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta Birgediya Janar Yahya Saree...
Kwararan bayanai na nuni da cewa tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya fara tattaunawa da Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, kan shirin komawa jam’iyyar. Majiyoyi daga cikin APC a Kano sun bayyana cewa Kwankwaso ya rubuta wasiƙa zuwa sakatariyar jam’iyyar ta ƙasa a Abuja, yana sanar da aniyarsa ta...
Dangin wata yarinya ’yar shekara 14 a unguwar Gangare da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato, sun nemi a bi musu haƙƙi bisa zargin fyaɗen da wani mazaunin unguwar ya yi mata. Bayanai sun ce tun farko an cafke mutumin da ake zargi, Ibrahim Rawi, wanda da fi sani da Baban Siyama,...
Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta kama wani matashi ɗan shekara 30 mai suna Mutawakilu Ibrahim da laifin daɓa wa kakanninsa wuwa har lahira bayan wata taƙaddama kan abinci a Ƙofar Dawanau Ƙuarters da ke cikin birnin Kano. A cewar wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna...

An Yi Bikin Nune-Nunen Hotuna Da Bidiyo Na MDD Da Bikin Kade-Kaden Fina-Finai Masu Alaka Da Zaman Lafiya A Birnin New York
Bugu da kari, mahalarta bikin sun bayyana cewa, bikin ya nuna maimaituwar tarihin MDD na shekaru 80 da suka gabata, tare da yin kira da a karfafa hadin gwiwa tsakanin bangarori daban daban, domin karfafa aniyar al’ummomin kasashen duniya ta kare zaman lafiya, da inganta fahimtar juna. Haka kuma, Babban rukunin gidan rediyo da...
Ba madatsar ruwa ta Dashimen kadai ce ta ba da damar noma amfanin gona a cikin yankin hamada ba. A cikin shekaru goma da suka gabata, yawan madatsan ruwa da aka gina ko gyara a yankin kwarin Tarim ya kai fiye da 120, wadanda suka hada rassan kogin Tarim 144, kuma hakan ya samar da...
An gurfanar da wasu malamai biyu na wata makaranta ta Zariya Children School da ke yankin GRA Zariya, a gaban kotun majistare da ke Tudun Wada bisa zargin lalata wata ɗalibar makarantar mai shekaru 11. Jami’in da ke gabatar da ƙara a gaban kotun, ASC Mustapha Abdulkadir, ya ce malamai biyu tare da wasu uku...
Shugaban Hukumar Alhazzan Jihar Yobe, Alhaji Mai Aliyu Usman Biriri ya bayyana cewar sun gudanar da aikin Hajjin 2025 cikin nasara da kwanciyar hankali. Mai Aliyu ya bayyana hakan ne ranar Laraba a tattaunawarsa da manema labarai a babban ɗakin taron Hukumar da ke garin Damaturu dangane da yadda suka gudanar da aikin hajjin bara. An...
Gwamnatin Jihar Katsina ta kori ma’aikata 3,488 daga ƙananan hukumomi 34 da hukumomin ilimi na ƙananan hukumomi (LEA) bayan wani binciken tantance su ya bankado badakala. Gwamnan jihar, Dikko Radda, wanda ya karɓi rahoton kwamitin a ranar Laraba, ya ce an tantance ma’aikata 50,172, inda aka tabbatar da sahihancin 46,380, yayin da sauran suka bayyana...
Wannan domar dai an dogara da kundin tsarin aikin gwamnatin Tarayya bisa ga sashe na 10(1) na dokar Ilimi ta (National Minimum Standards and Establishment of Institutions) ta shekarar 1985. A baya-bayan nan, an gano cewa sama da mutum 22,500 sun yi amfani da takardun bogi daga jami’o’i marasa izini a Benin da Togo...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin Tarayya ta umarci dukkanin ma’aikatu, hukumomi, sojoji da kuma cibiyoyin kuɗi da ma’aikatu masu zaman kansu da su fara tantance takardun shaidar kammala makaranta na ma’aikatansu daga ranar 6 ga watan Oktoba, 2025. Wannan mataki ya biyo bayan yawaitar bogi da takardun karatu na bogi a Najeriya. Shugaban EFCC ya bayyana a Aso Rock...