2025-10-13@18:08:15 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1641

«gudanar da hawan salla»:

    Zamu kawo muku cikakken bayani idan sun bayyana. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Rundunar Ƴansanda Ta Kama Gaggan Ƴan Fashi 9 A Kano October 13, 2025 Labarai Magance Bala’o’i: Gwamna Lawal Ya Jaddada Ƙudirin Gwamnatin Zamfara Na Ci Gaba Da Haɗin Gwiwa Da NEMA October 13, 2025 Labarai Ba Bu Dalilin Da ASUU Za Ta Fara Yajin Aiki, An Biya Duk Buƙatunsu – Ministan Ilimi  October 13, 2025
    A hakila, sha’anin yawon shakatawa na fadada hanyoyin samun kudi ga mutanen Xinjiang.   Alkaluman da hukumar kula da harkokin al’adu da yawon shakatawa ta Xinjiang ta samar sun shaida cewa, a yayin hutun bikin murnar kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin a kwanakin baya, yankin ya karbi baki masu yawon shakatawa sama da miliyan 18, adadin da ya karu da kashi 11.26% idan aka kwatanta da na bara, kudin da bakin suka kashe ya kai fiye da Yuan biliyan 25, kwatankwacin dalar Amurka sama da biliyan 3.5, wanda kuma ya karu da kashi 11.71%. Hakan ya nuna cewa, aikin yawon shakatawa na Xinjiang yana da makoma mai kyau.   A watan Mayu na wannan shekara, an fitar da “Shirin raya...
    Wani mummunan rikicin ƙabilanci a ƙaramar hukumar  Birniwa ta jihar Jigawa ya yi ajalin mutane biyu, yayin da wasu bakwai suka samu munanan raunuka. Kakakin ’yan sanda ta jihar, DSP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin da yake zantawa da manema labarai. Ya ce tawagar jami’an tsaro ƙarƙashin Operation Salama sun garzaya wurin domin dawo da zaman lafiya tare da cafke wasu mutane bakwai da ake zargi da hannu a rikicin. Ganau sun ce lamarin ya faru ne lokacin da wasu da ake zargin Fulani ne suka kai farmaki ƙauyen Dagaceri, inda suka ƙona gidaje tare da kai wa mazauna garin hari da kibau a lokacin da suke barci. Rahotanni sun ce gidaje da dama sun ƙone...
     Magu ayyukan ceto a gaza sun gano gawakin Falasdinawa fiye da 320 a karkashin burbushin gine-ginen da aka rusa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa tun bayan fara yakin tufanul Aksa shekaru biyu da suka gabata Falasdinawa kimani fiye da 10,000 suka bace. Kuma a zatun mafi yawansu suna bisne a karkashin burbushi na gine-ginan da HKI ta rusa a kansu a zikin gaza. Asbitoci a gaza ya zuwa yansu sun bada sanarwan karban gawakin Falasdinawa 323 wadanda aka zakulo karkashin burbushin gine-gine. Da HKI ta rusa a kansu. Labarin ya kara da cewa a lissafin MDD ya zuwa tsagaita budewa juna wuta a gaza HKI ta rusa gidajen falasdinawa 430,000 a gaza. Banda haka akwai...
    Kungiyar ‘Yan Dako ta kasa reshen jihar Jigawa ta kaddamar da Malam Muhammad Tajudeen Maigatari a matsayin sakataren kungiyar na jihar. Da yake jawabin a lokacin bikin kaddamawar a garin Maigatari, Shugaban kungiyar na jihar Malam Nasiru Idris Sara, ya bayyana shugabanci a matsayin rikon amana a maimakon hanyar tara dukiya da alfahari, a don haka akwai bukatar sakataren ya yi aiki tukuru dan kare martabar sana’ar dako da masu yin ta. Yana mai cewar shugabancin kungiyar zai hada kai da shugabannin kananan hukumomi da masu rike da sarautu da jami’an tsaro a matsayin abokan kawo cigaba wajen daga likkafar sana’ar dako. Nasiru Idris Sara ya kuma yi kira ga daukacin ‘yan dako a fadin jihar da su yi rijista...
    Cibiyar kula da lafiya ta Nasser Medical Complex da ke Gaza ya bayyana cewa: Yara 5,500 ne ke bukatar agajin gaggawa a kasashen waje Daraktan cibiyar kula da lafiya ta Al-Shifa da ke Gaza ya ce: Babu wani agajin jinya da ya shiga zirin Gaza duk da cewa an shafe sa’o’i 72 tsagaita bude wuta. Ya kara da cewa: Mutane 170,000 marasa lafiya da kuma wadanda suka jikkata na bukatar tafiya cikin gaggawa zuwa wajen Gaza domin neman magani. Al-Nasser Medical Complex ya kuma ce: Yara 5,500 na bukatar magani a wajen Gaza. Daraktan asibitin yara na Nasser Medical Complex, Dr. Ahmed Al-Farra, ya bayyana cewa, akwai yara 5,500 a zirin Gaza da ke bukatar agajin gaggawa a wajen yankin...
    Wata kungiya mai zaman kanta ta tantance mutane 60 wadanda za’a yiwa aikin ido kyauta a wasu kananan hukumomi 2 dake jihar Jigawa. Shugaban kungiyar mai zaman kanta, Alhaji Umar Saidu Yelleman Jambola ya bayyana cewar za’a gudanar da aikin ne kyauta ga mutane 60 a kananan hukumomin Malam madori da kaugama. A cewar sa wadanda za su ci moriyar aikin an zabi su ne daga dukkanin mazabu da ke kananan hukumomin. Sa’idu Yalleman ya kara da cewa yara da manya ne za su amfana da aikin idon kyauta wanda kungiyar ta dau nauyi. Da yake jawabi ga manema labarai, Dr Abubakar Adamu yace wadanda aka tantance kuma suke da yanar ido za’a kai su asibitin...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya ce kasar Iran ta yi maraba a tsagaita wuta a Gaza da kuma kawo karshen kisan kiyashi wa Falasdinawa, amma ya kara da cewa HKI ba abar amincewa bace, don haka tana iya yaudara da kuma kawo karshen tsagaaita budewa junan wutar gaba daya. Abu ne da saba yi don haka Falasdinawa su yi hattara. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a jiya Asabar ya kuma kara da cewa, Iran tana maraba da dukkan abinda zai kai ga kawo karshen kisan kiyashi a gaza, wanda ya dau shekaru 2 ana yi. Ministan ya jawo hankalin Hamas da sauran Falasdina kan amincewa da duk abin HKI...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il Makaie ya tir da HKI saboda hare-haren da ta kai kan wasu wurare a kudancin kasar, Lebanon wanda ya sabawa da farko yarkeniyar tsagaita wutan da ta cimma da kungiyar Hizbulla a cikin watan Nuwamban shekara ta 2024 sannan ya sabawa dokokin kasa da kasa. Baghaei ya bayyana cewa ci gaba da keta hurumin kasar Lebanon a kai a kai, da kuma shirun da kasashen duniya suka yi duk sun sabawa dokokin kasa da kasa wadanda HKI da wadanda suke riya daukar nauyin kola da cewa an dabbaka yarjeniyar MDD na kuduri mai lamba 1107. Ya zargi kasashen Faransa da kuna Amurka wadanda suka gabatar da kansu a matsayin masu lamuni don aiwatar...
      Hukumar kwallon kafa ta Nijeriya (NFF) ta tabbatar da cewa ta dauki matakin gaggawa bayan faruwar lamarin inda aka aike da wani jirgin sama daga Legas domin jigilar tawagar zuwa Uyo, sai dai lamarin ya haifar da tsaiko a shirin da tawagar ta ke yi na tunkarar jamhuriyar Benin a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya na shekarar 2026. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0 October 9, 2025 Wasanni Ba Yanzu Zan Koma Gasar Firimiyar Ingila Ba – Harry Kane October 7, 2025 Wasanni Yanzu-Yanzu: Kwara United Ta Sallami Kocinta, Tunde Sanni October 6, 2025
      Ba abin mamaki ba ne cewa tsaro shi ne babban ƙalubalen da jihar Zamfara ta daɗe tana fama da shi. Daga Maradun zuwa Shinkafi, daga Anka zuwa Zurmi, matsalar ‘yan bindiga ta yi ƙatutu na tsawon shekaru.   Da yake karɓar mulki, Gwamna Dauda Lawal ya sanar da cewa “ba za a iya gina tattalin arziki ba idan tsoro ya mamaye ƙasa.”   Tun daga farkon watannin mulkinsa, ya kafa Kwamitin Tsaro na Musamman, wanda ke haɗa jami’an soja, ‘yan sanda, NSCDC da ‘yan sa-kai. Gwamnatin ta samar da motocin sintiri sama da 500, da kayan aikin zamani ga jami’an tsaro.   Har ila yau, an kafa Command and Control Centre a Gusau domin sa ido kan al’amuran tsaro...
    Al’ummomin dake garin Warwade da kewaye a karamar hukumar Dutse ta jihar Jigawa sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta yashe madatsar ruwa ta Warwade wanda ta kasance daya daga cikin hanyar samun aikin dogaro da kai ga Mazauna yankin. Wakilinmu Usman Mohammed Zaria ya ziyarci al’ummomin da ke zaune a kusa da mmadatsr ruwan wanda aka gina ta sama da shekaru hamsin da suka gabata. Madatsar ruwan ta Warwade ta kasance hanyar samun sana’o’in dogaro da kai ga mazauna yankin, wadanda suke kamun kifi da noman rani domin samun na yau da kullum. Malam Umar Sani, wanda masunci ne a Warwade, yace da abin da yake samu daga kamun kifi yake kula da iyalan shi da kuma sauran...
    Bayanan da suka fito daga kasar Indunusiya sun nuna cewa gwammnatin kasar ta ki bada visa ga tawagar wasan jiminastik din HKI da aka shirya za’a yi wasa a birnin Jakarta a wannan watan, domin nuna rashin amincewa da kisan kare dangi da HKI ke yi a yankin Gaza. Wannan matakin yana kara nuna irin yadda batun kisan kiyanshin gaza yayi tasiri sosai hatta a harkar wasanni, kasar dake da yawan musulmi tana aikewa da sako na siyasa ne ta hanyar takawa yan wasan isra’ila birki, da kuma neman goyon bayan duniya ga alummar falasdinu. An tsara cewa tawagar wasan Jemanastik din HKI ta za shiga gasar jiminastik na duniya da za’a yi a Jakarta daga ranar 19-25 ga wannan...
      “Abin takaici ne ace Nijeriya tana karancin Mlaman makaranta da suka kai 194,876 a makarantun gwamnati a fadin tarayyar Nijeriya. Halin da makarantunmu na Sakandare suke ciki shi ma lamarin bata canza zane ba. Rashin isassun Malamai shi ma lamarin abin damuwa ne domin kuwa sannu a hankali hakan zai iya shafi samar da ingantaccen ilimi a makarantunmu kamar yadda sakamakon hakan ba zai haifar da da mai ido ba cewar, Amba”.   Don haka ya ja kunnen Nijeriya cewa rashin isassun Malaman zai iya kawo cikas wajen kokarin da Nijeriya ta ke yi na cimma muradin ci gaba na 4 (SDG 4) da ya kunshi ingantaccen ilimi ba tare da wani bambanci ba, tsakanin gwamnatoci uku ba tare...
    Bangarorin kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa sun fitar da sanarwar hadin gwiwa kan tsagaita bude wuta a Gaza Kungiyar Hamas, Jihad Islami, da kuma Popular Front mai fafatukar ‘yantar da Falasdinu, sun fitar da sanarwar hadin gwiwa a jiya Juma’a, inda suka bayyana matakin farko na yarjejeniyar tsagaita bude wuta a zirin Gaza, inda suka yi maraba da gwagwarmayar al’ummar Falastinu, musamman a Gaza wajen fuskantar laifukan yahudawan sahayoniyya. Kungiyoyin Hamas da na sauran kungiyoyin Falasdinu sun yaba da jarumtar gwagwarmayar da ta janyo hasara ga makiya, suna masu jaddada cewa: “Muradin jama’a da ‘yan gwagwarmaya ya fi duk wani yunkuri na murkushe su.” Har ila yau, sun jinjinawa “bangarori masu goyon bayansu a Yemen, Lebanon, Iran, da Iraki saboda goyon bayan...
    Falasdinawan da HKI ta kora daga gidajensu a birnin Gaza sun kama hanyar komawa gidajensu a birnin Gaza dake arewacin yankin Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran reuters na cewa ya zuwa tsakiyar rana a yau jumm’a sojojin HKI sun janye makamansu daga babban titi wanda ya taso daga arewacin zirin Gaza zuwa kudancin yankin , wanda kuma ake kira Titin Rasheed. Sun janye zuwa inda aka amince zasu koma a wannan matakin na sabon yarjeniyar.  Hotunana daga yankin ya nuna falasdinawa gungu-gungu suna takawa da kafa zuwa arewacin zirin Gaza, daga inda sojojin yahudawan suka koresu a farkon watan da ya gabata, suka kuma hana kowa bin kan titin Rasheed. A wani bangare...
    Hukumar Kwastam shiyyar bodar Najeriya ta Seme da ke jihar Legas ta ce ta cafke motoci biyar da ke maƙare da buhuna 10,000 na lalatacciyar fulawa da darajarsu ta kai Naira biliyan 1.2. Rundunar ta kuma ce ta tara jimillar kuɗin shigar da ya kai Naira biliyan daya da rabi a watan Satumba, wanda hakan ya nuna kari da kaso 182 cikin 100 idan aka kwatanta da Naira miliyan 531 da aka tara a watan Agustan da ya gabata. NAJERIYA A YAU: Kalubalen Da Ke Gaban Sabon Shugaban Hukumar Zabe Ta Kasa Tinubu ya yi wa Mamman Vatsa, Farouk Lawan da wasu mutum 173 afuwa Kwamandan rundunar a shiyyar, Wale Adenuga, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai na...
    Rahotanni daga Gaza na cewa Isra’ila ta fara janye sojojinta daga wasu yankuna na zirin Gaza. Wannan dai na zuwa ne bayan da gwamantin Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta dake kunshe a shirin zaman lafiya na Trump da ta cimma da kungiyar Hamas. Daraktan Hukumar Ba da Agajin Gaggawa da Hadin Kan Kasa da Kasa ta Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Gaza Mohammad Al-Moughayyir, ya ce sojojin Isra’ila sun janye daga yankuna da dama a cikin birnin Gaza da arewacin zirin da kuma wasu yankunan kudancin yankin. A Khan Younis da ke kudancin zirin Gaza, Motocin Isra’ila sun janye daga kudancin birnin da tsakiyar birnin zuwa yankunan gabashi. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of...
    Hukumar Bunkasa Ma’aikata ta Jihar Jigawa ta shirya taron karawa juna sani na kwana daya ga jami’an kula da dakunan karatu  a wani bangare na aikinta na daga darajar ma’aikata da ma’aikatan gwamnati da masu zaman kansu.   A jawabinsa na bude taron, Darakta Janar na MDI, Umar Farouk Wada, ya ce makasudin shirya taron shi ne don bunkasa kwarewa da sanin makamar aikin da ake da su ta yadda za a samar da ingantacciyar hidima kamar yadda Cibiyar ta tanadar.   Ya kuma bayyana cewa, za a ci gaba da gudanar da irin wannan horon ne domin a baya Cibiyar ta shirya bita ga nau’ukan ma’aikatu masu zaman kansu da na gwamnati.   Umar Farouk ya bayyana ɗakin karatu...
    Mai Magana da yawun gwamnatin Iran Fatemeh Mohajerani ta tabbatar da cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran a ko da yaushe tana goyon bayan al’ummar Palastinu a gwagwarmayar neman ‘yanci da mutunci. A cikin wata sanarwa da ya fitar, Mohajerani ta ce Iran za ta goyi bayan duk wani mataki ko wani shiri da zai kai ga dakatar da kisan kiyashin da ake yi a Gaza, da janyewar sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila, da shigar da kayayyakin jin kai, da sakin fursunonin Falasdinu, da kuma tabbatar da hakkinsu na yau da kullun. Ta yi nuni da cewa goyon bayan Iran ga al’ummar Palasdinu “ba matsayi ne na siyasa kawai ba, a’a yana dogara ne akan  imani da ‘yancin al’ummar Palasdinu da kuma...
    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da afuwar Shugaban Kasa ga mutane 175. Daga ciki har da wadanda aka yi wa afuwar bayan mutuwa ga marigayi Manjo Janar Mamman Jiya Vatsa da ɗan gwagwarmayar kwato ’yancin kan Najeriya, Herbert Macaulay. An dauki wannan mataki ne bayan amincewa da shawarwarin da Majalisar Tsofaffin Shugabannin Ƙasa ta bayar a taronta da aka gudanar a ranar Alhamis a Abuja. Gwamnatin Kano ta shirya ɗaurin auren ma’aurata 2,000 Tinubu ya naɗa Amupitan a matsayin Shugaban INEC A cewar sanarwar da mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin bayanai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya kuma yi afuwa ga tsohon ɗan majalisa Farouk Lawan da wasu mutum uku, Misis Anastasia...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Masu Kallon Fina-Finai Na Sin Sun Gamsu Da Fina-Finan Da Aka Gabatar A Lokacin Hutun Bikin Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar Sin Ta 2025 October 9, 2025 Daga Birnin Sin Sin Na Ci Gaba Da Goyon Bayan Kawo Karshen Rikicin Gaza October 9, 2025 Daga Birnin Sin An Yi Tafiye-tafiye Miliyan 16.34 Da Suka Shafi Shiga Da Fita Daga Kasar Sin Yayin Hutun Kwanaki 8 Na Kasar  October 9, 2025
    Rahotanni sun bayyana cewa, karar mai lamba FHC/OS/194/2024, ta nemi umarnin tilastawa INEC da shugabanta na lokacin da su sanya sunayen wasu jami’an Jam’iyyar AA a shafin hukumar na yanar gizo bayan an cire su.   Sai dai Udeze ya ci gaba da cewa, babu irin wannan hukunci ko umarnin kama shi (Yakubu), yana mai tabbatar da cewa, rahotannin ƙage ne kawai. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC  October 9, 2025 Labarai SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati October 9, 2025 Labarai An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba October 9, 2025
    Jami’an Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa (NIS) a Jihar Jigawa, sun kama wani matashi da ake zargi da sato motar asibiti daga Jamhuriyar Nijar, yayin da yake ƙoƙarin shigowa da ita Najeriya. Kwanturolan hukumar a jihar, Tahir Abdullahi Musa ne, ya tabbatar wa manema labarai hakan a Dutse. Falasdinawa na murna da tsagaita wutar hare-haren Isra’ila a Gaza Sauye-sauyen Tinubu ba su rage talauci a Najeriya ba — Bankin Duniya Ya ce an kama wanda ake zargin mai suna Yusif Bashir da motar asibiti ƙirar Toyota Land Cruiser mai lambar ONG-0777, bayan ya shigo da ita ta iyakar Babura da Jamhuriyar Nijar. Tahir, ya ce tuni hukumar ta fara shirye-shiryen miƙa sh ga rundunar ’yan sandan jihar, domin ci...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Kira ga tsayar da sallah wani aiki ne na wajibi ga hukumomin da’awar addini da malamai Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya jaddada cewa: Kira ga tsayar da sallah da koyar da ita, da bayyana ma’anonin da ke cikinta, da riko da ita, wani aiki ne na wajibi da ya rataya a wuyan hukumomin da’awar addini da malamai da ma’abuta addini. Dole ne a yi amfani da hanyoyin zamani domin watsa wannan fanni. A cikin sakon da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya aike ga zaman taron cibiyar karfafa tsayar da sallah karo na 32 ya bayyana cewa: Taron karfafa tsayar da sallah yana daya daga cikin mafi...
    Kungiyar Jihadul-Islami ta Falasdinu ta bayyana cewa: Abin da aka cimma na yarjejeniyar dakatar da bude wuta ba kyauta ce daga kowa ba Kungiyar Jihadul-Islami ta Falastinu ta bayyana cewa: Yarjejeniyar tsagaita bude wuta da musayar fursunoni da makiya yahudawan sahayoniyya ba kyauta ce daga kowa ba. A cikin wata sanarwar manema labarai da ta fitar da safiyar yau Alhamis din nan, kungiyar Jihadul -Islami ta kara da cewa: Ko da yake ba su musanta yunkurin kasashen Larabawa da na kasa da kasa ba, amma suna jaddada gagarumin sadaukarwar da al’ummar Falastinu suka yi da kuma jajircewa da dogewa wajen kalubalantar makiyansu a fagen daga. Bayanin ya ci gaba da cewa: A wannan lokaci na tarihi, al’ummar Falasdinu ba za...
    An shawarci mata a karamar hukumar Kirikasamma da ke jihar jigawa da su kawo ‘ya’yansu domin yi musu rigakafin cutar shan inna, kyanda, da Gaida da sauran cututtuka masu ban tsoro.   Uwargidan Shugaban Karamar Hukumar, Hajiya Fatima Maji Marma ta ba da wannan shawarar a lokacin kaddamar da shirin rigakafin cutar kyanda da na rigakafi na yau da kullum a fadar Hakimin Marma.   Ta kuma jaddada aniyar karamar hukumar na bayar da tallafin da ake bukata domin samun nasarar gudanar da aikin rigakafin.   Hajiya Fatima ta kuma yabawa gwamnatin jihar Jigawa bisa bullo da inshorar lafiya ga marasa galihu a matakin unguwanni a kananan hukumomin jihar 27.   A nasa jawabin manajan hukumar kula da lafiya matakin...
    Hukumar kiyaye haddura ta kasa reshen jihar Kano ta sanar da fara aiki a hukumance da sabon kwamandan hukumar, Kwamanda Idris Mohammed Lawal.   Kwamanda Lawal ya karbi ragamar shugabancin hukumar ta Kano ne biyo bayan tura shi da hukumar FRSC ta yi a ranar 3 ga watan Oktoba.   Ya gaji kwamandan Corps MB Bature, wanda ya yi ritaya a kwanan baya bayan ya kamala shekarun sa a aikin gwamnati.   Kafin sabon mukamin nasa, Lawal ya taba zama shugaban aiyuka na shiyyar a hedikwatar hukumar FRSC shiyya daya da ke Kaduna.     A jawabinsa na farko, sabon Kwamandan sashin ya nuna godiya ga rundunar Corps Marshal da Hukumar FRSC bisa amincewarsu. Ya yi alkawarin sadaukar da aikin...
    Kwamishinan kasuwanci da masana’antu na jihar Zamfara, Abdulrahman Muhammad Tumbido, ya yabawa gwamna Dauda Lawal bisa jajircewar sa wajen tallata jihar Zamfara a matsayin cibiyar zuba jari.   Kwamishinan, wanda ya bi sahun gwamna Lawal a wata tawaga ta hukuma zuwa bikin baje kolin kasuwanci da zuba jari na Canada–Africa da aka gudanar a Toronto, Canada, ya ce halartar gwamnan ya bude wa jihar sabbin damammaki na kasuwanci da bunkasar tattalin arziki.   A wata sanarwa da jami’in yada labarai na ma’aikatar, Jamilu Bello, Tumbido ya fitar, ya tabbatar da cewa ma’aikatar kasuwanci da masana’antu za ta ci gaba da bin diddigin ayyukan hadin gwiwa da yarjejeniyoyin da aka kulla a wannan tafiya.   A cewarsa, Gwamna Lawal ya baje...
    Gwamna AbdulRazaq ya yabawa Shugaba Tinubu yayin da Sojoji suka tura cikakken birgediya domin fatattakar masu garkuwa da mutane daga dazukan Kwara.     Hedkwatar sojojin Najeriya ta aika da  cikakken birgediya da manyan kayan aiki a sassa daban-daban na Kwara ta Kudu, domin rage matsalolin tsaro a yankin.   Wata sanarwa da sakataren yada labarai gwamnan, Rafiu Ajakaye ya fitar ta ce Tuni dai sojojin suka yi ta luguden wuta ta cikin kauyukan Oke Ode da Babanla, dukkansu a karamar hukumar Ifelodun.   Har ila yau, rundunar ta kara da cewa, aikin ya zarce zuwa Edu da Patigi domin ratsa dazuzzukan da masu garkuwa da mutane suka fara kai hare-hare na matsorata a kan al’ummomi daban-daban tare da yin...
    Falasdinawan da ke Gaza da Isra’ila ta shafe sama da shekara biyu tana kai wa hare-hare sun nuna jin dadi da farin ciki bayan sanar da yarjejeniyar tsagaita wuta da nufin kawo karshen yakin. Yayinda labarin yarjejeniyar ya yadu a cikin yankin da aka kewaye, mazauna Khan Younis a kudancin Gaza sun fito tituna suna murna da fatan wannan zai zama farko zaman lafiya daga hare-haren Isra’ila. Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙaryata rahoton Bankin Duniya kan yawan talakawa a Najeriya Majalisa ta yi watsi da zargin Amurka na yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya “Alhamdulillah da wannan dakatar da fada, karshen zubar da jini da kashe-kashe… duk Gaza na cikin farin ciki,” in ji Abdul Majeed Abd Rabbo, mazaunin...
    Fadar Shugaban Ƙasa ta yi fatali da sabon rahoton tattalin arziki da Bankin Duniya ya fitar, wanda ya kiyasta cewa mutane miliyan 139 na rayuwa cikin talauci. Fadar ta bayyana adadin a matsayin wanda ya saba da zahiri kuma ya kauce wa hakikanin halin tattalin arzikin ƙasar. SSANU da NASU za su yi wa gwamnati zanga-zanga kan rashin cika musu alƙawari 2027: Atiku, Jonathan da Obi ba za su iya kayar da Tinubu ba — Kalu Mai ba Shugaban Najeriya Bola Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa, Sunday Dare, ya bayyana a shafinsa na X a ranar Laraba cewa dole ne a rahoton bai duba yanayin tsarin auna talauci na duniya ba. “Duk da cewa Najeriya na daraja...
    ShareTweetSendShareMASU ALAKA Daga Birnin SinBabban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan October 8, 2025Daga Birnin SinYawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana October 8, 2025Daga Birnin SinAdadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7 October 8, 2025
    Dalibai da malaman Jami’o’i a kasar Burtania sun bar ajujuwansu don halattar ganganmi a cikin jami’o’insu, na goyon bayan al-ummar Falasdinu da kuma yin tir da gwamnatin kasar saboda goyon bayan da take bawa HKI a kissan kiyashi, wanda ya kai shekaru biyu kenan a Gaza. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa  zanga zangar bata takaita a jami’o’in birnin London kadai ba, sai dai an gudanar da su a manya –manyan biranen kasar duk tare da gargadin jami’an yansandar kasar kan cewa an haramta zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a kasar. Sauran biranen da aka gudanar da gangamin dai sun hada Glasgow, Manchester, Bristol, Sheffield da Edinburgh. Daliban da kuma malamansu suna rera taken “Yanci ga Falasdinu...
    Al’umma a kauyen Sumore da ke Ƙaramar Hukumar Dutse a Jihar Jigawa sun shiga cikin alhini bayan mutuwar wata mata mai shekaru 30, Adama Hannafi, wacce ake zargin ta rataye kanta. Lamarin, wanda ya faru a ranar Talata, ya tayar da hankulan mazauna kan ƙalubalen da ke tattare da rashin lafiyar kwakwalwa a cikin al’umma, musamman a yankunan karkara. ‘Akwai ɗaliban da ke yin digiri yanzu ba tare da sun taɓa shiga ɗakin karatu ba saboda AI’ Joash Amupitan na iya zama sabon shugaban INEC Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, SP Lawan Shi’isu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an samu gawar matar a rataye a jikin wata bishiya a kauyen. “Mun samu kiran...
    Dakarun bangaren sojin kungiyar Jihadul Islama ta Falasdinu Sarayal-Quds ta bayyana cewa: Fursunonin mamaya ba za su ga hasken rana ba har sai an sharuddan Falasdinawa Dakarun bangaren sojin kungiyar Jihadul Islama ta Falasdinu, sun jaddada cewa: Fursunonin mamayar Isra’ila ba za su ga hasken rana ba, sai dai ta hanyar tattaunawa da musayar ra’ayi da yahudawan sahayoniyya da suka kuduri aniyar kawo karshen yakin Gaza. A cikin wata sanarwa da dakarun Sarayal-Quds suka fitar, sun jaddada cewa su da dukkanin bangarorin gwagwarmaya ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen samar da hanyar kawo karshen yakin Gaza da kuma wahalhalun da Falasdinawan suke ciki. Har ila yau, sun tabbatar da cewa: “Makaman ‘yan gwagwarmaya makamai ne da aka...
    Falasdinawa 12 ne suka yi shahada a Gaza yayin da sojojin mamayar Isra’ila ke ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri kan yankin a yau Sojojin mamayar Isra’ila na ci gaba da zafafa matakan soji a zirin Gaza duk da kiran da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na Isra’ila ta gaggauta dakatar da kai hare-hare a zirin Gaza. Majiyoyin lafiya a asibitocin Gaza sun watsa rahoton cewa: Hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suka kai a cikin ‘yan sa’o’i da suka gabata ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa 12 da suka hada da hudu a birnin Gaza da bakwai a Khan Yunis da ke kudancin zirin Gaza, yayin da wani Bafalasdine daya ya yi shahada a yankin tsakiyar Falasdinu....
    Ya gargaɗi masu aikata laifuka da su daina, ko kuma su fuskanci hukunci, inda ya bayyana cewa waɗanda aka kama tuni aka miƙa su kotu.ShareTweetSendShareMASU ALAKA Labarai‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno October 8, 2025Manyan Labarai‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio October 8, 2025LabaraiCika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya October 7, 2025
    Dubban mutanen kasar Moroko ne su ka fito kan titunan birnin Rabat domin yin Zanga-zangar nuna goyon bayansu ga al’ummar Falasdinu da HKI take yi wa kisan kiyashi. Mahalarta Zanga-zangar sun hada lauyoyi, dalibai, kungiyoyin fararen hula da sauran mutanen gari, suna dauke da tutar Falasdinu, tare da kuma da bayar da taken: “Yanci ga Falasdinu, da yin kira da a shigar da kayan agaji a cikin yankin na Gaza. Bugu da kari, masu Zanga-zangar sun yi gangami a bakin ginin majalisar dokokin kasar. Mutanen sun nuna rashin amincewarsu da  halin da mutanen Gaza suke ciki, tare da yin kira da a kawo karshensa. Mahalarta Zanga-zanagr dai sun fito ne daga biranen Tangier, Casbalanca da Feiz, da kuma wasu garuruwa...
    Hukumar kula da yan gudun hijirar a majalisar dinkin duniya ta jinjinawa kasar Iran game da kokarin da tayi wajen kulawa da miliyoyin yan gudun hijira kasar Afghanistan , da suka zauna a kasar na tsawon shekaru, Babban darakta na hukumar ta IOM shi ne yayi wannan bayani ga Mohammad Batgae mtaimakin ministan harkokin cikin gidan kasar iran a birnin janeva a jiya litinin, a wani taro da suka gudanar a bayan babban taron Majalisar dinkin duniya karo na 76 da hukumar kula da yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya take gudanarwa. Ana sa bangaren bathaei babban jami’I na kasar Iran ya bayyan yadda jamhuriyar musulunci suka bada kula ta musamman  ga dubban yan gudun hijiran kasar ta Afghanistan...
    Tun bayan harin 7 ga watan Oktoba, 2023, da mayaƙan Hamas suka kai wa Isra’ila wanda ya hallaka sojoji sama da 60 , Isra’ila ta fara luguden wuta a Gaza.Tun daga wannan lokacin, yankin ya zama wurin tashin hankali da yunwa, inda mutane da dama ke mutuwa a kowace rana.Tags: FalasɗinawaGazaHamasIsra'ilayaƙiShareTweetSendShare Sadiq Related Kasashen KetareMe Yarjejeniyar Kawo Karshen Yakin Gaza Da Amurka Ta Tsara Ta Kunsa? 3 days agoKasashen KetareWadanne Kasashen Afirka Ne Ba Sa Goyon Bayan Kafa Kasar Falasdinawa? 1 week agoKasashen KetareBirtaniya Ta Amince Da Kafa Falasɗin A Matsayin Ƙasa 2 weeks ago
    Al’ummar Ƙaramar Hukumar Kebbe da ke Jihar Sakkwato sun roƙi gwamnati ta ba su dama su riƙa ɗaukar makamai domin kare kansu daga hare-haren ’yan bindiga da suka addabi yankinsu. Mutanen sun ce sun gaji da kashe-kashe, sace-sace, da kona gidaje da gonakinsu da ’yan bindiga ke yi, wanda ke jefa su cikin tsananin wahala da asara. Mazauna yankin sun ce daga cikin garuruwa 17 da ke cikin Ƙaramar Hukumar Kebbe, an riga an raba mazauna akalla 11 da gidajensu saboda yawan hare-hare. Wani shugaban al’umma a yankin, Tukur Muhammad Fakum, ya shaida wa BBC cewa halin da suke ciki ya sa suka fara tunanin yadda za su kare kansu da kansu. Ya kamata a karɓe ikon naɗa Shugaban INEC...
    Al’ummar Ƙaramar Hukumar Kebbe da ke Jihar Sakkwato sun roƙi gwamnati ta ba su dama su riƙa ɗaukar makamai domin kare kansu daga hare-haren ’yan bindiga da suka addabi yankinsu. Mutanen sun ce sun gaji da kashe-kashe, sace-sace, da kona gidaje da gonakinsu da ’yan bindiga ke yi, wanda ke jefa su cikin tsananin wahala da asara. Mazauna yankin sun ce daga cikin garuruwa 17 da ke cikin Ƙaramar Hukumar Kebbe, an riga an raba mazauna akalla 11 da gidajensu saboda yawan hare-hare. Wani shugaban al’umma a yankin, Tukur Muhammad Fakum, ya shaida wa BBC cewa halin da suke ciki ya sa suka fara tunanin yadda za su kare kansu da kansu. Ya kamata a karɓe ikon naɗa Shugaban INEC...
    Wani saksmkon kuri’ar jin ra’ayin jama’a da cibiyar dimokuradiyya ta Isra’ila ta gudanar ya nuna cewa kashi 66 cikin 100 na Isra’ilawa sun yi imanin cewa lokaci ya yi da za a kawo karshen yakin Gaza, tare da bayyana hadarin da fursunoni ke fuskanta. Wannan adadi na kashi 66% ya karu da kashi 13% a kan sakamakon da aka fitar a shekara guda da ta gabata lokacin da aka yi musu tambaya iri ɗaya. Sakamakon  ya kuma nuna cewa kashi 45% na Isra’ilawa sun yi imanin cewa ya kamata Firayim Minista Benjamin Netanyahu ya yi murabus nan da nan kafin karshen yakin, tare da dora masa alhakin abubuwan da suka faru a ranar 7 ga Oktoba, 2023. Sakamakon ya nuna...
    Kungiyar Jihadul-Islami ta jaddada cewa: Za ta ci gaba da kare kasarsu da kuma neman kai wa ga dukkan hakkokin al’ummarsu Kungiyar Jihadul-Islami ta Falasdinu ta tabbatar a yau Litinin din nan cewa: Za ta ci gaba da daukar alkawarin kare al’ummarsu da wurarensu masu tsarki har sai sun kai ga samun ‘yancin kwato kasarsu, tare da cikakken hadin gwiwa da dukkanin dakarun gwagwarmayar Falastinawa karkashin jagorancin kungiyar gwagwarmaya ta Hamas. A cikin sanarwar da kungiyar ta fitar ta bayyana cika shekaru 38 da gudanar da jihadi da kuma cika shekaru biyu da harin daukan fansa na “Ambaliyar Al-Aqsa”, kungiyar ta ce: Shekaru 38 da kaddamar da Harkar Jihadin Musulunci ta Falastinu ta zo daidai da cikar shekaru biyu na...
    Babban mai shiga tsakani na kungiyar gwagwarmayar falasdinawa ta Hamas Khalil Al-Hayya ya isa Masar, inda ya jagoranci tawagar da ake sa ran za ta fara tattaunawa wacce ba ta kai tsaye ba da Isra’ila, a cewar kungiyar. Hamas ta ce za a fara tattaunawar ce kan “hanyoyin tsagaita bude wuta, da janye sojojin mamaya, da musayar fursunoni.” yau Litinin ne aka tsara tawagar Isra’ila za ta isa wurin, kamar yadda ofishin Benjamin Netanyahu ya bayyana, a wani bangare na tattaunawar. Su ma wakilan Amurka, Masar da kuma Qatar zasu halarci tattaunawar a matsayinsu na masu shiga tsakani. A cewar majiyoyin diflomasiyya, tattaunawar tsakanin Isra’ila da Falasdinawa za ta gudana ne a birnin Sharm el-Sheikh. Ana sa ran tattaunawar za...
      Shugaba Mahama ya kuma yabawa kamfanin Greenhouse International Development Group saboda irin ayyukan da ya gudanar a kasar tun daga shekarar 2011 da ya shiga Ghana, ciki har da yankin masana’antu na Bright International Industrial Park da masana’antu da dama masu samar da kayayyaki a farashi mai rahusa ga ‘yan kasar da samar da gurabun ayyuka kimanin 10,000 tare da zuba jari a bangaren aikin gona da na gine-gine. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A ranar Talatar da ta shude ne dai aka ga gawar jakadan kasar Afirka Ta Kudu a kasar Faransa Nathi Matherhwa, da aka nuna cewa ya fado daga kan benen Hotel hawa na 22. Babban sufeton ‘yan sanan kasar ta Afirka Ta Kudu Fenni Masemola ya sanar da aikewa da tawagar masu bincike su biyar da za su hada karfi da takwarorinsu na Faransa domin gudanar da bincike akan musabbabin mutuwar jakadan. A ranar Litinin din makon da ya shude ne dai matar jakadan ta sanar da cewa ya bace, lamarin da ya bude kofar bincike da ta kai ga ganin gawarsa a kasan Hotel din Hyatt Regency a ranar Talata. Wani jami’in ‘yansanda Faransa ya fada wa manema labaru...
    Jaridar Ma’ariv ta HKI ta buga labarin da yake cewa gwamantin HKI ta kwace kudaden gwamnatin kwarya-kwarya ta Faladinu da sun kai dala miliyan 7.54 ta rabawa wasu iyalan yahudawa 41 da su ka riya cewa hare-haren Faladinawa sun yi sadaniyyar kashe musu ‘ya’ya da dangi. Jaridar ta kuma kara da cewa; An rabawa iyalan yahudawan kudin da sun kai Shakel miliyan 25 wanda shi ne kwatankwacin Dala miliyan 7.54, ta hannun lauyoyinsu. Haka nan kuma jaridar ta ce hukumar dake kula da haraji da ke karkahsin ma’aikatar shari’a ce ta aiwatar da raba kudin a matsayin abinda su ka kira diyyar ayyukan t’addanci.! Jaridar ta kuma ce tun a 2019 ne wadannan ‘yan sahayonioyar su ka bukaci a biya...
    Sanarwar ta ƙara da cewa: “A cikin baƙin ciki muke alhinin rasuwar Ambasada Muhammad Jabbi Maradun, fitaccen dattijon jiha kuma ɗan jiharmu ta Zamfara na gaskiya.   “An haifi Jakada Jabbi ne a ranar 12 ga Nuwamba a shakrar 1943, a Ƙaramar Hukumar Maradun.   “Ambasada Maradun ya taba zama jakadan Nijeriya a ƙasar Tunisia daga 1999 zuwa 2003.   “Ya yi fice a yunƙurin samar da jihar Zamfara.   “Bayan kafuwar jihar Zamfara, Ambasada Jabbi ya shiga gwamnatin soja ta farko a ƙarƙashin Kanar Jibril Bala Yakubu, inda ya riƙe muƙamin kwamishinan Kasuwanci, Masana’antu da Yawon Buɗe Ido.   “Ayyukan sa na siyasa sun haɗa da jam’iyyun GNPP, NPN, da NRC, kuma ya kasance mai ruwa da tsaki a...
    Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya gana da Gwamna Siminalayi Fubara da wasu Dattawan Jihar Ribas. Mai taimaka wa Wike kan yaɗa labarai, Lere Olayinka ne, ya wallafa hoton ganawar a shafukan sada zumunta, inda ya ce kakakin Majalisar Dokokin jihar, Martin Amaewhule, ya halarci taron. An yi wata gagarumar zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a Turai Ban taɓa cewa Buhari yana da alaƙa da Boko Haram ba — Jonathan Ko da yake Olayinka bai bayyana abin da aka tattauna a taron ba, amma wannan ce ganawa ta farko da aka yi tsakanin Wike da Fubara tun bayan da gwamnan ya kori wasu daga cikin muƙarrabansa yayin da yake shirin kafa sabuwar majalisar zartarwa a jihar. Rahotanni sun nuna cewa...
    Dubun dubatar mutane ne suka fito zanga-zanga jiya Asabar a sassan wasu ƙasashen Turai domin nuna goyon baya ga Falasɗinawa, tare da kiran a kawo ƙarshen yaƙin Gaza. Rahotanni sun ce masu zanga-zangar sun kuma buƙaci a saki masu fafutuka da ke cikin ayarin jiragen ruwan nan da ke hanyar kai kayan agaji ga Falasɗinawa a Gaza. Rundunar Sojin Nijeriya ta cafke jami’anta 16 kan saɓa ƙa’idar aiki Fitaccen ɗan jarida a Kano, Aliyu Abubakar Getso ya rasu ’Yan sanda a birnin Rome na Italiya sun ce kimanin mutane dubu 250 ne suka fito zanga-zanga a rana ta huɗu a jere, bayan da Isra’ila ta kama ayarin jiragen ruwa 45 da ke ƙoƙarin isa Gaza domin kai wa al’umma agaji...
    Iran ta yi kira ga kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC da ta dauki matakin haramtawa Isra’ila shiga harkokin wasanni na kasa da kasa. A cikin wata wasika da ya aike zuwa ga ministocin harkokin wasanni na kasashe 57 na kungiyar ta OIC, ministan wasanni da matasa na kasar Iran Ahmad Donyamali ya bukaci takwarorinsa da su hada karfi da karfe wajen ganin an kawar da Isra’ila daga wasannin kasa da kasa. Mista Donyamali ya yi kira da a kafa kungiyar wasanni ta kasashen musulmi domin neman kwamitin Olympics na kasa da kasa (IOC) ya dakatar da gwamnatin Isra’ila a gasar wasannin duniya. A cikin wasikar tasa, ya jaddada cewa gwamnatin Isra’ila ta keta yarjejeniya wassanin Olympics da duk...
    Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qassem ya tabbatar da cewa Palasdinawa ne kawai suke da hakkin shawara kan makomar yankin zirin Gaza, da kuma abin da suke ganin ya dace da hakan, yana mai jaddada cewa mika wuya ba dabi’ar Falastinawa ba ce. Dangane da shirin shugaban Amurka Donald Trump kan zirin Gaza, Sheikh Qassem ya bayyana cewa shrin yana tattare da hadari, inda ya kara da cewa an gabatar da shi ta wani salo na musamman ga wasu kasashen Larabawa. An yi ganawa tsakanin Trump da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, kuma an yi canje-canje a cikin da suka yi daidai da mahangar Isra’ila a cikin bayanin, sabanin abin da aka sanar da kasashen larabawa da na musulmi tun...
    “Ba wani bata lokaci bane za’a fara harkar. Idan ka cancanta amma har yanzu baka nemi a baka dama ba, zaka iya neman a baka damar yin hakan. Sai ka nemi damar hakan ta https:// modeofstudy.ui.edu.ng domin ka samu digirin da yake da muhimmanci na jami’ar Ibadan.Irin tsarin karatu na UI-ODeL yana bada dama yadda za a samu koya ta fasaha da kwarewa mai amfani. “Wadanda suke da sha’awar yin karatun akwai bukatar ya samu nasara kan darussan daya rubuta jarrabawa biyar, a zama daya, ko kuma shida a rubuta jarrabawa sau biyu.” Omobowale ya kara jaddada cewar sababbi da kuma dalibai masu shiga makarantar an kaddamar da su a wurin da ake rubutar jarrabawar CBT Compled, bayan haka za...
    Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da aikin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana a Kasuwar Dutse Ultra-Modern Market, inda ya cika alkawarin gwamnatinsa na samar da tsaftataccen makamashi ga ‘yan kasuwa a jihar Jigawa.   Aikin wanda Hukumar Samar da Tattalin Arzikin Kasa da Samar da ayyukan yi ta Jihar Jigawa ta gudanar, ya hada shaguna 300 da wutar lantarki daga na’urorin hasken rana da aka sanya a cikin kasuwar, inda kowane shago kuma an saka masa fanka amfani da hasken rana kyauta.   Da yake jawabi a wajen bikin kaddamar da kasuwar a hukumance, Malam Umar Namadi ya ce shirin zai saukaka harkokin kasuwanci, da rage kashe kudi, da kuma bunkasa ribar ‘yan kasuwa.    ...
    Wata mata ta zuba wa kanta man fetur sannan ta banka wa kanta wuta a Jihar Bauchi. Matar wadda mai matsakaicin shekaru ce, ta yi wannan aika-aika ne a ƙofar gidan tsohon Fira Ministan Najeriya, Marigayi Sa Abubakar Tafawa Ɓalewa. Shaidu sun ce bayan saukar matar daga wani babur mai kafa uku, riƙe da galan ɗin man fetur a hannunta, ta nemi ganin Yelwa Abubakar, ’yar Marigayi Tafawa Ɓalewa, wadda ita ce Shugabar Hukumar Kula da Yara Masu Rauni da Marayu ta Jihar Bauchi (BASOVCA). Amma da aka shaida mata cewa Hajiya Yelwa ba ta nan, sai matar ta zuba wa kanta fetur ɗin ta kuma kiyasta wa kanta ashana a babbar ƙofar shiga gidan. Duk ƙoƙarin mutanen da ke...
    Kasashen duniya sun fara yabawa kungiyar Hamas kan amincewa da shirin zaman lafiya na Trump. Qatar mai shiga tsakanin Isra’ila da Hamas a yakin Gaza ta yaba da matakin da kungiyar ta dauka. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Qatar Maged al-Ansari, wanda kuma ya goyi bayan kiran da Donald Trump ya yi na tsagaita bude wuta ya ce ” Qatar na maraba da sanarwar da Hamas ta yi cewa ta amince da shirin na Shugaba Trump.” A nata bangare Masar tana kallon wannan a matsayin “ci gaba mai kyau.” Kuma tana fatan a sakamakon haka, bangarorin biyu “za su himmatu wajen aiwatar da shirin Shugaba Trump da kuma kawo karshen yakin,” in ji ma’aikatar harkokin wajen kasar a shafin Facebook. Ita...
    A yau Jumma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon taya murna ga Grand Duke Guillaume na Luxembourg bisa hawa karagar mulki. Xi ya yi nuni da cewa, tun bayan kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Luxembourg a cikin shekaru fiye da 50 da suka gabata, a ko da yaushe suna mutunta juna tare da daukar junansu a matsayin daidai, da kafa wani abin koyi na cimma nasarori a tsakaninsu da samun moriyar juna a tsakanin kasashen masu mabambantan girma, tsari da kuma matakan ci gaba. Kazalika, ya ce, a halin yanzu, kasashen Sin da Luxembourg sun samu kyakkyawan hadin gwiwa a fannonin karafa, kudi, harkokin jigila da dai sauransu. Yana mai cewa, “Hanyar siliki ta sufurin jiragen...
    Mutane 4 ne suka rasa rayukansu a harin da wani ya kai kan wurin bautar yahudawa a birnin Manchester na kasar Burtaniya a cikin wadanda aka kashe har da mai gadin wurin bautar. Sannan yansanda sun kashe wanda ya kai harin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyoyin labarai daga birnin Manchester, birni na 3 a girma a kasar Burtaniya na cewa , an kai harin ne a wurin bauta na yahudawa na Crumpsall a tsakiyar birnin. Hakama firai ministan kasar ta Burtaniya Keir Starmer ya yanke ziyarar aiki da yake yi a birnin Copenhegen ya dawo London don jajorantar majalisar ‘Cobra Meeting’ don tattauna baton harin. Shugaban yansanda masu yaki da ayyukan ta’addanci Lawrence Taylor ya...
    Sakatarin majalisar koli ta tsaron kasar Iran Dr Ali Larijani ya soki kasashen yamma da kokarin tursasawa Iran kan shirinta na makamashin Nukliya da kuma makamanta masu linzami. Ya maimakon su dauki hanyar tattaunawa da diblomasiyya sai sukazami hanyar tursasawan da kuma nuna karfi. Larijani ya bayyana haka ne a wata hira da yayi da wata tashar talabijin ta cikin gida. Ya kuma kara da cewa, wani abin lura a bukatun wadan nan kasashe shi ne bukatar wai dole iran ta rage nisan makamanta masu linzami zuwa kilomita 500 kacal. Larijina ya kara da cewa, kasashen yamma suna son su takaida hakkin kasar Iran ta kare kanta daga makiyanta, da sunan diblomasiyya. Sannan ya kara da cewa shirin makamai masu...
    Gwamnan jihar Zamfara, Dr. Dauda Lawal, ya kaddamar da wasu sabbin motocin alfarma masu kujeru 18 guda 50, domin inganta ayyukan zirga-zirgar jama’a na jihar.   Da yake jawabi a wajen kaddamar da bikin a Gusau, babban birnin jihar, Gwamna Lawal ya bayyana ci gaban a matsayin wani sabon babi a tarihin sufuri na Zamfara.     A cewar Gwamnan, motocin bas din suna da kayan kariya na zamani da na jin dadi, wadanda suka hada da na’urorin sanyaya waje da sauran kayyakin jin dadin matafiya.   Dokta Lawal ya bayyana cewa, da gangan aka samu jinkirin tura motocin bas din bayan isowarsu, inda ya ce gwamnati ta fara samar da tsare-tsare na sa ido da kuma bin diddigi don...
    Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), ofishin Kano, ta gudanar da wani taron kara wa masu yi wa kasa hidima na NYSC aiki a karkashin Hukumar Ba da Agajin Gaggawa (EMVs).   An zabo mahalarta taron ne daga kungiyoyin ci gaban al’umma (CDS) a kananan hukumomin Tarauni da Dawakin Kudu Kano.   An tsara horon don ƙarfafa ilimin membobin ƙungiyar a matsayin wakilai na gaba na rage haɗarin bala’i da amincin al’umma.   Da yake jawabi a lokacin bada horon, shugaban ayyuka na hukumar NEMA Kano reshen jihar Jigawa, Dakta Nura Abdullahi, ya bukaci jami’an tsaro da su ci gaba da jajircewa wajen ci gaba da koyo.   Mahalarta taron sun nuna haɗin kai mai ƙarfi a duk...
    Ma’aikatar lafiya ta yankin gaza ta fadi cewa akalla sama da falasdinawa 66225  ne suka rasa rayukansu, yayin da 168938 kuma suka jikkata a aci gaba da kiran kare dangi da HKI ke yi a yankin gaza tun daga watan oktoban shekarar bara da ta gabata. Akalla fararen hula 77 ne ake kaashewa 222 kuma suke jikkata a duk rana sakamakon hare hare da sojojin Isra’ila ke kawai kan fararen hula marasa karia a yankin Gaza. Fararen hula da dama ne ciki har da mata da yara kanana suka dimauce bayan da HKI ta harba hayaki mai sa hawaye da kuma bomb na hayaki da jirgi mara matuki na HKI ya kai a makarantu da gidaje domin tarwatsa alumma dake...
    Fira ministan kasar malesiya Anwar Ibrahim da na Pakistan shehbaz sharif suna tir da matakin da HKI ta dauka kan jiragen tawagar Sumud Flotilla  ajiya Alhamisi a shafukansu na X , bayan da jagororin tawagar suka sanar da cewa sojojin HKI sun kama jiragen ruwa guda 14 dake dauke da yan kasashen waje da kayayyakin agaji zuwa yankin Gaza. Haka zalika shugaban kasar Bolivia da takwaransa na kasar Cuba  suna yi Allah wadai da Isra’ila , haka su ma ministocin harkokin wajen spaniya jose manueal dana kasar irish simon harris sun bayyana damuwarsu matuka game da halin da tawagar ta flotilla ke ciki a hannun Israi’la na kokarin hana su isa yankin gaza. Ita dai tawagar Sumud Flotilla tana dauke...
    Sule ya bayyana cewa, “ilimi shi ne abu mafi mahimmanci da gwamnatinsa ta fi mayar da hankali akai, hakan ne ya sa aka ware kashi 36 cikin 100 na kasafin kuɗin jihar na shekarar 2025 ga sashen ilimi”.   Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta dawo da tallafin karatu na ƙasashen waje, inda a halin yanzu take ɗaukar nauyin ɗalibai 155 da ke karatu a fannoni daban-daban a ƙasashe daban-daban na duniya.   Ya ƙara bayyana cewa, gwamnatin jihar na ɗaukar nauyin ɗaliban jinya da kuma wasu a jami’o’i daban-daban a faɗin ƙasar.   “Mun kuma biya kuɗin rajistar jarabawar kammala sakandire ta kasa (NECO) ta shekarar 2025 ga ɗalibai sama da 24,000 na makarantun sakandare na gwamnati, domin...
    Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijiran Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya “UNRWA” ta sanar da cewa; A kowace rana Falasdinawa guda 100 ne suke yi shahada saboda zaluncin sojojin mamayar Isra’ila Babban kwamishinan hukumar ta UNRWA Philippe Lazzarini ya bayyana cewa: A kowace rana sojojin mamayar Isra’ila suna kashe kimanin Falasdinawa 100 a zirin Gaza. Lazzarini ya ce ta hanyar dandalin X, “A takaice ana kashe mutane 100 a kowace rana a Gaza, sakamakon farmakin da sojojin mamayar Isra’ila ke kaiwa ko kuma harbe-harbe a wuraren rarraba abinci da gidauniyar agaji ta Gaza ke gudanarwa.” Ya ci gaba da cewa, “A lokaci guda kuma, wasu na mutuwa saboda yunwa ko kuma rashin kula da lafiya”. Lazzarini ya kara da cewa...
    Akalla Falasdinawa 44 ne sukayi shahada a yayin da wasu da dama suka jikkata a ranar Laraba a wasu jerin hare-haren da Isra’ila ta kai kan wasu yankuna na zirin Gaza, a cewar shaidu da majiyoyin lafiya. Sojojin Isra’ila sun yi luguden wuta kan wasu gidaje a sansanin ‘yan gudun hijira na Shati da ke birnin Gaza, inda suka kashe Falasdinawa 5 tare da jikkata wasu da dama, wasu ma sun makalle a karkashin baraguzan gine-gine. Wasu mutane 11 kuma sun yi shahada, sannan wasu da dama sun jikkata a harin bam din da aka kai a makarantar Al-Falah da ke unguwar Al-Zeitoun a kudu maso gabashin wannan birni. Makarantar tana dauke da iyalai da suka yi gudun hijira. A...
    Kungiyoyin Kare Muradun Arewa, wato Arewa Defence League, sun fitar da sanarwar da suka kira October Declaration, wadda ta tanadi matakai na gaggawa don magance matsalolin tsaro, koma bayan tattalin arziki da kalubalen rayuwa a Arewacin Najeriya. Shugaban kungiyar, Murtala Abubakar, ya bayyana hakan a taron dabarun da aka gudanar a Arewa House Kaduna, inda ya ce “lokacin alkawura marasa amfani ya wuce, wannan sanarwa kuwa ita ce alkawarinmu ga mutanen Arewa.” Ya yi gargadi kan karuwar ta’addanci da ‘yan bindiga, rashin aikin yi da kuma yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, lamarin da ya danganta da gazawar shugabanci da kuma rashin wakilci nagari. A cewarsa, kungiyar ba ta da manufar ballewa daga kasa, amma akwai gaggawar bukatar sabuwar...
    Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa, ya taya gwamnati da al’ummar Nijeriya murnar cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai, inda ya bayyana ranar a matsayin abin tunawa da hadin kai, juriya, sadaukarwa da suka gina kasar.   A sakonsa na fatan alheri, Gwamna Namadi ya ce bikin ba wai kawai lokacin yin tunani ne kan irin gwagwarmayar da iyayen da suka kafa kasar suka yi ba, har ma wata dama ce ta sabunta sadaukarwar hadin gwiwa don samar da zaman lafiya, ci gaba, da wadata.   “A yau, muna bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai cikin alfahari da godiya. Wannan ranar tana tunatar da mu sadaukarwar da jaruman mu suka yi a baya, wadanda hangen nesa...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A wannan Laraba ce wata kotu a Afirka ta Kudu ta samu madugun ‘yan adawa Julius Malema da laifin harba bindiga a bainar jama’a a shekarar 2018, hukuncin da zai iya sa a hana shi shiga majalisar. Malema ya harba bindiga sama a lokacin bikin cikar shkaru biyar da kafa jam’iyyar Economic Freedom Fighters (EFF)  a lardin Eastern Cape, wanda ya saba wa dokar hana sarrafa bindigogi. Idan har aka yanke masa hukuncin zaman gidan yari, Malema, wanda ya shafe sama da shekaru 10 yana dan majalisa, za a dakatar da shi  daga ci gaba da zama mamba a majalisar dokoki a karkashin kundin tsarin mulkin kasa. A rahoton kamfanin dillancin labaran Reuters Mai shari’a Twant Olivier ta ce, kwanaki...
    Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya a Nijeriya ya jaddada ƙudirinsa na yin aiki tare da Gidauniyar Malala a ƙoƙarinta na ci gaba da bunƙasa ilimi da magance ƙalubalen da ke hana miliyoyin yara, musamman ’yan mata rashin zuwa makaranta. Da yake yi wa Malala Yousafzai  maraba a ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya, Babban jami’in kula da ayyukan jin ƙai a ofishin Mohammed Malick Fall, ya ce Majalisar Ɗinkin Duniya zata yi aiki tare da gidauniyar Malala, wacce ta samu kyautar lambar yabo ta Nobel. PENGASSAN ta dakatar da yajin aiki, ta gargaɗi mat An yi garkuwa da tsohon Shugaban SUBEB na Jihar Neja “Majalisar Ɗinkin Duniya ta sake jaddada goyon bayanta ga asusun Malala wajen ganin ‘ya’ya mata da yawa suna samun...
    Rima hassan wani bafranshe mai nuna goyon bayan falasdinu kuma mamba a majalisar tarayyar turai kuma daya daga cikin tawagar Sumud flotilla ya sanar ta kafar sada zumunta cewa gobe ne ake saran tawagar flotilla za ta isa yankin Gaza duk da yake cewa Isra’ila ta tanadi tsauraran matakai na tunkararta. A daren jiya ma isra’ila takai kai hari kan tawagar ta Flotilla , wannan ya zo ne bayan da matukan jiragen ruwa guda biyu suka fitar da bayani cewa Isra’ila ta kai harin kan jiragen ruwansu guda biyu, inda avila yace sojojin Isra’ila sun yi amfani da yakin kwakwalwa ga wasu daga cikin tawagar flotilla inda suka yi musu kawanya Agefe daya mataimakin ministan harkokin wajen kasar Austreliya ya...
    Jakadan Iran na dindin a majalisar dinkin duniya yayi kira da a gaggauta kakabawa HKI takunkumi saboda hujjoji da ake da shi dake tabbatar da cewa tana kisan gillan ne kan alumma Gaza, kuma yayi tir da matsayin kasashen turai game da abin da ke faruwa a yankin gaza. A baya bayan nan kwamitin bincike mai zaman kansa ta majalisar dinkin duniya ya fitar da sakamakon bincike da ya tabbatar da irin kisan  gillan da HKI ke yi kan alummar falasdinu ,a gefe guda kuma kasar iran shugabar yan gwagwarmaya tana goyon bayan alummar falasdinu, Tun bayan harin 7 ga watan oktoba lokacin da kungiyar Hamas ta kai hari kan HKI  mutane da dama sun nuna kin jinin gwamnatin sahyuniya...
    Kwamitin Shura na Jihar Kano, ya ta dakatar da Malam Lawan Shuaibu Triumph daga yin wa’azi har zuwa lokacin da za a kammala bincike kan zarginsa da yin ɓatanci ga Annabi Muhammad (S.A.W). Sakataren kwamitin, Alhaji Shehu Wada Sagagi ne, ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a yau Laraba. PENGASSAN ta dakatar da yajin aiki, ta gargaɗi matatar Dangote Jihar Gombe ta fara aiwatar da dokar hana kiwo da daddare “Yau mun sake yin zama domin karɓa da kuma nazarin zarge-zargen da ake yi wa Sheikh Lawal Shuaib Abubakar, wanda aka fi sani da Triumph. Mun saurari sauti da kuma kallon bidiyon da aka turo. “A cikin tattaunawarmu, mun yi bincike mai zurfi. Mun yanke cewa...
    Kwamitin Shura na Jihar Kano, ya ta dakatar da Malam Lawan Shuaibu Triumph daga yin wa’azi har zuwa lokacin da za a kammala bincike kan zarginsa da yin ɓatanci ga Annabi Muhammad (S.A.W). Sakataren kwamitin, Alhaji Shehu Wada Sagagi ne, ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a yau Laraba. PENGASSAN ta dakatar da yajin aiki, ta gargaɗi matatar Dangote Jihar Gombe ta fara aiwatar da dokar hana kiwo da daddare “Yau mun sake yin zama domin karɓa da kuma nazarin zarge-zargen da ake yi wa Sheikh Lawal Shuaib Abubakar, wanda aka fi sani da Triumph. Mun saurari sauti da kuma kallon bidiyon da aka turo. “A cikin tattaunawarmu, mun yi bincike mai zurfi. Mun yanke cewa...
    Kwamitin Shura na Jihar Kano, ya ta dakatar da Malam Lawan Shuaibu Triumph daga y’in wa’azi har zuwa lokacin da za a kammala bincike kan zarginsa da yin ɓatanci ga Annabi Muhammad (S.A.W). Sakataren kwamitin, Alhaji Shehu Wada Sagagi ne, ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a yau Laraba. PENGASSAN ta dakatar da yajin aiki, ta gargaɗi matatar Dangote Jihar Gombe ta fara aiwatar da dokar hana kiwo da daddare “Yau mun sake yin zama domin karɓa da kuma nazarin zarge-zargen da ake yi wa Sheikh Lawal Shuaib Abubakar, wanda aka fi sani da Triumph. Mun saurari sauti da kuma kallon bidiyon da aka turo. “A cikin tattaunawarmu, mun yi bincike mai zurfi. Mun yanke cewa...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Argchi ya bayyana a jiya Talata kan cewa yana dab da fara tattaunawa ta karshe dangane da shirin Snapback wanda ya maida takunkuman tattalin arziki na MDD kan kasar bayan daukewa na shekaru 10. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Aragchi yana fadar haka a birnin NewYork na kasar Amurka, a jiya Talata. Ya kuma kara da cewa tattaunawarsa da babban sakataren MDD kan shirin na Snapback na karshe. Ya ce a tattaunawar zai gabatarwa Antonio Guttres matsayin kasar Iran kan wannan matakin da kasashen E3 suka dauka a kan kasar Iran. Yace wannan ya nuna irin ketan da wadan nan kasashe sukewa JMI da kuma kiyayyar da suke nuna mata....
    Tawagar jiragen ruwan ‘Usturah’ masu rajin karya kofar ragon da aka yiwa Gaza, sun bada labarin cewa sojojin ruwa na HKI sun kai masu hare-hare a safiyar yau Laraba. Tashar talabijin ta Al-mayadeen ta bayyana cewa, majiyar ta bayyana cewa al-amarin akwai hatsari amma duk da haka zasu ci gaba da hanyarsu ta zuwa Gaza, duk tare da wadannan hattsurran. Labarin ya kara da cewa, jirgin Alman, ya gamu da hare-hare daga yahudawan wanda ya tilasta masa jada baya zuwa wani waje. Banda ya an yanke dukkan kafafen sadarwa da waje. Gwamnatin yahudawan dai sun sha alwashin hana dukkan jiragen Ustura isa gaza, kuma ta bayyana cewa ta tura jiragen ruwan yaki, wadanda suka kama dukka mutanen da suke cikin...
    Xi Jinping da sauran shugabannin sun yi tattaki zuwa gaban ginin, inda ya gyara furannin dake cikin kwandunan. Sannan ya zagaya ginin a wani mataki na nuna girmamawa. (Fa’iza Mustapha)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Tarayya ta wajabta wa ɗaliban da suka kammala karatu mika kundin bincikensu na ƙarshe a matsayin sharaɗi kafin a tura su aikin yi wa kasa hidima NYSC. Dokar za ta fara aiki ne daga ranar 6 ga Oktoba, 2025, kamar yadda Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume ya sanar. Ya bayyana cewa dokar ta shafi duk ɗaliban ajin ƙarshe da suka cancanci zuwa NYSC ko da kuwa a ƙasashen waje suka kammala karatu. Bisa haka, daga yanzu babu ɗalibin da za sahalewa zuwa NYSC ba tare da ya miƙa takardar shaidar kammala binciken karshe na kammala digirinsa ba. Gwamnatin Tarayya ta ce hakan zai taimaka wajen yakar matsalar amfani da takardun kammala karatu na bogi da kuma adana ilimi...
    Ali Larijani, sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran, wanda ya ziyarci kasar Lebanon domin halartar bikin zagayowar shahadar Sayyid Hassan Nasrallah, ya gana da babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qassem. Babban labarin jaridar Pars Today na cewa, Ali Larijani, sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran ya gana da babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qasem a ranar Lahadin da ta gabata. A wajen taron, Larijani ya jaddada goyon bayan Iran ga kasar Labanon da tsayin daka, inda ya yi misali da umarnin Imam Khumaini da Ayatullah Khamenei Jagoran juyin juya halin Musulunci tare da goyon bayan gwamnati da al’ummar Iran. Ya jaddada cewa Iran a shirye take ta ba da tallafi ga Lebanon da juriya “a kowane...
    Shugabannin ƙungiyar manyan ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Najeriya (PENGASSAN) da wakilan Matatar Dangote na halartar wani taron gaggawa tare da wakilan Gwamnatin Tarayya. Shugaban ƙungiyar PENGASSAN, Festus Osifo, tare da Babban Sakataren Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (TUC), Nuhu Toro, ne ke jagorantar ɓangaren ƙungiyoyin ƙwadago, yayin da Ministan Ƙwadago da Ayyuka, Maigari Dingyadi da wasu jami’ai ke wakiltar Gwamnatin Tarayya. Ya zama tilas ɗalibai su gabatar da ‘Project’ kafin rajistar NYSC — Tinubu Gwamnatin Tarayya ta ayyana hutu ranar Laraba Aminiya ta ruwaito cewa tun a ranar Lahadin da ta gabata ce Gwamnatin Tarayya ta gayyaci shugabannin PENGASSAN da na ɓangaren Matatar Dangote zuwa wannan taro sakamakon rikicin da ke tsakanin ɓangarorin biyu. Sai dai, duk da...
    Bana shekara ce ta cika shekaru 80 da samun nasarar yakin da al’ummar Sin suka yi da mamayar dakarun kasar Japan, da yakin duniya na kin tafarkin murdiya. Ranar 30 ga watan Satumba ita ce ranar tunawa da jarumai ta kasar. A safiyar ranar, shugaban kasar Sin Xi Jinping da sauran shugabannin JKS da na kasar, tare da wakilai daga sassa daban-daban, za su ajiye furanni don jinjinawa jarumai da suka sadaukar da rayukansu saboda kasa a filin Tian’anmen. A lokacin, babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG zai watsa wannan biki kai tsaye.(Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
    Majalisar Dinkin Duniya ta sake sanyawa Iran takunkumin rashin adalci a hukumance A hukumance Majalisar Dinkin Duniya ta sake kakabawa Iran takunkumi mai tsauri kan shirinta na makamashin nukiliya da take gudanarwa ta hanyar lumana, ta hanyar amfani da tsarin da aka fi sani da “Snapback”. Matakin na Majalisar Dinkin Duniya ya samo asali ne daga zargin karya da ake yi wa Iran na karya yarjejeniyar makamashin nukiliyar da aka kulla a shekarar 2015 da Amurka, da Birtaniya, da Rasha, da Faransa, da China da kuma Jamus. Wannan shawarar dai ta zo ne duk da irin jajircewar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi kan yarjejeniyar, da ficewar Amurka daga cikinta a shekara ta 2018, da kuma kasashen Turai uku,...
    Kasashen duniya 77 ne suka kauracewa jawabin fira ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a Majalisar Dinkin Duniya Wani bincike da Isra’ila ta gudanar ya nuna cewa kasashe 77 ne suka fice daga zauren Majalisar Dinkin Duniya a lokacin da fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benyamin Netanyahu ke jawabi ga babban zauren Majalisar a birnin New York. Jaridar Yedioth Ahronoth ta Isra’ila ta ruwaito cewa: Bayan duba kasashen da suka kaurace wa jawabin, an gano cewa: “dukkan makwaftan Isra’ila hudu, baya ga Saudiyya” na daga cikin mutane 77 da suka kauracewa taron, lamarin da ya sa Netanyahu ya yi magana a wani zauren da ke kusa da babu kowa. Sabanin haka jaridar yahudawa ta yabi wakilan Bahrain da Hadaddiyar Daular Larabawa da...
    Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bar birnin New York na Amurka, bayan kammala wakiltar Shugaba Bola Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 (UNGA). Ya nufi Jamus domin ganawa da jami’an Bankin Deutsche kan batutuwan haɗin gwuiwa da zuba jari a shirye-shiryen ci gaban Nijeriya. A yayin taron UNGA, Shettima ya samu yabo daga Sakatare-Janar na MDD, António Guterres, bisa ƙoƙarin Nijeriya na neman kujerar dindindin a Kwamitin Tsaro. Haka kuma ya gabatar da damar zuba jari a fannin makamashin mai darajar dala biliyan 200, tare da ƙarfafa haɗin gwuiwa da Birtaniya kan harkokin kasuwanci da tsaro da kuma ƙaura (ci rani). Gwamna Yusuf Ya Aike Da Sunayen Kwamishinoni Zuwa Majalisar Dokokin Jihar Kano UNGA: Tinubu Ya...
    Jami’ar Bayero Kano (BUK) da ke Kano ta sanar da korar ɗalibai 57 saboda kama su da laifuka masu nasaba da maguɗin jarrabawa. Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da darektan sashen kula da harkokin jarrabawa na jami’ar, Malam Aminu Wada Kurawa ya fitar. Nukiliya: MDD ta sake ƙaƙaba wa Iran takunkuman karayar tattalin arziki ‘Yan fashi sun sace mutum 17 a mahadar tekun Akwa Ibom da Kuros Riba Sanarwar ta ce an dakatar da wasu ƙarin mutum 8 da aka kama da laifuka masu nasaba da hakan tare da wanke ƙarin ɗalibai biyu daga zargin. Jami’ar ta ce bincike ya tabbatar da cewa ɗaliban da aka kora sun aikata laifuka daban-daban da suka shafi karya ƙa’idojin jarrabawa. Cikin wadanda...
      Kamaru Kasar Kamaru tana da alaka sosai da Isra’ila. Daraktan fannin tsaro na Cibiyar Nazarin Tsaron Kasashen Afirka da tsare-tsare a Geneba, Dabid Otto ya ce Isra’ila na kallon Kamaru a matsayin daya daga cikin kawayenta na kusa a Afirka. Ya ce “Kamaru ba za ta yi gangancin lalata alakar diflomasiyya da ke tsakaninta da Isra’ila ba.” Ya ce alakarsu na da kwari sosai, kuma ya shafi batu ne na tsaro. “Isra’ila ta taimaka sosai kuma tana ci gaba da taimakawa wajen kare gwamnatin Kamaru,” in ji shi. Isra’ila ta bayar da horo, kuma ana da amannar cewa tana ci gaba da bai wa dakaru na musamman na Kamaru horo, wani abu da ke tabbatar da tsaron shugaban kasar....
    Kamfanin dillancin labarai na WAFA ya sanar da cewa, Isra’ila ta kashe akalla wasu Falasdinawa 98 a hare-haren da ta kai a yankin Gaza da ta yi wa kawanya a baya baya nan. Hukumar ta ruwaito wasu majiyoyin lafiya na cewa an kai mutum 23 da lamarin zuwa asibitin Al-Shifa, 29 zuwa Asibitin Baftisma na Al-Ahli, 28 zuwa Asibitin Al-Awda, tara zuwa Nasser Medical Complex, sannan tara zuwa Asibitin Al-Aqsa. Tun bayan da gwamnatin Isra’ila ta kaddamar da yakin kisan kare dangi a Gaza a ranar 7 ga watan Oktoban 2023, ta kashe Falasdinawa kusan 66,000 tare da raunata fiye da 167,000, yawancinsu mata da yara. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new...
    Rahotanni sun bayyana cewa sama da mautane 77 su ne suka mutu a wani hari da HKI ta kai a yankin gaza a yau kawai, da ya hada da wani harin da takai da ya kashe mutane 11 iyalan mutum guda, Ma’aikatar lafiya ta bada rahoton cewa a ranar alhamis da ta gabata kimanin  falasdinawa 265 ne suka jikkata yayin da wasu guda 27 na daban kuma suka mutu a ci gaba da yakin da ta kaddamar kan mutanen gaza. Wasu falasdinawa guda 4 sun yi shahada ciki har da wasu guda biyu a wani hari da HKI taki da  jirgin sama mara matuki a sansanin yan gudun hijira na Nuseirat dake tsakiyar Gaza, Ya zuwa yanzu isara’ila ta kashe...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    MDD ta kara yawan sunayen kamfanonin da su ka yi aiki tare da HKI wajen keta hakkokin al’ummar Falasdinu, ta hanyar ayyukan da suke aiwatarwa a cikin sansanonin yahudawa ‘yan share wuri zauna. A cikin rumbun bayanan MDD dai an fara zayyana sunayen  kamfanoni  11, da a halin yanzu sun karu zuwa 158. Tun a shekarun baya ne dai MDD ta fara fitar da sunayen kamfanonin da suke aiki tare da HKI a wajen keta dokokin kasa da kasa da keta hakkokin al’ummar Falasdinu. Daga cikin kamfanonin bayan nan da aka  kara sunayensu da akwai  Heidelberg na kasar Jamus da kuma Ineco na kasar Spain. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies...
    Da dama daga cikin tawagogin da suke halartar taron babban zauren MDD na shekara-shekara sun fice a yayin da Fira ministan HKI ya fara jawabi, domin nuna kin amincewa da kisan kiyashin yankin Gaza. A jawabin nasa wanda tsirarun mutane su ka saurare shi, ya soki kasashen Faransa, Birtaniya, Australia da Canada da  su ka bayyana amincewarsu da kasar Falasdinu. Wani kwamiti da MDD ta kafa na bincike akan abinda yake faruwa a Gaza, ya tabbatar da cewa sojojin Isra’ila” suna aikata laifukan yaki cikin ganganci. HKI tana kara yin bakin jini a tsakanin kasashen duniya saboda yakin Gaza da kuma yadda ta ke take dokokin kasa da kasa. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Reform ya kuma ce yana shirin hana wani wanda ba dan Biritaniya ba damar samun walwala. Jam’iyyar ta yi ikirarin cewa shirin nasu zai yi tanadin fam biliyan 234 cikin shekaru da dama. Chancella Rachel Reebes ta ce tanadin da aka ba da shawarar “ba shi da tushe a zahiri” kuma tuni gwamnati ta fara duban hana walwalar bakin haure. Jagoran kawo sauyi a Burtaniya, Nigel Farage, ya ce bai kamata Birtaniya ta zama “bankin abinci na duniya ba”. Da yake kaddamar da sabbin manufofin, Farage ya ce: “Ba a gare mu ba ne mu bane a ce mutane na shigowa daga ko’ina cikin duniya.” A karkashin tsarin na yanzu, bakin haure na iya neman izinin zama na dindindin bayan...
    Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa ta karɓi ƙorafe-ƙorafe da dama da kuma martani daga ƙungiyoyin addinin Musulunci kan kalaman da Sheikh Lawan Triumph ya yi kwanan nan a jihar. A cewar sanarwar da ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar ta fitar ta hannun mai magana da yawunsa, Musa Tanko, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince a miƙa batun ga Majalisar Shura ta Jihar Kano domin yin nazari da tattaunawa. Yawan Kudin Da Aka Kashe Na Zamantakewa A Watan Agusta A Kasar Sin Ya Kai RMB Triliyan 3.97 Tinubu Ya Miƙa Saƙon Ta’aziyyar Babban Ɗan Jarida Kabir Yusuf Ƙungiyoyin da suka shigar da ƙorafe-ƙorafen sun haɗa da Safiyatul Islam of Nigeria, da Tijjaniya Youth Enlightenment Forum, da Interfaith Parties for Peace and...