2025-11-03@12:40:35 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2563

«Hukumar Yaki da Cutuka Masu Yaduwa NCDC»:

    Akalla mutane 11 ne aka kashe a harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a unguwannin Kagara da San-Isa da ke karamar hukumar Kaura-Namoda a jihar Zamfara. Majiyoyi daga yankunan biyu sun shaida wa wakilinmu cewa an kai hare-haren ne a unguwannin Kagara da San-Isa tare da wasu kauyukan da ke kewaye. Waɗanne Ƙasashe Ne...
    Gwamna Mohammed Umar Bago na jihar Neja ya bayar da umarnin bude jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida Lapai domin fara gudanar da karatu na yau da kullun.   Umurnin sake bude jami’ar ya biyo bayan nazari sosai kan matakan tsaro da inganta ababen more rayuwa a jami’ar.   Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa...
    Gwamnatin Jihar Kano ta sake tabbatar da kudurinta na yaki da zaizayar ƙasa, ambaliyar ruwa, da sauran matsalolin da suka shafi muhalli. Wannan bayani ya fito ne daga Gwamna Abba Kabir Yusuf yayin kaddamar da babban shirin dashen itatuwa da za a shuka tsirrai miliyan biyar da rabi a faɗin jihar, wanda aka gudanar a...
    Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya bukaci sabbin mambobin hukumar yi wa kasa hidima (NYSC) da aka rantsar da su kasance masu kishin kasa da kuma ci gaba da zama ’yan kasa nagari.   Gwamna AbdulRazaq ya bayyana haka ne a yayin bikin rantsar da rukunin ‘B’, a sansanin NYSC dake Yikpata a karamar hukumar...
    Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Gusau/Tsafe ta tarayya Kabiru Amadu (wanda aka fi sani da Mai Palace) ya shirya taron addu’a na musamman ga jihar Zamfara da Najeriya baki daya, domin neman zaman lafiya da cigaba mai dorewa.   Taron addu’o’in wanda ya gudana a babban masallacin Juma’a na Tudun Wada da ke Gusau,...
    Gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ya bayyana jin dadinsa kan aikin titin Eiyenkorin zuwa Afon Ojoku zuwa Offa zuwa Odo zuwa Otin mai tsawon kilomita 49 da ake ginawa.   Titin siminti na daya daga cikin manyan tituna hudu da ake ba da tallafi a jihar Kwara a karkashin shirin gwamnatin tarayya na karbar haraji...
    Gwamnatin jihar Kano ta jaddada kudirinta na yaki da gurbacewar kasa, zaizayar kasa da sauran kalubalen muhalli.     Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne a yayin bikin kaddamar da wani katafaren shirin dashen itatuwa, inda za a dasa itatuwa miliyan 5 da rabi a fadin jihar, wanda aka gudanar a karamar hukumar...
    A cewar sanarwar, AIHS za ta taimaka wajen haɓaka tambarin dangote da haɓaka dabarun haɗin gwiwa tare da masu ruwa da tsaki. Kodinetan shirin Barista Festus Adebayo ya shaida wa manema labarai cewa, za a iya cike giɓin gidaje a ƙasar ta hanyar haɗin gwiwar Haɗin kan Jama’a masu zaman kansu (PPP). Ya ce: “Kwarewa...
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da babban shirin dashen bishiyoyi miliyan biyar a shekarar 2025. An fara dashen ne yankin Yanbawa da ke Ƙaramar Hukumar Makoda. Sake zaɓen Tinubu zai lalata makomar Najeriya — El-Rufai  Gwamnan Yobe ya naɗa Gadaka a matsayin sabon Sarkin Gudi Gwamnan ya ce wannan shiri na nufin...
    Mai Martaba Sarkin Dutse, Dr Hameem Nuhu Muhammadu Sunusi ya kaddamar da rabon zakkar kudi ta shekarar musulunci ta 1446 a gundumar Yayari dake Karamar Hukumar Buji. A jawabin sa, Mai Martaba Sarkin ya ja hankalin al’umma da su ci gaba da fitar da hakkin Allah domin samun makoma a nan duniya da kuma gobe...
    Gwamnatin jihar Borno na shirin sake tsugunar da ‘yan gudun hijira kusan 5,000 daga al’ummomin Bama su biyar kafin damina ta kare. Gwamna Babagana Umara Zulum ya bayyana haka a wata ziyarar ban girma da ya kai wa Shehun Bama, Dakta Umar Kyari Umar El-Kanemi a ranar Juma’a. Ministan Yaɗa Labarai Ya Buƙaci A Kwantar...
    Sojojin HKI sun kashe falasdinawa 62 daga safiyar jiya Asabar zuwa lokacin bada wannan labarin a yau Lahadi. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa mafi yawan wadanda aka kashen masu neman abainci ne, a cibiyoyin karban abincin wadanda HKI da Amurka suka kafa. Kafafen yada labarai daga asbitocin Gaza sun bayyana...
    Minista Idris ya bayyana damuwa da irin martanin da al’umma da masu ruwa da tsaki a harkar yaɗa labarai suka nuna dangane da lamarin. Amma ya jaddada cewa hukumar da ke da hurumin dakatar da lasisin gidajen rediyo da talabijin ita ce Hukumar Kula da Gidajen Radiyo da Talabijin ta Ƙasa (NBC), kamar yadda doka...
    Ya danganta mutuwar ta ƙanana da matsakaitan sana’oi a ƙasar, kan rashin samun rancen kudaɗen da za su ci gaba da ka kasuwancin su da rashin kayan aiki, da rashin kasuwa da ba a samu sosai da kuma rashin gudanar da ingantaccen shiri, kafin su fara gudanar da kasuwancinsu. Ya sanar da cewa, ya zama...
    Sai dai tuni masu sanatoci da dama, kamar Sanata Shehu Buba, da Sanata Abdul Ahmad Ningi da ke wakiltar Bauchi ta tsakiya suka ƙaryata labarin da cewa babu gaskiya a cikinsa tare da neman jama’a da su yi watsi da shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun...
    “Kazalika sarkin ya bayyana cewa, mun kuma duba yanayinmu. Me muke da shi? Me za mu iya yi? Me ya kamata mu yi domin inganta rayuwar mutanenmu? Allah ya albarkaci ƙasarmu, ƙasa ce mai faɗi sosai, kuma ta dace da ayyukan noma. Mun kuma yi la’akari da fannin ilimi. Jihar Neja, an san tana gaba...
    Fiye da shekaru goma da suka gabata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya dora samun ci gaba marar gurbata muhalli a matsayin wata muhimmiyar manufar raya kasa. Ya taba fitar da manufar raya kasa ta hanyar bayar da muhimmnci ga “Muhalli”, wadda ta yi nuni da cewa ingantaccen yanayin muhalli abu ne mai matukar daraja don samun...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Suna fatan haɓakar musayar kasuwanci tsakanin Iran da Pakistan ta haura dala biliyan 10 Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bar birnin Tehran a wannan ranar Asabar din zuwa Islamabad na Pakistan a wata ziyarar aiki a kasar bisa gayyatar da fira ministan Pakistan Shehbaz Sharif ya yi masa....
    Jaridar Ma’arif ta Isra’ila ta bayyana cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila na fuskantar daya daga cikin manyan shan kashi a tarihinta Masanin harkokin soji na jaridar Ma’ariv ta Isra’ila Avi Ashkenazi ya amince da cewa: Isra’ila na fuskantar matsala ta gaske bayan shafe kusan watanni 22 ana yakin Gaza, yana mai cewa gazawar tsarin siyasar Isra’ila...
    An yi jana’izar Marigayi Sarkin Gudi da ke Jihar Yobe, Alhaji Isa Bunuwa Madugu Ibn Khaji, ranar Juma’a a Abuja, inda ya rasu a wani asibiti bayan fama da jinya. Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni ya ranar Juma’a ya jagoranci tawagar gwamnatin jihar wajen hakartar taron. Sanarwar da Mamman Mohammad daraktan yada labarai na gwamna...
    Bincike a kan zargin da ake wa Hukumar Raya ƙasashe ta Amurka (USAID) da wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu na cikin gida da na ƙasa da ƙasa game da tallafa wa ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP da sauran masu tayar da ƙayar baya a Nijeriya har yanzu bai kammala ba. Kawo yanzu babu wata ƙwaƙƙwarar...
    Bugu da ƙari, Hukumar ta NPA ta bayyana cewa, tana kan ƙoƙarin inganta kayan aiki Tashoshin Jiragen Ruwan ƙasar, wanda ta zuba dala biliyan daya, domin fara gyaran Tashoshin Jiragen Ruwa ta Tin Can Island tare da yin ayyukan kwakwarima, a Tashoshin Jiragen Ruwa na, Apapa, Riɓers, Onne, Warri da kuma Kalaba. Ita kuwa a...
    Gwamnatin Tarayya ta bayyana aniyar ta na hadin gwiwa da Cibiyar Binciken Cututtuka ta Jihar Kano(KIRCT) a fannonin bincike, samar da rigakafi, habaka magunguna da kuma yaki da cututtuka masu nasaba da zafi (tropical diseases). Darakta Janar na Hukumar Binciken Harkokin Halittu ta Kasa (NBRDA), Farfesa Abdullahi Mustapha ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar...
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana naɗin Saidu Yahya a matsayin sabon Shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafen Jama’a da yaƙi da cin hanci da rashawa (PCACC), bayan ƙarewar wa’adin tsohon shugaban, Barrister Muhuyi Magaji Rimin Gado, a watan Yuni. Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ta...
    Akalla ’yan gudun hijira miliyan daya da dubu 400 da ke Arewa maso gabashin Najeriya ne suke fuskantar barazanar yunwa bayan yanje tallafin da Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ke bayarwa. Wani rahoton majalisar a kan abinci da tsaro wanda gwamnatin Najeriya, Shirin Kula da Abinci na Majalisar (FAO) da sauran masu ruwa da tsaki a...
    Ya nuna rashin jin daɗinsa da rabon ayyukan tituna kamar yadda aka samu a cikin wata sanarwa da ma’aikatar ayyuka ta fitar a watan Mayun 2025, wanda a cewarsa, an ware Naira tiriliyan 1.394 wa yankin Kudu-maso-Yamma, yayin da ɗaukacin yankin Arewa-maso-gabas suka samu Naira biliyan 30, sai kuma yankin Arewa-maso-Yamma Naira 105 biliyan. “Rashin...
    Dangote Ya Bada Shawarar Samar Da Gidaje Masu Rahusa Da ‘Yan Nijeriya Za Su Iya Mallaka Majalisar Dattawa Ta Yi Allah-wadai Da Zanga-zangar Ƙin Jinin ’Yan Nijeriya A Ghana Sai dai, abin dubi a nan shi ne, yadda kusan yanzu a kasar, tabbatar da doka da oda, a cikin kasar, ya koma kachokam, a huunun...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Karin wa’adin aiki da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa Kwanturola Janar na Hukumar Hana Fasa Kwauri ta Kasa, Bashir Adewale Adeniyi na ta shan suka daga mutane daban-daban. Yayin da wasu ke ganin abin da shugaban ya yi da cewa ya dace, wasu kuwa na...
    Gwamna Zulum ya nuna jin dadinsa ga kwamishinonin biyu, tare da yi musu fatan alheri a cikin ayyukansu na gaba.   Sai dai ya sanar da nadin Engr. Mohammed Habib da Ibrahim Hala Hassan domin maye gurbin kwamishinonin biyu da aka sauke.   A halin da ake ciki, Gwamna Zulum ya kuma amince da nadin...
    Fadar Shugaban ƙasa ta bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙarin wa’adin shekara guda ga shugaban hukumar Kwastan ta Nijeriya, Bashir Adewale Adeniyi. Kafin wannan ƙarin wa’adin, aikin Adeniyi zai kare ne a ranar 31 ga Agusta, 2025. Sai dai sanarwar da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya...
    Tsohon ɗan wasan tsakiyar Barcelona, Carles Perez, yana kwance a asibiti a ƙasar Girka bayan da wani kare ya cije shi a al’aurarsa yayin da yake yawo da nasa karen a Thermi, a wata unguwa a Thessaloniki, ranar Talata. Perez, mai shekaru 27, yana ƙoƙarin raba karensa da wani da suke fada lokacin da ya...
    Shugaban kasar Lebanon wanda ya gabatar da jawabi da safiyar yau ya ce; A cikin sakwannin da mu ka aike wa Amurka, mun bukaci ganin an kawo karshen hare-haren da Isra’ila take ci gaba da kawo wa Lebanon, ta sama, kasa da ruwa, haka nan kuma kisan gillar da take yi wa mutane a cikin...
    Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta saki tare da hada wadanda aka yi garkuwa da su talatin da biyar tare da iyalansu.   Sun kunshi mata goma sha shida da yara goma sha tara daga Kagara, Tegina da Agwara, bayan sun shafe makonni a hannun ‘yan sanda da ke tsare da kuma kawar da hankalinsu...
    Masu ruwa da tsakin Arewa sun yaba da kwazon Tinubu, inda suka bukaci a kara karfafa gwiwar ‘yan kasa a taron Kaduna.   Masu ruwa da tsaki a Arewacin Najeriya sun yaba wa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa irin ci gaban da ta samu wajen cika alkawuran zabe, musamman a muhimman batutuwan da suka...
    Hukumar kula da da’ar ma’aikata ta sanar da cewa, a halin yanzu ana iya  bayyana kadarorin ma’aikatan ta hanyar yanar gizo, wani mataki da aka tsara domin saukaka aikin da kuma kara yin lissafi.   Daraktan ofishin na jihar Jigawa Abubakar Bello ne ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci shugaban ma’aikatan jihar Alhaji...
    Ya ce har yanzu matsalar tsaro tana addabar sassan Nijeriya da dama, kuma ana yaudarar shugaban ƙasa game da hakan. Ya ce, “Idan Shugaba Tinubu yana sauraron labarai masu daɗi kawai daga waɗanda ke son faranta masa rai, to yana rayuwa ne a cikin duhu.” Abdullahi ya bayyana cewa al’umma da dama a Nijeriya har...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF) ta zargi Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da kin yin adalci wurin ayyuka da raba mukamai tsakanin Arewa da Kudancin Kasar nan. Wadannan zarge-zarge suka sa fadar Shugaban Kasa ta hannun mai taimaka masa na musamman kan kafofin yada labarai Bayo Onanuga mayar...
    Shugaban kwamitin kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa, Alhaji Aminu Zakari, ya ce kwamatin ya jinkirta rangadin kananan hukumomin jihar 27 a Zango na uku na shekarar 2024 ne a sakamakon zaben kananan hukumomi, don haka akwai bukatar ba su damar gudanar da ayyuka kafin tantance kwazon su.   Alhaji Aminu Zakari ya yi...
    Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da shirin tallafi guda biyu da suka kai fiye da naira miliyan 392, ga membobin kungiyar direbobi ta NURTW da kuma ƴan kungiyar mahauta a jihar Jigawa. Wannan tallafi wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatinsa na inganta rayuwar masu sana’o’in  da ke taka muhimmiyar rawa a rayuwar yau da kullum....
    Wadannan ’yan wasan kwallon kafa na mutum-mutumi sun sake nuna bajintar da kasar Sin ke nunawa a fagen kere-keren mutum-mutumi masu siffar dan’adam da kuma yadda masana’antar bangarensu ke samun ci gaba cikin hanzari a kasar. A watan Agusta mai kamawa ne kasar Sin za ta karbi bakuncin gasar wasannin motsa jiki na mutum-mutumi masu...
    Kakakin majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa kyale HKI wanda kasashen duniya suka yi ne, ya ke bawa HKI karfin giwan ci gaba da abinda take yi a gaza. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin majalisar dokokin kasar ta Iran yana fadar haka a taron shuwagabannin majalisun...
    Kwanan baya, kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin ya shirya taron bita tare da wadanda ba ’yan jam’iyyar ba, dangane da yanayin tattalin arzikin kasar, da kuma ayyukan tattalin arziki da za a aiwatar a rabin shekarar bana ta biyu, domin sauraren ra’ayoyinsu. Xi Jinping, babban sakataren jam’iyyar ne ya shugabanci taron tare da...
    Adamu ya bayar da hujjar cewa, Sarkin Musulmi ne ke shugabantar daular gargajiya mafi girma a Arewacin Nijeriya, tare da dukkan sarakunan yankin karkashin jagorancinsa na ruhi da al’adu.   Ya yaba da shugabancin Sarkin Musulmi Abubakar na tsaka-tsaki, samar da zaman lafiya, da jagoranci na hadin kai.   Sun bayyana shi a matsayin mutum...
    Kakakin ofishi mai lura da harkokin yankin Taiwan a majalisar gudanarwar kasar Sin Chen Binhua, ya ce kalaman da aka jiyo jagoran yankin Taiwan na kasar Sin Lai Ching-te na yi dangane da sakamakon zagayen farko na kuri’ar kiranye da al’ummar Taiwan suka kada, ya nuna rashin gamsuwarsu da salon mulkin jam’iyyar DPP mai mulkin...
      Ministan Ƙasa na Ci Gaban Yankuna, Uba Maigari Ahmadu, ya yaba wa ci gaba da tattaunawa tsakanin jami’an gwamnati da shugabannin arewa yana mai cewa wannan “tattaunawa ce mai tarihi kuma cike da ƙarfi,” yana nuna cewa hangen nesa na Shugaba Bola Tinubu ga Arewa ya fara samo asali kuma yana haifar da sakamako....
    Sanata Aniekan, ya gargaɗi jama’a da su daina yaɗa jita-jita ko bidiyo na ƙarya da ka iya tayar da hankali, tare da yaba wa da ƙoƙarin da ofisoshin jakadancin Nijeriya da Ghana da kuma ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya ke yi wajen warware matsalar. Ya ƙara da cewa: “Zaman lafiya, haɗin kai da girmama juna su...
    Kwamandan, Nigerian Defence Academy NDA, Manjo Janar Abdul Khalifa Ibrahim ya bukaci dalibai da su jajirce wajen ganin sun samu nagartar ilimi. Manjo Janar Abdul Khalifa Ibrahim ya yi wannan kiran ne a yayin bikin yaye dalibai da jawabai da kuma bayar da kyaututtuka da aka yi a Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Malali Kaduna. Kwamandan...
    Sakatariyar kungiyar kasashen yankin Caribeans  ( Caricom) ta bayyana cewa; kasashen yankin suna son ganin bunkasa alakar kasuwanci da abokansu na nahiyar Afirka.  Sakatariyar kuniyar ta kasashen Caribbian ta bayyana hakan ne a lokacin jawabin bude taron karawa juna sani a taron kasuwanci da zuba hannun jari a tsakanin yankin da nahiyar Afirka da aka...
    ’Yan bindiga sun tarwatsa kauyuka sama da 10 da ke zagaye da ƙaramar hukumar Bakori ta jihar Katsina sannan suka mayar da sama da 6,000 ’yan gudun hijira. Maharan dai sun rika kashe mazauna kauyukan sannan su sace wasu su yi garkuwa da su domin karɓan kuɗin fansa. Bayanai na cewa a ’yan kwanakin nan,...
    Gwamnatin jihar Kano tare da hadin gwiwar wata kungiya mai suna Partnership for Agile Governance and Climate Change (PACE) ta kaddamar da manufofinta na sauyin yanayi a hukumance. Wannan manufa mai mahimmanci ta samar da taswirar dabaru don ragewa, daidaitawa, da tsarin tafiyar da yanayi mai hadewa a duk sassan ci gaba a jihar.  ...