2025-09-18@03:45:32 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2145

«Hukumar Yaki da Cutuka Masu Yaduwa NCDC»:

    A cewarsa, kudaden fansa da ake yawan ji ana biya yawanci iyalan wadanda abin ya shafa ko al’ummarsu ne ke tarawa.   Ya kuma bayyana cewa rahotanni sun nuna ’yan bindiga sun karɓi sama da Naira biliyan 2.5 a shekarar 2025 kadai, adadin da ya ce babu wata gwamnati da za ta iya ɗauka.  ...
    A yau Laraba kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum, inda ya bayyana cewa, kasar Sin ta soki lamirin harin da aka kaddamar a birnin Doha, fadar mulkin kasar Qatar a jiya Talata, tana kuma adawa da matakin Isra’ila na cin zarafin ikon mulkin...
    Zanga-zangar matasa a Nepal, da aka ƙirƙira a matsayin “Gen Z Revolution,” ta ɓarke ne da nufin ƙalubalantar rashawa da takunkumin amfani da kafofin sada zumunta, sai dai ta rikiɗe zuwa tarzoma mai muni. Rahotanni sun bayyana cewa, an fara zanga‑zangar ne sakamakon hana amfani da manyan kafafen sada zumunta guda 26, ciki har da...
    Haka zalika, Ministan Ilimi, Dakta Olatunji Alausa , shi ma ya jinjinawa rawar da Gwamna Sani ya taka wajen sauƙaƙa bikin kaddamar da Cibiyar Horar da Sana’o’i da Kwarewa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gudanar, yana mai cewa yanzu haka ana sake fasalin makarantun fasaha na ƙasa baki ɗaya domin su mai da hankali...
    Rabi Laxmi Chitrakar, matar tsohon Firaministan Nepal, Jhalanath Khanal, ta rasu bayan masu zanga-zanga sun banka wa gidansu wuta a unguwar Dallu da ke birnin Kathmandu a ranar Talata. Bayanai sun ce masu zanga-zanga a ƙasar mai tsaunuka da ke fama da tashin hankali mafi muni cikin shekaru da dama sun tarfa matar tsohon firaministan...
    Jiragen yakin HKI sun kai sabbin hare-hare kan kasar Yemen a yau Laraba, inji tashar talabijin ta Al-Masirah na gwamnatin kasar. Labarin ya kara da cewa yahudawan sun kai hare-haren ne a tsakanin wasu duwatsu a cikin kasar, da kuma kan cibiyar kungiyar Ansarullah da ke tsakiyar birnin San’a babban birnin kasar, da kuma ma’aikatar...
    Bisa amincewar majalisar gudanarwar kasar Sin, gwamnatin kasar za ta kafa yankin kare muhallin halittu na Huangyan Dao. Tuni dai aka fitar da sanarwar amincewa da hakan a shafin yanar gizo na gwamnatin tsakiyar kasar Sin, wato www.gov.cn a Larabar nan, bayan da ma’aikatar kare albarkatun kasa ta gabatar da bukatar hakan. Sanarwar amincewa da...
    Yayin da aka gano gawar Surajo a ranar Litinin, an gano gawar Fatima washegari, Talata. Sai dai har yanzu ba a gano gawar kanwar Fatima ‘yar shekara uku, Haneefa ba.   A lokacin da lamarin ya faru, Fatima tana goye da kanwarta Haneefa mai shekaru uku a duniya.   Su biyun suna dawowa ne daga...
    Jagoran jam’iyyar NNPP na kasa kuma dan takararta na shugaban kasa a 2023, Rabiu Kwankwaso, a ranar Talata ya gana da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a jihar Kuros Ribas domin tsara dabarun tunkarar babban zabe na 2027. Da yake jawabi a babban birnin jihar, Kalaba, Kwankwaso ya bukaci ‘ya’yan jam’iyyar da su ba...
    “Wannan matakin ya zama dole don dakatar da saran gandun daji, kare muhalli, da tabbatar da ɗorewar albarkatun ƙasa,” in ji Dokta Hashim.   Ya yi gargaɗin cewa, duk wanda ya karya doka zai fuskanci hukunci mai tsauri. “Za a tsaurara doka, tare da biyan tarar ₦500,000 da kuma yiwuwar ɗauri a gidan yari saboda...
    Onuh ta ce, “Ba zai yi wu ba, mu bar ayyukanmu, da yawa daga cikinmu sun yanke hutun da suke kai, muka taho daga Legas saboda wannan zama amma Ministan ya yi watsi da kiran majalisar.   “An jefa ‘yan’uwanmu cikin hatsari, wannan ba abun wasa ba ne, don haka mun dakatar da taron kuma...
    Martanin farko da gwamnatin Siriya ta fitar game da hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suka kai a Homs, Latakia da Palmyra Ma’aikatar harkokin wajen kasar Siriya ta yi kakkausar suka tare da Allah wadai kan hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wasu wurare a yankunan Homs, Latakia da Palmyra, lamarin da ya saba...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Oyo ta sanar da ceto wani ɗan ƙasar Masar da wasu da ba a san ko su wane ba suka yi garkuwa da shi. Kakakin rundunar, CSP Adewale Osifeso, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Talatar nan a Ibadan, babban birnin jihar. DSS...
    Yayin da ake gab da yin bikin ranar malamai ta kasar Sin karo na 41 nan ba da jimawa ba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da martanin wasika ga wakilan malamai na musamman a duk fadin kasar, inda ya bayyana fatansa tare da mika gaisuwar ranar ga malamai da ma’aikata a bangaren ilmi...
    Gwamnan Sakkwato, Dakta Ahmad Aliyu, ya buƙaci jami’an tsaro da su riƙa ɗaukar duk wani infoma da ke bayar da bayani ga ’yan bindiga a matsayin abu ɗaya da babu wani bambanci a tsakaninsu. Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyara ƙananan hukumomin Wurno da Rabah a ranar Litinin da ta...
    Ya ce: “A Zamfara an kashe ‘yan ta’adda 30 a hare-haren sama da kasa, yayin da masu tada kayar baya 76 da suka hada da mata da kananan yara suka mika wuya ga jami’an tsaro.   “Rundunar ‘yansanda ta bayar da rahoton kama mutane 1,950 da ke da alaka da munanan laifuka, garkuwa da mutane,...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’ila Baghaei ya bayyana cewa dangantakar Iran da hukumar IAEA zai sauya saboda hare-haren da HKI ta kaiwa cibiyoyin makamashi nukliya na kasar iran a cikin watan yunin da ya gabata. Tashar talabijan ta Presstv a nan tehran ta nakalto Baghaei yana fadar haka a yau litinin ya kuma...
    Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da jami’an Hukumar Kula da Man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA), wakilan kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC, shuwagabannin kamfanin ‘MRS Holdings Limited’ da kuma kungiyar ‘yan kasuwa ta kasa (TUC).   Da yake bayyana bude taron, Minista Dingyadi ya jaddada aniyar gwamnati na sulhu a tsakanin kungiyar da masu...
      Ya bayyana karya ka’idojin da aka shimfiɗa kan amso basussukan a matsayin “babban abin damuwa da fargaba kan ɗorewar tattalin arzikin kasar,” yana mai jaddada cewa, akwai buƙatar samar da “sabbin tsaruka masu ƙarfi, da za su daidaita hanyoyin karɓar rance na gaskiya, da kuma ƙuduri na bai ɗaya don tabbatar da cewa, duk...
    “Don haka, Ma’aikatar Yaɗa Labarai tana aiki kafada da kafada da Ma’aikatar Harkokin Ƙananan Hukumomi, Hukumar Harkokin Addinai, tare da haɗin gwiwar manyan shugabannin gargajiya da na addini, domin tabbatar da cewa wayar da kai da kuma tura saƙon rajista ya isa kowace mazaba, ƙauye, da unguwa a fadin Jihar Kaduna,” in ji Maiyaki.  ...
    Sayyid Abbas Araqci ministan harkokin wajen kasar iran a wani sakon mayar da martani da ya aike da shi game da shirun da kasashen turai suka yi kan fadada shirin nukiliyar HKI ya jaddada cewa yin shiru da baki da suka yi ya nuna cewa yanzu basu da wata dama ko kwarin guiwar yin Magana...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada yin kira ga al’ummar Musulmi cewa: Wajibi ne kasashen musulmi su yanke alakarsu da ‘yan sahayoniyya Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa: Dole ne kasashen musulmi su yanke duk wata huldar kasuwanci da siyasa da gwamnatin ‘yan sahayoniyya azzaluma tare da mayar...
    Yayin da makarantu a fadin Najeriya ke dawowa sabuwar zangon karatu ta shekarar 2025/2026 a yau Litinin, iyaye sun koka kan mummunar ƙalubalen tattalin arziki da ke hana su samun sauƙin biyan kuɗin makaranta da sauran kayayyakin karatu. Rahotanni daga jihohi daban-daban sun nuna yadda tsadar rayuwa da hauhawar farashin kaya suka zame wa iyaye...
    Jimilar kudin asusun ajiya na kasar Sin a ketare ya kai dala triliyan 3.3222 zuwa karshen watan Agusta, inda ya karu da dala biliyan 29.9 ko kaso 0.91, idan aka kwatanta da na karshen watan Yuli. Hukumar kula da musayar kudi ta kasar Sin ta alakanta karuwar da tasirin sauyin kudi da sauyin farashin kadarori....
    Aƙalla mutum bakwai ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu 11 suka jikkata a wani sabon hari da ’yan bindiga suka kai ƙauyen Wake da ke gundumar Agunu, a Ƙaramar Hukumar Kachia ta Jihar Kaduna. Hari  ya faru ne da misalin ƙarfe 5:55 na safiyar ranar Lahadi, lokacin da ’yan bindigar suka mamaye garin, inda...
    Ministan yakin HKI Israel Kazt ya bayyana cewa sun yi kokarin kashe jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae a yakin kwanaki 12 amma bayanan da suke da shi ya kasa kaiwa ga manufarsu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa wannan shi ne karon farko wanda HKI take tabbatar...
    Na dauki fim sana’a, kuma sana’ar ce. Dan wallahi sana’a ce me kyau ma, ta ba ni gida, ta ba ni mota, na ci, na koshi. Yanzu idan zan shekara na ce ba zan fita ba, a cikin gidana ne, kuma darajar Kannywood. Ina finafinai na a haka na samu gidana, na gina gidan kuma...
    Kazalika, an amince da amincewar ne a taron majalisar zartarwa na jihar karo na 12, wanda Gwamna Malam Dikko Umaru Radda, ya jagoranta a gidan gwamnati da ke Katsina. Da yake karin haske ga manema labarai bayan taron, kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin gida, Dakta Nasiru Mu’azu Danmusa ya ce, an sanar da matakin...
    A jawabin da ya yi wa shugabannin sashen sintiri, jami’an ‘yansandan motoci, da sauran jami’an da ke aiki a hedikwatar rundunar, CP ya ce halayen jami’an sintiri a fili suke bayyana hoton da al’umma ke da shi game da rundunar ‘yansanda. Adeh ta bayyana cewa CP ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda jami’ai ke...
    ’Yan ta’adda sun kashe aƙalla mutum 63 a wani mummunan hari da suka kai a garin Darul Jamal, kusa da kan iyakar Najeriya da Kamaru, a yankin Bama na Jihar Borno. Gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum, ya tabbatar da cewa daga cikin waɗanda suka rasa rayuka akwai sojoji 5 tare da fararen hula 58. Tsagin...
    Kwamandan Sojojin Iran ya jaddada cewa: Dole ne a ko da yaushe Iran ta kasance a shirye don yin yaki Babban kwamandan sojojin kasar Iran ya jaddada wajibcin kasancewa cikin shiri a ko da yaushe domin yaki, yana mai cewa: A yau sun fahimci yaki da gaba da kuma makircin makiya daidai da yadda suke...
    Ƙungiyoyin Musulmi maza da mata da ƙananan yara daga sassa daban-daban na Jihar Oyo sun gudanar da bukukuwan zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta, Manzon Allah Annabi Muhammad (SAW), na bana (shekara ta 1447 bayan hijira). Aminiya ta ruwaito cewa an fara gudanar da bukukuwan ne a ranar Asabar daga harabar babban Masallacin Unguwar Sabo, mazaunin...
    A jiya Jumma’a 5 ga wannan wata, babban taron MDD karo na 79 ya jefa kuri’a tare da zartas da kudurin hadin gwiwar dake tsakanin MDD da kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai wato SCO da kasar Sin da dukkan kasashe membobin kungiyar SCO kimanin 40 suka gabatar tare. Kudurin ya amince da muhimmiyar rawar da...
    Rahotanni sun tabbatar da cewa ’yan bindiga sun kashe mutane bakwai, yayin wani hari da suka kai ƙauyen Magajin Wando da ke Ƙaramar Hukumar Ɗandume, a Jihar Katsina. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na daren ranar Juma’a, lokacin da maharan suka afka wa ƙauyen. Mauludi: Ƙungiyoyin addini sun nemi gwamnati ta sassauta...
    Rahotanni sun tabbatar da cewa ’yan bindiga bakwai sun mutu a wani hari da suka kai ƙauyen Magajin Wando da ke Ƙaramar Hukumar Ɗandume, a Jihar Katsina. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na daren ranar Juma’a, lokacin da maharan suka afka wa ƙauyen. Mauludi: Ƙungiyoyin addini sun nemi gwamnati ta sassauta dokar...
    An ce saurayin ya yi wa Ammaye wasa da cewa yana son aurenta domin “cika Sunnah”. Sai dai kuma an ce Ammaye ta yi wata magana da aka dauka a matsayin Batanci. Wannan ne ya fusata matasan yankin. Lamarin aka kai shi fadar Dagacin Kasuwar Garba, inda aka yi mata tambayoyi, kuma a cewar rahoto...
    Ƙaramar hukumar Tureta na fama da matsalar tsaro, inda hare-haren ‘yan bindiga ke yawan faruwa, inda suke kashe mutane. A baya, ɗaruruwan mazauna yankin sun yi zanga-zanga suna neman gwamnati ta kawo musu ɗauki. Matasa kuma sun yi barazanar ɗaukar makamai domin kare kansu idan gwamnati ta gaza samar da tsaro. Daga kanmu, magana...
    Mambobin kwamitin zartarwar na ADC da suka hada da Bolaji Abdullahi (Sakataren yada labarai na kasa), Babachir Lawal (Mataimakin shugaban jam’iyyar na yankin arewa maso gabas), Usani Uguru Usani (Mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa), Farfesa Oserheimen Osunbor (Babban lauyan jam’iyyar na kasa), Bar Chinedu Idigbo (Sakataren shirye-shiryen jam’iyyar na kasa), Sen. Musa Elayo (Mataimakin shugaban...
    Fira Ministan gwamnatin kasar Senegal ya nemi afuwar rashin amsa gayyatarsa ​​ta farko a hukumance zuwa Faransa Fira ministan Senegal Ousmane Sonko ya nemi afuwar rashin amsa gayyata a matsayin babban bako a zaman taron bugu na 11 na BPI France Generation Innovation Forum, wanda aka shirya gudanarwa ranar 23 ga watan Satumba a birnin...
      “Kowace ranar 12 ga watan Rabi’ul Auwal rana ce ta murnar zagayowar ranar haihuwar Manzonmu mai albarka (SAW).   “Wannan lokaci ne mai kyau da ya kamata dukkan Musulmi su yi koyi da rayuwar Manzon Allah (SAW).   “Musulunci ba addini kawai ba ne, hanya ce ta rayuwa, rayuwar Annabi (SAW), ta shiryar da...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “Haka nan, ‘yan bindigan, suna sake kawo wani harin a wannan gari namu na Galadi da misalign karfe 10:15 na daren ranar Laraba, inda suka kewaye baki-dayan Galadin; illa bangare guda shi ma saboda gulbi ya tare wannan gefen ne, inda suka bude wa Galadin wuta ta kowane gefe baki-daya,” in ji shi. Kazalika ya...
    Wanda aka kama sunansa iro Garba mai shekaru 25 daga Zangwaye Fulani a ƙaramar hukumar Ajingi a Jihar Kano. Ya amsa cewa shi da wasu mutane huɗu sun yi garkuwa da mutane a Kano, Jigawa da Bauchi. An kuma samu rigunan sojoji guda uku a hannunsa. Kwamishinan ya ce ana ci gaba da ƙoƙarin kama...
    Fadar gwamnatin Amurka ta White House ta ce a yau Juma’a, shugaba Amurka Donal Trump zai rattaba hannu kan wata doka da za ta sauya sunan ma’aikatar tsaron kasar zuwa ma’aikatar yaki. Canjin suna na dindindin na buƙatar Izinin majalisa, to amma umarnin zartarwa da shugaban zai sa wa hannu, zai ba da damar amfani...
    Yakin ya farkar da Sin da duniya baki daya, wanda ya zama tushen kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin a shekarar 1949, daga bisani kuma ya dora kasar bisa tafarkin zamani. Ga duniya, mulkin mallaka ya fara wargajewa. Kasashe da dama sannu a hankali suka fahimci cewa, in sun jajirce, za su samu ‘yancin kai. Tasirin...
    Karamar karamar hukumar Jibiya ita ce ta fara shirya taro domin yin sulhu da ‘yan bindigar, sai dai kuma ba a ga wakilin gwamnatin Jihar Katsina a wannan sulhu ba, amma dai an ga shugaban karamar hukumar da sauran jami’an tsaro da ake zargin daga Abuja suke halartar irin wannan taro. An yi wannan sulhu...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta sake jaddada haramcin hawa babura daga ƙarfe 7 na dare zuwa 6 na safe, a wani mataki na tsaurara tsaro yayin bikin Mauludi a jihar. Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP Bello Yahaya, ya bayyana cewa dokar na da muhimmanci domin hana aikata...
    “Tun lokacin Buhari har zuwa yanzu lokacin Tinubu, ‘yan Nijeriya na cikin wahala. Talauci tana nan a ko’ina, matasa ba su da aikin yi, kuma tattalin arziki yana lalacewa. Su na cewa suna yaki don Nijeriya, amma a zahirin gaskiya, suna yaki ne kawai don kansu da aljihunsu.   “Na kasance cikin gwagwarmaya tun daga...
    Da yake ganawa da ‘yan jarida a ranar Litinin, tsohon shugaban kungiyar masu tsara gidaje a Nijeriya, Aliyu Wammako, ya ce, rashin biyan ‘yan kwangila kudadensu na shafan tattalin arziki sosai. Ya bukaci gwamnatin tarayya da ka da ta tsaya bata wani lokaci ta kama biyan ‘yan kwangila kudadensu da hakan zGwamnatin tarayyar Nijeriya ta...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Argchi ya gana da jami’a mi kula da al-amuran harkokin wajen na tarayyar Turai Kaja Kallas a birnin Doha na kasar Qatar a jiya Alhamis. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa, jami’an guda biyu sun tattauna inda aka kwana dangane da shirin nukliyar kasar Iran...