2025-11-03@12:40:10 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2563
«Hukumar Yaki da Cutuka Masu Yaduwa NCDC»:
Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Yi Tsokaci Kan Furucin Netanyahu Game Da Kafa “Babbar Kasar Isra’ila’
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya yi tsokaci kan furucin Netanyahu game da kafa ‘Babban Kasar Isra’ila’ Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya bayyana a safiyar yau alhamis cewa: Kafafen yada labaran yammacin duniya a al’ada na zargin duk wanda ya ambaci ra’ayin ‘yan sahayoniyya na kafa “Babban kasar Isra’ila” da kiyayya ga wata...
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya Bayyana cewa: Shugabannin gwamnatin nuna wariyar al’umma suna kokarin yaudarar al’ummar Iran A martaninsa ga fira ministan gwamnatin ‘yan sahayoniyya da ya yi a baya-bayan nan, shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Kasar Iran a yayin da yake gabatar da wasu takardu kan matsalar karancin ruwa da kuma matsalar...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta kama wani matashi mai shekara 18 bisa zargin aikata fashi da makami a jihar. An kama shi ne a garin Kwadon bayan samun sahihin bayani daga jama’a. NDLEA ta lalata gonar tabar wiwi a Gombe ’Yan ci-rani 26 sun nitse a teku suna ƙoƙarin tsallakawa Turai Kakakin ’yan sandan...
Gwamnan ya yi alƙawarin cewa gwamnatin jihar za ta yi aiki tare da hukumomi masu ruwa da tsaki domin hanzarta shari’o’i da kuma rage cunkoson gidan yarin. A lokacin ziyarar, ya lura da cewa yawancin fursunonin na zaune a ƙasa babu katifa. Don inganta rayuwarsu, ya umarci a samar musu da katifu 500. Gwamna Sule...
A yayin ziyarar, Gwamna Lawal ya jajantawa iyalan waɗanda suka rasa ‘yan uwansu tare da tabbatar wa al’ummar yankin ƙudurinsa na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi. A nasa jawabin, gwamnan ya yi kakkausar suka ga hare-haren da ’yan bindiga ke kai wa a baya-bayan nan, yana mai cewa da gangan maƙiya ke nufin...
Tinubu ya yi kira da a sake duba kudaden gudanar da aikin NNPC da ake cire kashi 30 cikin 100 wanda doka ta tanadar a karkashin dokar masana’antar mai. Shugaban ya bayyana godiya ga mambobin majalisar bisa jajircewarsu da aiki tukuru wajen aiwatar da gyare-gyare masu tsauri da wahala wadanda suka dabaibaye ci gaban...
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya miƙa ƙudiri zuwa Majalisar Dokokin Jihar domin neman amincewarta a ƙirƙiri sabbin ƙananan hukumomi 13. Gwamnan, ya bayyana cewa wannan mataki zai taimaka wa gwamnati wajen kusantar al’umma, da ayyukan raya ƙasa. Jama’a sun koka kan rashin kammala aikin titi a Kafanchan Majalisar Kano ta dakatar da ciyaman...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: Lokaci Ya Yi Da Za A Daina Kakaka Takunkumi Da Ba Dace Ba Kan Kasashe
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Lokaci ya yi da za a amince da takunkumin da bai dace ba a matsayin laifi ga bil’adama Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya ce lokaci ya yi da za a amince da takunkumin bai daya da Amurka da kawayenta suka kakaba wa Iran a matsayin wani...
Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da bikin makon shari’a na shekarar 2025 wanda ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA) reshen jihar Jigawa ya shirya, inda ya yi kira da a ƙara ƙarfafa bin ƙa’idojin aikin shari’a da hanzarta gudanar da shari’a a duk fadin jihar. A jawabinsa wajen bikin bude taron a Dutse, Gwamna Namadi ya...
Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: A Lokaci Ya Yi Da Za A Daina Kakaka Takunkumi Da Ba Dace Ba Kan Kasashe
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Lokaci ya yi da za a amince da takunkumin da bai dace ba a matsayin laifi ga bil’adama Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya ce lokaci ya yi da za a amince da takunkumin bai daya da Amurka da kawayenta suka kakaba wa Iran a matsayin wani...
Wani sabon rikici ya barke a jihar Sokoto inda ‘yan bindiga sun kai hari a wani masallaci a kauyen Marnouna da ke karamar hukumar Wurno, inda suka kashe akalla mutum daya tare da yin awon gaba da wasu da ba a tantance adadinsu ba a lokacin da ake sallar isha. Shugaban jam’iyyar APC reshen...
Gwamna Mohammed Umar Bago na jihar Neja, ya yaba wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan kama Abubakar Abba, jagoran kungiyar Mahmuda, daya daga cikin manyan kungiyoyin ta’addanci da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta yi a Najeriya. An ce an kama shi ne a Wawa da ke karamar hukumar Borgu ta Jihar...
Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya ce, “Idan ba a zarge ni wajen binciken gwamnoni da ministocin jam’iyyar da ke mulki ba, bai kamata a zarge ni idan na binciki ’yan hamayya ba.” Duk da haka, mutane da dama a kafafen sada zumunta sun nuna shakku, tare da tambayar dalilin da ya sa EFCC ba ta...
Bankin Duniya ya amince da bayar da dala miliyan 300 domin aiwatar da wani sabon shiri da zai inganta rayuwar ’yan gudun hijira da kuma al’ummomin da suka ba su matsugunni a Arewacin Nijeriya. Bankin ya bayyana cewa a ƙarƙashin shirin mai suna Solutions for the Internally Displaced and Host Communities Project wato SOLID, wanda...
Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga LEADERSHIP a ranar Talata, Kakakin Rundunar ’Yansandan Jihar Bauchi, CSP Ahmed Wakil, ya ce rundunar ‘yansandan ta samu kiran waya da misalin karfe 9:20 na safe daga CLO, inda ya ce Chukwuebuka mai lambar jiha BA/25A/2069 bai farka ba daga barcinsa, yayin da sauran ’yan uwansa Kiristocin ke...
Hukumar Kwastam Najeriya ta kama kwantainoni 16 ɗauke da makamai da miyagun ƙwayoyi da magungunan da wa’adin aikinsu ya ƙare da wasu haramtattun kaya na kimanin Naira 10 a Tashar Jiragen Ruwa ta Apapa da ke Jihar Legas a ranar Litinin. Hukumar ta bayyana cewa ta kama mutane shida dangane da wannan haramtattun kaya da...
Babban sakataren Majalisar Kolin Tsaron kasar Iran Ya bayyana cewa: Kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah ba ta bukatar juya akalarta Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya bayyana cewa: Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah tana da cikakken ilimin siyasar da zata gudanar da al’amuranta bisa dacewa, kuma gwagwarmaya ba ta bukatar horo....
Hakan ya gudana a ƙarƙashin jagorancin hukumomin da ke lura da yadda ake tafiyar da gasar da kuma kare haƙƙin masu amfani da kaya (FCCPC), hukumar kula da tallace-tallace ta Nijeriya (ARCON), da hukumar kula da harkokin caca da wasanni ta Jihar Legas (LSLGA). Zaɓen ya kasance cikin gaskiya da adalci, inda waɗanda yi nasara...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Babban abin kunya ne shirun da gwamnatocin yammacin Turai suka yi game da muggan laifukan ‘yan sahayoniyya Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya dauki kisan gillar da yahudawan sahayoniyya suka yi wa ‘yan jaridun Falasdinawa a matsayin wata shaida ta ta’addancin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila...
Babban Sakataren Majalisar Kolin Tsaron Kasar Iran Ya Ce: ‘Yan Gwagwarmaya Sun San Abubuwan Da Suka Dace
Babban sakataren Majalisar Kolin Tsaron kasar Iran Ya bayyana cewa: Kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah ba ta bukatar juya akalarta Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya bayyana cewa: Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah tana da cikakken ilimin siyasar da zata gudanar da al’amuranta bisa dacewa, kuma gwagwarmaya ba ta bukatar horo....
Kasar Italiya ta janye jirgin ruwanta daga tekun Bahar Maliya bayan gazawarta a fage kwamawa da kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Kasashen Turai sun ci gaba da janye jiragen ruwa da jiragen yaki daga tekun Bahar Maliya, lamarin da ke tabbatar da hukuncin da kasashen nahiyar suka dauka na cewa ci gaba da zamansu a...
Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta kama wasu mutane biyu da ake zargin ’yan kungiyar asiri ne tare da kwato musu wasu abubuwa na bata gari a Ilorin. A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, Adetoun Ejinre-Adeyemi ya fitar, ya ce, ‘yan sandan da ke aiki bisa sahihiyar...
Dakarun Operation FANSAN Yamma (OPFY) sun yi nasarar fatattakar ‘yan ta’adda da dama a wani hari da suka kai ta sama da kasa a yankin Makakkari da ke dajin Gando a karamar hukumar Bukkuyum a jihar Zamfara. Wannan farmakin wanda ya gudana a ranar 10 ga watan Agustan shekarar 2025, ya biyo bayan wasu...
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sake nada Dr. Muheeba Dankaka a matsayin shugaban hukumar kula da da’a ta tarayya (FCC) a wa’adi na biyu na shekaru biyar. Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai, Bayo Onanuga, ya ce nadin na daya daga cikin alkawurran da shugaban kasar ya yi na...
Yajin aikin sai baba-ta-gani da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC reshen jihar Taraba, da kungiyar Kwadago (TUC) reshen jihar Taraba suka kaddamar a ranar Litinin da ta gabata, ya gurgunta ayyukan gwamnati a ma’aikatu da hukumomin gwamnati a jihar. Matakin wanda ya fara da tsakar daren litinin, ya kasance tare da hadin gwiwar shugabannin...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Samun matasan da ke bayar da gudunmawa ga ci-gaban al’ummominsu abu ne da ba kasafai ake samu ba a wannan zamani. Amma duk da haka, wasu matasa sun sadaukar da rayuwarsu wajen bayar da gudunmawarsu wajen ci-gaban al’ummarsu. NAJERIYA A YAU: Yadda Damina Ke Shafar Masu Ƙananan Sana’o’i...
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC) murna bisa ci gaba da riƙe matsayin Maturity Level 3 (ML3) na Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) wajen kula da magunguna da rigakafi. Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Harkokin Bayani da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, a...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jam’iyyar ADC ta zargi hukumar EFCC na yin son zuciya tare da yin aiki a matsayin kayan aikin siyasa ga jam’iyyar mai mulki APC. Jam’iyyar ta gargaɗin cewa irin wannan mataki yana rage ingancin yaƙin da ake da cin hanci da kuma rage amincewar jama’a. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar...
Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya Ya Gudanar Da Zaman Taro Kan Aniyar ‘Yan Sahayoniyya Kan Gaza
Kasashen Turai biyar na kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya sun ki amincewa da matakin mamaye Gaza Wakilin dindindin na Slovenia ya gabatar da wata sanarwa ga kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya a madadin Burtaniya, Faransa, Denmark, da Girka, yana mai cewa: “A matsayinsu na kasashen Birtaniya, Denmark, Faransa, Girka, da Slovenia, sun kira taron gaggawa...
Wani mutum ya ba da kyautar motarsa da ita kadai gare shi ga wani mai jan baki (alaramma) saboda ƙwarewarsa a haddar Al-kur’ani. Malam Yusuf Ɗan-Birni, ya kyautar da motar ce a taron wa’azin wata-wata da Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa Iƙamatis Sunna (JIBWIS) ta shirya a garin Kubwa da ke yankin Babban Birnin Tarayya....
Kungiyar Kwadago da ta ‘yan kasuwa ta Nijeriya (NLC da TUC) reshen jihar Taraba sun bayyana shirin fara yajin aiki tun daga karfe 12 na daren Litinin 11 ga watan Agusta, 2025. Wannan mataki ya biyo bayan sakamakon taron majalisar zartarwa ta jihar da kungiyoyin biyu suka yi a ranar Lahadi a Jalingo, babban birnin...
Rundunar sojin Isra’ila ta ce ta kashe wani fitaccen dan jarida na kafar yada labarai ta Al Jazeera Anas al-Sharif tare da abokan aikinsa hudu a wani hari da ta kai Gaza. Isra’ila ta zarge shi da kasancewa wani jagora na Hamas sannan ta ce ta hallaka shi saboda irin rahotannin da yake bayarwa masu...
Gwamna Oyebanji ya godewa ‘yan majalisar zartarwar jihar da abin ya shafa tare da yi musu fatan samun nasara a ayyukansu na gaba. Sai dai, umarnin bai shafi babban Lauyan jihar da kwamishinan shari’a ba. Har ila yau, daga cikin wadanda sallamar ba ta shafa ba, akwai Kwamishinonin Lafiya da Ayyukan Jama’a, Noma...
Gwamna Mohammed Umar Bago na jihar Neja, ya kaddamar da aikin sarrafa man kade tan dubu talatin a karamar hukumar Mokwa ta jihar tare da alkawarin samar da muhallin kasuwanci don bunkasa. Wani wuri mai daraja na duniya, wanda Salid Agriculture Nigeria Ltd ya gina kuma bankin NEXIM PLC zai samar da shi zai...
Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta cafke wasu mutane shida da ake zargin ‘yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane ne a karamar hukumar Doma da ke jihar. Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar SP Ramhan Nansel ya bayyana haka a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai...
Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta ce ta karfafa matakan tsaro a yankin Babanla biyo bayan harin da wasu da ake zargin mahara ne suka kai musu, inda suka kashe mutane 5 ciki har da dan sanda Adejumo Wasiu. A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, SP Adetoun...
Sin Ta Gudanar Da Gwajin Farko Na Gagarumin Bikin Murnar Cika Shekaru 80 Da Cimma Nasarar Yakin Kin Jinin Harin Dakarun Japan
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Damina lokaci ne da ɗan Adam yake matuƙar bukata. Da za ta yi jinkiri, sai a ga hankalin kowa ya tashi. A lokaci guda kuma, yadda damina kan hana wasu harkoki gudana kan jefa wasu mutane cikin wani irin yanayi. NAJERIYA A YAU: Shekara nawa shugabanni ke bukata...
Sojojin HKI sun shiga yankuna da dama a lardin Qunaitara na kasar Siriya a Jiya Asabar. Inda ta kafa shingaye a kan tituna a wasu garuruwa a lardin suka yi ta binciken ababen hawa, kafin su janye daga baya. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, HKI tana shirin mamayar wadan nan...
Ƴan bindiga sun kashe mutane biyar, ciki har da wani Ɗansanda, a sabon harin da suka kai garin Babanla a ƙaramar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara. Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, kwanaki ƙalilan bayan kisan wasu matafiya uku da garkuwa da wasu biyu a yankin. Mai magana da yawun rundunar ƴansandan jihar, Toun...
Wakilan LEADERSHIP sun lura cewa yanzu ana amfani da wasu daga cikin waɗannan ofisoshin hulɗa da jama’a na Jihar Legas a matsayin matsugunin ‘yan kasuwa na da masu safarar barasa. Binciken da aka yi ya kuma nuna cewa jami’an tsaro da masu kula da waɗannan gidaje suna hayar wasu sassan gine-ginen da daddare don yin...
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da matakin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta dauka na mamaye zirin Gaza Ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da matakin baya-bayan nan da majalisar ministocin gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta dauka na mamaye yankin zirin Gaza da korar al’ummarta, tare da la’akari da...
Jami’in ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa; Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta cimma babban matsayi a yakin kwanaki 12 Ali Baqiri Kani mamba a majalisar tsare-tsaren a ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta cimma babban matsayi a yakin kwanaki 12 da aka kwashe ana gwabzawa da yahudawan...
An sake shiga tashin hankali a Jihar Sakkwato bayan wani sabon mummunan hari da ’yan bindiga suka kai a wasu kauyuka, lamarin da ke ƙara tsananta matsalar tsaro a faɗin jihar. Rahotanni sun nuna cewa duk shekara musamman a lokacin damina, ’yan bindiga sukan ƙara ƙaimi wajen kai hare-haren da ke tarwatsa jama’a a garuruwansu...
Jami’in ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa; Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta cimma babban matsayi a yakin kwanaki 12 Ali Baqiri Kani mamba a majalisar tsare-tsaren a ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta cimma babban matsayi a yakin kwanaki 12 da aka kwashe ana gwabzawa da yahudawan...
Ɗan wasan Liverpool Mohamed Salah ya soki hukumar kwallon kafa ta Turai, UEFA, kan wallafa sakon alhinin mutuwar ɗan wasan Falasɗinawa da ya rasu ba tare da ba da cikakken bayani kan abin da ya yi sanadin rasuwarsa ba. A ranar Alhamis aka kashe Suleiman al-Obeid, wanda aka fi sani da Pelen Falasɗinawa – a...
Gwamna Yusuf Ya Amince Da Korar Wasu Mataimaka Biyu Bisa Hannu Akan Belin Wani Dilan Miyagun Kwayoyi
Gwamnatin jihar Kano ta amince da korar wasu manyan mataimaka na musamman (SSAs) ba tare da bata lokaci ba, sakamakon zarge-zargen da wasu kwamitocin bincike suka yi na gudanar da bincike kan wasu laifuka. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Alhaji Umar Farouk Ibrahim ya fitar. A wani...