2025-10-13@22:26:50 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4223

«Trading»:

    Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce soke faretin zagayowar ranar ’yancin kai karo na 65 da sojoji ke yi ya ba shi damar yin lafiyayyen barci da kuma yin kyakkyawan kari a ranar Laraba. Aminiya ta rawaito cewa Gwamnatin Tarayya ta soke bikin da aka shirya domin murnar cikar Najeriya shekara 65 da samun ‘yancin...
    Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana damuwarta kan yadda likitoci ke kin zuwa aiki musamman a lokutan da suke kai ziyara wuraren kiwon lafiya da ba a shirya ba.   A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar lafiya ta jihar, Suleiman Isah ya fitar, ya ce kwamishinan lafiya Dr. Nafisa Muhammad Maradun ta...
    Tsohon Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Gombe, Julius Ishaya Lepes, ya rasu. Ishaya, ya riƙe mukamin Kwamishina a farkon gwamnatin Inuwa Yahaya na tsawon shekaru huɗu, amma ya yi murabus domin yin takara. Tinubu ya buƙaci ’yan Najeriya su daina yi wa ƙasar mummunan fata Rashin Tsaro: An rufe makarantu sama da 180 a Arewacin...
    Mai magana da yawun gwamnatin Iran Fatemah Mohajerani ta fayyace cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta maraba da yaki, amma tana ci gaba da shirye-shiryen tsaro mafi girma  don kare kanta. Ta kara da cewa Tehran ta bayar  da shawarar tattaunawa da Amurka kai tsaye a wata ganawa tare da  ministocin  Turai, amma wakilin...
    Kungiyar Global Sumud Flotilla ta fitar da wata sanarwa a daren jiya Laraba inda ta sanar da cewa sojojin mamaya na Isra’ila sun kai farmaki a kan jiragenta da ke kan hanyar isa Gaza domin kai kayan agaji, inda suka lalata kamarori da kuma sauran kayan ayyukan fasaha da suke cikin wasu daga cikin jiragen...
    Jakadan kasar Rasha a Majalisar Dinkin Duniya, Vasily Nebenzya, ya ce maido da tsarin takunkuman karya tattalin arziki a kan Iran da wasu kasashen yammacin duniya suka yi ya saba wa kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya. Nebenzya ya bayyana hakan ne a wata doguwar wasika da ya aike wa babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya...
    Adadin wadanda suka yi shahahda a yakin kisan kare dangi da Isra’ila ke aiwatarwa kan al’ummar yankin zirin Gaza ya kai shahidai 66,148 da kuma jikkata wasu 168,716, tun daga ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023. Bisa kididdigar baya-bayan nan da ma’aikatar lafiya ta zirin Gaza ta fitar, adadin wadanda suka yi shahada tun...
    Aƙalla makarantu 188 na gwamnati aka rufe a Arewacin Najeriya sakamakon ta’azzarar matsalar tsaro. ’Yan bindiga sun kai wa wasu makarantun hari, yayin da wasu kuma yanzu ana amfani da su a matsayin mafakar ’yan gudun hijira ko sansanonin sojoji. Antoine Griezmann ya ci ƙwallo 200 a Atletico Kwamitin Shura ya dakatar da Malam Lawan...
    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta PSG, ta doke Barcelona a wasan mako na 2 na gasar Zakarun Turai a wasan da suka buga a filin wasa na Luis Companys. Ferran Torres ne ya fara jefa ƙwallon a ragar PSG a minti na 19 da fara wasan, amma gab da tafiya hutun rabin lokaci Senny Mayulu ya...
    Fitaccen masanin karatu da ƙira’ar Al-Qur’ani kuma babban malamin nan da ke karantarwa a Masallacin Annabi da ke Madina, Sheikh Bashir bin Ahmed Siddiq, ya riga mu gidan gaskiya a yau Laraba. Shafin Al-Haramain ya ruwaito cewa Sheikh Bashir ya rasu ne bayan shafe kusan shekaru sittin yana koyar da Al-Qur’ani a Al-Masjid An-Nabawi da...
    A yan kwanaki kin nan kasashen duniya sun fuskanci wani lamari mai jan hankali sosai, wanda ya jaddada hakkin falasdinu na kafa kasarsa mai cin gashin kai,  hakika wannan lamari ya kai kololuwasa inda ya kai ga ranar litinin da ta gabata aka kira wani taro a gegen taron majalisar dinkin duniya karo na 80...
    Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar yan jarida da bata da iyaka a karon na biyar ta shigar da kara a babban kotun duniya mai hukumta laifukan yaki ICC kan kisan da HKI take yi wa yan jaridu a bakin aikinsu a yankin gaza. A ranar talata ce aka sanar da sake shigar da karar,tun bayan...
    Jakadan Iran na dindin a majalisar dinkin duniya yayi kira da a gaggauta kakabawa HKI takunkumi saboda hujjoji da ake da shi dake tabbatar da cewa tana kisan gillan ne kan alumma Gaza, kuma yayi tir da matsayin kasashen turai game da abin da ke faruwa a yankin gaza. A baya bayan nan kwamitin bincike...
    A jiya 30 ga watan Satumba, firaministan kasar Sin Li Qiang ya mika sakon taya murna ga Safi Kharib bisa zama sabon firaministan kasar Algeria. Li Qiang ya bayyana cewa, Sin da Algeria sun sada zumunta mai zurfi da juna. A cikin shekaru 67 da kulla dangantakar diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu, an raya dangantakarsu...
    Kwamitin Shura na Jihar Kano, ya ta dakatar da Malam Lawan Shuaibu Triumph daga yin wa’azi har zuwa lokacin da za a kammala bincike kan zarginsa da yin ɓatanci ga Annabi Muhammad (S.A.W). Sakataren kwamitin, Alhaji Shehu Wada Sagagi ne, ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a yau Laraba. PENGASSAN ta...
    Kwamitin Shura na Jihar Kano, ya ta dakatar da Malam Lawan Shuaibu Triumph daga yin wa’azi har zuwa lokacin da za a kammala bincike kan zarginsa da yin ɓatanci ga Annabi Muhammad (S.A.W). Sakataren kwamitin, Alhaji Shehu Wada Sagagi ne, ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a yau Laraba. PENGASSAN ta...
    Kwamitin Shura na Jihar Kano, ya ta dakatar da Malam Lawan Shuaibu Triumph daga y’in wa’azi har zuwa lokacin da za a kammala bincike kan zarginsa da yin ɓatanci ga Annabi Muhammad (S.A.W). Sakataren kwamitin, Alhaji Shehu Wada Sagagi ne, ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a yau Laraba. PENGASSAN ta...
    Gwamnatin Jihar Kogi ta bayyana alhininta game da rasuwar aƙalla mutum 26 waɗanda hatsarin jirgin ruwa ya rutsa da su. Mutanen sun fito ne daga Ƙaramar Hukumar Ibaji, kuma suna kan hanyarsu ta zuwa kasuwar Ilushi a Jihar Edo. Jihar Gombe ta fara aiwatar da dokar hana kiwo da daddare Gwamna Abba ya bukaci Tinubu...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Argchi ya bayyana a jiya Talata kan cewa yana dab da fara tattaunawa ta karshe dangane da shirin Snapback wanda ya maida takunkuman tattalin arziki na MDD kan kasar bayan daukewa na shekaru 10. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Aragchi yana fadar haka a birnin...
    Babban hafsan sojojin kasar Iran Manjo Janar Abdurrahim Musawi yay aba da shirin sojojin ruwan kasar na fuskantar duk wani harin da makiya zasu kawowa kasar daga yanzun, Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Janar Musawi yana fadar haka a jiya Talata a lokacinda ya kai ziyarar aiki a sansanin sojojin ruwa...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa aiwatar da yarjeniya ta musamman da kasar china a halin da ake ciki a yankin da kuma yadda duniya take sauyawa da sauri ya zama wajibi ga kasar Iran. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a lokacin da yake gabatar...
    Tawagar jiragen ruwan ‘Usturah’ masu rajin karya kofar ragon da aka yiwa Gaza, sun bada labarin cewa sojojin ruwa na HKI sun kai masu hare-hare a safiyar yau Laraba. Tashar talabijin ta Al-mayadeen ta bayyana cewa, majiyar ta bayyana cewa al-amarin akwai hatsari amma duk da haka zasu ci gaba da hanyarsu ta zuwa Gaza,...
    Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bukaci Shugaban Kasa Bola Tinubu ya cire Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar, Ibrahim Adamu Bakori, saboda yadda ya siyasantar da aikinsa. Kiran na zuwa ne bayan kwamishinan tare da ilahirin dakarun rundunar a jihar sun kaurace wa halartar bikin tunawa da ranar samun ’yancin kai da aka...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shekara guda bayan shahadar Sayyed Hassan Nasrallah, yanayin siyasa da zamantakewar yankin ya sake yin tasiri da tunawa da shi. Nan da nan kuma shahadarsa ta zama wani muhimmin batu na samun hadin kai a tsakanin kungiyoyi masu adawa da mamaya da kuma sabunta himma ga manufofin tsayin daka. Sayyid Hassan Nasrallah, babban sakataren kungiyar...
    Tsohon shugaban hukumar makamashin Nukiliya  ta kasa da kasa,Muhammmad El-Baradei ya ce, Shirin na Trump akan Gaza ba komai ba ne sai kokarin tilasta larabawa su mika wuya, su kuma rusuna. Muhammad El-Baradei ya wallafa a shafinsa na X cewa; na saurari taron manema labaru a fadar White House akan Gaza, amma na fada cikin...
    Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya fada a jiya Talata cewa ya bayar da umarnin aikewa da jiragen ruwa masu ninkaya a karkashin ruwa dake dauke da makaman Nukiliya da su karaci gabar ruwan kasar Rasha, a matsayin kandagarko. Trump ya kara da cewa; A cikin kwanakin bayan an aiko mana sakon barazana daga Rasha,...
    Kungiyoyin gwgawarmaya na Hamas da Jihadul-Islami sun sanar da kai  hari akan sojojin HKI da suke yin kutse a cikin yankin Gaza’ Rundunonin soja na  “Al-Kassam” na Hamas da ‘Sarayal-Qudus” na Jihadul-Islami sun ce sun kai hare-haren ne akan sojojin mamayar da su ka shiga cikin yankunan Arewa da kudancin Gaza. A jiya Talata dakarun...
    Sojojin na Yemen sun sanar da kai hari wani jirgin ruwa mai suna: MINERVAGRACHT’ saboda ya keta dokar hana zuwa tasoshin jiragen ruwan Falasdinu dake karkashin mamaya. Janar Yahya Sari ne ya yi wannan sanarwa yana mai kara da cewa; An kai harin ne akan ruwan tekun Aden ta hanyar amfani da wani makami mai...
    Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya yaba wa ’yan Najeriya bisa abin da ya kira ‘hakurinsu, juriya da kwazo’ duk da tsananin matsin tattalin arziki da rashin tsaro da suke fama da shi. A cikin sakonsa na murnar cikar Najeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai da ya aike ga ’yan kasa, Atiku ya...
    Wata kotu a Jihar Florida da ke ƙasar Amurka ta aike da wani mutum Craig Vogt mai shekaru 61 gidan waƙafi, bayan samunsa da laifin yanka tsuntsayen Dawisu guda biyu, sannan ya yi dabge da naman su. Hukumomin Hudson, wani yanki da ke Florida, sun cafke mutumin ne bayan an samu rahoton abin da ya...
    Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya jinjina wa ’yan Najeriya bisa abin da ya kira “juriya, haƙuri da ƙarfin halin da suke nunawa duk da matsin tattalin arziki da matsalolin tsaro” da ƙasar ke fuskanta.  A cikin saƙonsa na taya ’yan Nijeriya murnar zagayowar ranar samun ’yancin kai da ƙasar ta yi shekaru 65...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga daukacin jama’ar kasar Sin da su yi aiki tukuru, tare da ingiza wanzar da zamanantarwa irin ta Sin. Xi, wanda kuma shi ne sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban hukumar zartarwar rundunar sojojin Sin, ya yi kiran ne yayin taron bikin cika shekaru 76 da kafuwar...
    Gwamnatin Jihar Gombe ta ƙaddamar da wani shiri na rajistar yara kyauta domin rage adadin waɗanda ke zaune gida ba tare da zuwa makaranta ba. Bincike ya nuna cewa fiye da yara 787,000 ne ba sa zuwa makaranta a faɗin jihar, wanda hakan ya sanya gwamnatin ta tashi tsaye wajen kawo sauyi a ɓangaren ilimi....
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa; Iran zata iya taka muhimmiyar rawa wajen gina duniya da ba ta da tashin hankali Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Iran a yau, kamar irin abubuwan da ta faru a baya, za ta iya taka muhimmiyar rawa wajen gina duniya da ba ta da tashin hankali,...
    Mataimakin shugaban kasar Iran ya bayyana cewa; Yakin kwanaki 12 da aka kaddamar kan Iran, gwaji ne na karfinta a fagen kimiyya da fasaha Mataimakin shugaban kasar Iran na farko Mohammad Reza Arif ya bayyana cewa: Wani bangare na ci gaban Iran a fannin kimiyya da fasaha na da nasaba da mayar da takunkuman da...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: An yi musayar saƙo kai tsaye da kuma ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka Ministan harlolin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: Sakamakon wuce gona da iri da bukatun Amurka da kasashen Turai suke da su, ya sa an kasa cimma matsaya...
    Mai ba da shawara ga Jagoran juyin juya halin Musulunci Janar Safawi ya bayyana cewa: An kashe matukan jirgin saman yakin Isra’ila 16 a harin da aka kaddamar kan Iran Mai ba da shawara ga Jagoran juyin juya halin Musulunci Manjo Janar Yahya Rahim Safawi ya sanar da cewa: Iran ta harba makamai masu linzami...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta ce kawo yanzu bata samu ba ta samu rubutaccen shirin zaman lafiya na shugaban Amurka Donald Trump kan Gaza ba. Mahmoud Mardawi wani babban jami’in kungiyar ta Hamas ya bayyana cewa har yanzu kungiyar ba ta samu daftarin shirin, wanda kafofin yada labaran Amurka suka wallafa bayanansa. Amma ya...
    Jami’an Isra’ila da dama da suka hada da Ministoci masu tsattsauran ra’ayi irin su Itamar Ben-Gvir da Bezalel Smotrich, sun soki Firaminista Benjamin Netanyahu kan neman gafarar Qatar bayan harin da gwamnatin Tel Aviv ta kai kan shugabannin Hamas a kasar a ranar 9 ga watan Satumba. Netanyahu ya nemi uzurin ne a wata ganawa...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya soki Amurka da kasashen Turai nan uku na (E3) kan haifar da koma baya a yarjejeniyar nukiliyar 2015 ta hanyar mayar da takunkumin Majalisar Dinkin Duniya kan Iran. Mista Araghchi ya yi wadannan kalamai ne, yayin ganawa da babban sakataren MDD Antonio Guterres, Ya kira sake sanya takunkumin...
    Shugaban kasar Madagaska Andry Rajoelina ya sanar da korar daukacin mambobin gwamnatinsa biyo bayan mummunar zanga-zangar da aka shafe kwanaki ana yi a kasar. A wani jawabi da ya yi na tsawon mintuna 17, ranar Litini, , Andry Rajoelina ya sanar da cewa ya ji kiran matasa tare da korar firaministansa da gwamnatinsa. Ya fara...
    Gwamnatin tarayya ta soke bikin faretin da aka shirya gudanarwa domin murnar cikar Najeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai a ranar Laraba, 1 ga watan Oktoba. Wannan sanarwar ta fito ne a ranar Litinin daga Ofishin sakataren gwamnatin tarayya. “Soke faretin bikin ƴancin kai da gwamnati ta shirya gudanarwa a ranar Laraba, 1 ga...
    Ƙungiyar manyan ma’aikatan kamfanonin iskar gas da fetur PENGASSAN ta ce tana nan kan bakarta na ci gaba da yajin aiki bayan kasa samun maslaha tsakaninta da matatar Dangote. Bangarorin biyu sun tashi baran-baran a tattaunawar da suka yi karkashin jagorancin ministan kwadago na Najeriya Mohammed Dingyadi a ranar Litinin. A ranar Litinin ne ƙungiyar...
    Gwamnatin Tarayya ta sanar da gobe Laraba a matsayin ranar hutu a ƙasar somin bikin cikar ƙasar shekara 65 da samun ƴancin kai. Cikin wata sanarwa da ministan cikin gida na ƙasar, Olibunmi Tunji-Oja ya fitar, ya taya ƴan Najeriya murnar cimma wannan ”babban matsayi”. Ministan ya kuma buƙaci ƴanƙasar su ci gaba da nuna...
    Shugaban hukumar kula da fice ta kasa iran frud askari ya bayyana cewa yawan adadin huldar kasuwancin na kasashen waje na kasar iran yana ci gaba da gudana tsakaninta da fiye da kasashen duniya 100. Kuma yawansa ya kai dala biliyan 54.311a cikin wata shidan farko na wannan shakarar. Da yake hira da manema labarai...
    Babban mai ba da shawara kan harkokin soji ga Imam Khamenei ya bayar da rahoton cewa, a kalla matukan jirgi 16 na sojojin gwamnatin sahyoniyawan ne aka kashe sakamakon harin makami mai linzami da Iran ta kai a yakin kwanaki 12. Babban mai baiwa Jagoran juyin juya halin Musulunci shawara kan harkokin soji Manjo Janar...
    Shugaban Amurka Donald Trump ya fada a wani taron manema labarai na hadin gwiwa tare da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a fadar White House jiya litinin cewa, yana fatan samun zaman lafiya mai dorewa a yankin gabas ta tsakiya. Trump ya sanar da kaddamar da abin da ya kira “Ka’idojin Zaman Lafiya” a hukumance, tare...
    A ranar Talatar nan ake sa ran ci gaba da tattaunawa tsakanin Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Man Fetur (PENGASSAN) da Kamfanin Matatar Man na Ɗangote kan taƙaddamar da ke tsakaninsu. Ana sa ran za a ci gaba da zaman sulhun, wanda Gwamnatin Tarayya ta kira domin sasanta ɓangarorin ne zuwa da yamma. Hakan ta faru ne...
    Fira Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ba wa Gwamnatin ƙasar Qatar haƙuri kan harin da ƙasarsa ta kai a birnin Doha, wanda ya yi ajalin wani jami’in tsaron Qatar. Netanyahu ya bayar da haƙuri ne a yayin wata tattaunawa da shugaban Amurka, Donald Trump ya shirya tsakaninsu da Fira Ministan Qatar, Mohammed Al-Thani. A saƙon...