2025-10-27@18:40:24 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1031
«a matsayin Mataimakin»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Sarah Mullally ta zama sabuwar Shugabar Cocin Ingila, wato Archbishop ta Canterbury, inda ta kasance mace ta farko da za ta jagoranci Cocin Ingila inda wannan muƙamin ya samo asali tun zamanin Daular Romawa da kuma al’ummar Anglican na duniya. Sarki Charles III ya amince da naɗin Mullaly bayan kwamitin da aka dora wa alhakin nemo wanda zai maye gurbin Justin Welby, wanda ya yi murabus a farkon wannan shekarar saboda wani zargi na cin zarafi, kamar yadda gwamnatin Birtaniya ta sanar a ranar Jumma’a. Cocin Ingila ita ce ta haifi ɗarikar Anglican a duniya. Mullally, mai shekaru 63, ta zama Archbishop ta Canterbury ta 106. A cikin wata sanarwa, tsohuwar ma’aikaciyar jinya ta bayyana cewa ta fahimci “babban nauyi”...
Wannan al’amari ya nuna yadda ake samun ƙarin rashin jituwa tsakanin shugabancin kamfanin da ƙungiyoyin ƙwadago, duk da cewa matatar ana ganin ta zama muhimmin ginshiƙi wajen cikar burin Nijeriya na cin gashin kai a fannin makamashi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A yau Alhamis, kamfanin sufurin jiragen kasa na kasar Sin ya bayyana cewa, layin dogo na kasar Sin ya gudanar da balaguron fasinjoji miliyan 23.13 a jiya Laraba, wato ranar farko ta hutun bikin ranar kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin da kuma bikin tsakiyar kaka na tsawon kwanaki 8. A cewar kamfanin sufurin jiragen kasan, wannan adadi ya nuna wani sabon tarihi na yawan balaguro da aka samu a rana daya. Kamfanin sufurin jiragen kasan ya yi kiyasin cewa, za a yi tafiye-tafiye miliyan 19.3 a ranar Alhamis, tare da karin jiragen kasa 1,409 da aka samar. Yayin da bikin tsakiyar kaka ya fado lokaci guda tare da ranar kafuwar PRC a wannan shekarar, ana sa ran hutun da ake...
Shugaban Colombia Gustavo Petro ya ce zai kori dukkanin jami’an diflomasiyar Isra’ila daga ƙasarsa a matsayin martani ga kama jiragen ruwa masu ɗauke da agaji zuwa Gaza. Ya kuma ya bayyana cewa an yi garkuwa da yan Colombia guda biyu. Petro babban mai caccakar yaƙin Isra’ila a Gaza, ya zargi Isra’ila da sake saɓa dokokin ƙasa da kasa inda ya buƙaci sakin su cikin gaggawa. Italiya ta kira kutsen jiragen ruwan da Isra’ila ta yi a matsayin fashin teku da kuma ta’addanci. An dai yi ƙokarin shigar da kayan agaji ne ta hanyar teku domin kaucewa shingen Isra’ila a yankin
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Alhaji Jibril Ismail Falgore, ya mika sakon taya murna ga ‘yan Najeriya a daidai lokacin da kasar ke cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Kamaluddeen Sani Shawai ya fitar, shugaban majalisar ya bayyana tafiyar Najeriya bayan samun ‘yancin kai a matsayin wanda ke cike da kalubale da dama, yana mai cewa idan aka yi hangen nesa da tsare-tsare, makoma mai haske tana nan kusa. Ya lura cewa duk da matsaloli, Najeriya a yau tana tsaye a matsayin kasa mai mutane sama da miliyan 230, galibi matasa da kuzarin da ke da karfi na musamman da kasashe da yawa ba su da su. ...
Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya taya al’ummar Jihar Nasarawa murnar cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai da kuma Jihar Nasarawa da ta cika shekara 29 da samun ‘yancin kai. Wata sanarwa da ta sanyawa hannu kuma ta raba wa manema labarai, mashawarci na musamman ga gwamna kan harkokin yada labarai Malam Ibrahim Adra ta ce al’ummar kasar nan sun samu gagarumar nasara a dukkanin bangarori na rayuwar dan Adam, haka nan kuma jihar nasarawa ta samu ribar dimokuradiyya tun bayan kafa jihar da marigayi tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha ya kafa. Sanarwar a yayin bikin murnar zagayowar ranar samun ‘yancin kai a yau, ta yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da...
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umar Bago na daga cikin wadanda suka halarci sallar jana’izar Marigayi Kyaftin Hassan Mohammed Baro, Kwamishinan dindindin a Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Neja. Sallar jana’izar wadda aka gudanar a kusa da gidan marigayin da ke Minna ta samu halartar babban daraktan kula da harkokin addini Malam Umar Faruk Abdullahi wanda ya samu halartar jama’a da dama da suka hada da mai martaba Sarkin Agaie Alh Yusuf Nuhu. Gwamnan ya kuma kasance cikin masu jajantawa a makabartar Musulmi ta Kpakungu inda aka yi jana’izar marigayi Captain Baro tare da babban limamin Minna, Malam Jibril Isah ya yi addu’ar Allah ya jikansa. Daga karshe Umar Bago ya jagoranci tawagar jihar zuwa gidan...
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta PSG, ta doke Barcelona a wasan mako na 2 na gasar Zakarun Turai a wasan da suka buga a filin wasa na Luis Companys. Ferran Torres ne ya fara jefa ƙwallon a ragar PSG a minti na 19 da fara wasan, amma gab da tafiya hutun rabin lokaci Senny Mayulu ya farkewa baƙin ƙwallonsu, yayin da Goncalo Ramos ya ci ƙwallon ƙarshe kuma wacce ta bai wa PSG nasara a mintin ƙarshe na wasan. Sojoji Sun Kashe Mayaƙan ISWAP, Sun Kama Wasu Da Miyagun Ƙwayoyi Li Qiang Ya Mika Sakon Taya Murna Ga Sabon Firaministan Algeria Da wannan nasarar da PSG ta samu ya sa ta koma matsayi na 3 a teburin gasar Zakarun Turai yayin...
A rana ta farko ta watan Oktoba, gwamnatin tarayya ta kasar Amurka ta sake tsayar da ayyukanta. Bisa binciken da CGTN ta gudanar na jin ra’ayoyi a duniya a kwanan baya tsakanin mutane 7,671 daga kasashe 38, an ce, masu bayyana ra’ayoyinsu sun nuna damuwa game da matsalar da aka samu a tsarin kasar Amurka sakamakon matsalar harkokin siyasa da sarrafa harkokin kasar, inda suka bayyana cewa, salon tsarin demokuradiyyar Amurka yana sabawa da ainihin tsarin demokuradiyya, kuma Amurka ba ta zama kasa mafi kyawun ba da jagoranci a wannan fanni ba. An sake tsayar da ayyukan gwamnatin kasar Amurka bayan shekaru 7, an samu irin hakan a baya yayin wa’adin shugaba Donald Trump karo na farko. Bisa binciken...
A yau sharhin namu zai yi muku Magana ne game amincewa da falasdinu a matsayin kasa da wasu kasashen turai suka yi a baya bayan nan ciki har da birtaniya da kasar Faransa, sai dai amincewa da kasar falasdinu ci gaba ne babba mai cike da tarihi amma haka
A yan kwanaki kin nan kasashen duniya sun fuskanci wani lamari mai jan hankali sosai, wanda ya jaddada hakkin falasdinu na kafa kasarsa mai cin gashin kai, hakika wannan lamari ya kai kololuwasa inda ya kai ga ranar litinin da ta gabata aka kira wani taro a gegen taron majalisar dinkin duniya karo na 80 domin bayyana nuna amincewa da warware rikicin falasdinu na kafa kasashen biyu masu cin gashin kansu, Akwai abubuwa guda buyi masu gayar muhimmancin da suka sanya aka gudanar da taron kafa daula biyu, na farko hakika yazo a yan kwanaki kadan sanar da shimfida taswirar hanya na kafa kasar falasdinu mai cin gashin kai bisa iyakoyin da aka cimma a wata yuni shekara ta 67...
Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojin kasar Pakistan sun bayyana cewa sun yi gwajin makami mai linzami na fatah 4 da aka kara inganta shi, wanda zai iya kai hari mai nisan kilomita 750 ba tare da wani kuskure ba, wanda ya kara inganta karfin makamai masu linzami na kasar. Babbar nasarar da aka samu wajen gwajin makamai mai linzami da aka kara inganta shi acikin gida na fatah 4,wanda aka karfafa shi da wani tsari na zamani, makamin zai iya kaucewa harin makami mai linzami na makiya ta hanyar tsarin rungumar kasa yayin da yake kai hari, Wannan wani bangare ne na karfin sojin kasar kuma da sannu za su kara inganta karfin makami mai linzami na fatah 4,...
Kyawawan sakamakon da aka samu a tsarin ci gaban kasa na shekaru biyar-biyar wanda a bana ake kammala karo na 14, sun nuna muhimmancin da ake bai wa rayuwar al’umma. A halin yanzu kasar Sin tana alfahari da tsarin kula da samar da ruwa mafi girma a duniya, inda ta mallaki manyan tafkunan adana ruwa fiye da 95,000, da manyan ayyuka 200 na janyo ruwa zuwa yankunan da ba su da shi domin aikin gona da inganta rayuwa a birane. Zuba jarin kasar a bangaren bincike da samarwa (R&D) ya karu da kashi 50%, wanda hakan ya haifar da samun nasarorin kimiyya masu yawa a cikin kasa har ma da duniya. Bangaren samar da ci gaba mara gurbata muhalli...
A yau Talata ne ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta fitar da wani kundi mai kunshe da matsayin kasar dangane da kudurin MDD mai lamba 2758. Kundin ya bayyana cewa, a ranar 25 ga watan Oktoban shekarar 1971, da babban rinjaye taron MDD na 26 ya zartar da kuduri mai lamba 2758, wanda a cikinsa aka fayyace mayar da dukkanin hakkoki ga janhuriyar jama’ar kasar Sin, da amincewa da wakilan janhuriyar jama’ar kasar Sin a matsayin wakilan kasar Sin kadai a hukumomin MDD. Wannan kundi ya kuma fayyace komai dalla-dalla, tare da warware batun wakilcin Sin, ciki har da batun yankin Taiwan, a dandalin MDD a mahanga ta siyasa, da shari’a, da matakan aiwatarwa. Kuma tabbas halasci, da inganci, da...
Wata kotu a Jihar Florida da ke ƙasar Amurka ta aike da wani mutum Craig Vogt mai shekaru 61 gidan waƙafi, bayan samunsa da laifin yanka tsuntsayen Dawisu guda biyu, sannan ya yi dabge da naman su. Hukumomin Hudson, wani yanki da ke Florida, sun cafke mutumin ne bayan an samu rahoton abin da ya aikata, wanda ya ta da hankalin maƙwabta da ya shaida musu cewa ya yanka tsuntsayen kuma ya soya har ya ɗebi dabgen. An ƙaddamar da shirin rajistar yaran da ba su zuwa makaranta a Gombe Mata masu zaman kansu za su fara biyan haraji a Nijeriya Rahotanni sun bayyana cewa, mutumin ya amince da laifinsa, yana mai cewa ya aikata hakan ne saboda ɓacin ran...
Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da uwargidansa, Sanata Oluremi Tinubu sun bayyana alhini kan kisan gillar da aka yi wa Somtochukwu ‘Sommie’ Maduagwu, waata ’yar jarida mai gabatar da labarai a gidan Talabijin na ARISE TV. A wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar, shugaba Tinubu da uwargidansa sun yi Allah-wadai da kisan, suna mai bayyana cewa a matsayin babban rashi a ƙasar da kuma fagen aikin jarida. ’Yan sanda sun cafke ababen zargi 4 a Yobe An ƙaddamar da shirin rajistar yaran da ba su zuwa makaranta a Gombe Aminiya ta ruwaito cewa, marigayiyar ta rasu ne bayan wani farmaki da ’yan fashi suka kai gidanta da ke Katampe a Abuja, a ranar Litinin da ta gabata. Tinubu...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Amurka ta kawo cikas ga yarjejeniya tsakanin Iran da Turai game da batun yin watsi da dawo da takunkumi kan Iran Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: An cimma yarjejeniya da kasashen turai dangane da yadda za’a yi watsi da batun sake dawo da takunkumi kan Iran, amma bangaren Amurka ya kawo cikas ga wannan yarjejeniya. A lokacin da ya iso filin jirgin saman Mehrabad na Iran daga birnin New York, shugaba Pezeshkian ya yi tsokaci kan ganawarsa da wasu shugabannin kasashen Turai da suka yi da ba a taba gani ba, yana mai cewa, “A birnin New York, sun tattauna da Turawa kan batutuwan da suka jibanci lamarin makamashin nukiliyar Iran,...
Jami’ar Bayero Kano (BUK) da ke Kano ta sanar da korar ɗalibai 57 saboda kama su da laifuka masu nasaba da maguɗin jarrabawa. Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da darektan sashen kula da harkokin jarrabawa na jami’ar, Malam Aminu Wada Kurawa ya fitar. Nukiliya: MDD ta sake ƙaƙaba wa Iran takunkuman karayar tattalin arziki ‘Yan fashi sun sace mutum 17 a mahadar tekun Akwa Ibom da Kuros Riba Sanarwar ta ce an dakatar da wasu ƙarin mutum 8 da aka kama da laifuka masu nasaba da hakan tare da wanke ƙarin ɗalibai biyu daga zargin. Jami’ar ta ce bincike ya tabbatar da cewa ɗaliban da aka kora sun aikata laifuka daban-daban da suka shafi karya ƙa’idojin jarrabawa. Cikin wadanda...
Firaministan Nijar Mahaman Lamine Zein ya yi Allah wadai da yadda kasashen ketare ke da hannu wajen tada zaune tsaye a yankin Sahel. Lamine Zein, ya bayyana hakan a jawabin da ya gabatar da a zauren babban taron MDD karo na 80 dake gudana a birnin New York. Nijar ta kuma yi Allah wadai da kisan kiyashin Isra’ila a Gaza, da kuma hare haren Isra’ilar kan Iran da Qatar, da kuma yadda ake nuna halin ko in kula game da rikicin Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo da Sudan dama yankin Sahel tare da hadin bakin wasu manyan kasashen yamma a nahiyar Afrika. Fira ministan na Nijar, Ya kuma kara da cewa gwamnatin Nijar da takwarorinta na Burkina da Mali, a sun sha...
Maude dan shekara 40, kwararren lauya ne, kuma haziki wanda ya kammala karatun digiri a fannin shari’a daga babbar jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria. Shi mamba ne a kungiyar lauyoyin Nijeriya da kuma a Cibiyar Masu sasantawa ta Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Da yammacin yau Asabar ne manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa Real Madrid da takwararta Athletico Madrid suka fafata wasan mako na 7 a gasar Laliga ta bana a filin wasa na Wanda Metropolitano da ke birnin Madrid. Normand na Athletico ne ya fara jefa ƙwallo a ragar Madrid kafin Mbappe ya farke a minti na 25, a minti na 36 Arder Guler ya sake jefa ƙwallo a ragar Athletico kafin Sorloth ya farke ƙwallon dab da tafiya hutun rabin lokaci. Tawagar Gwamnatin Tsakiya Na Ci Gaba Da Ziyartar Jami’ai Da Mazauna Yankuna Da Dama Na Jihar Xinjiang Masana Sun Dora Alhakin Rashin Cika Alkawuran ‘Yan Siyasa Kan Jam’iyyu Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci Julian Alvarez ya ci ƙwallaye biyu a...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jami’an ’yan sanda a Jihar Ondo sun kuɓutar da wata yarinya ’yar shekara huɗu da ta ɓace tare da gano wasu masu fataucin yara da ke gudanar da ayyukan su a yankunan Jihohin Ondo, Delta da Anambra. An fara shari’ar ne a ranar 3 ga Fabrairu, 2025, lokacin da Sunday Kingsley da ke yankin Alagbaka Extension a garin Akure, ya ruwaito cewa ’yarsa Jesinta, ta ɓace ne a lokacin da take tare da mahaifiyarta Sunday Happiness. Gwamnatin Kebbi ta sake jaddada goyon bayanta ga hukumomin tsaro Naɗin Olubadan: Tinubu da manyan jami’ai sun ziyarci Ibadan Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, Olusola Ayanlade ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar kuma aka sanarwa manema labarai a Akure ranar...
Sai kuma fannin fadada dazuzzuka da zai karu zuwa sama da kyubik mita biliyan 24, da mayar da ababen hawa masu aiki da sabbin makamashi kan gaba, cikin jimillar ababen hawa da kasar za ta rika sayarwa, da fadada kasuwar carbon ta kasar Sin, ta yadda za ta game dukkanin manyan sassan fitar da hayakin carbon, tare da kafa al’umma mai ingancin rayuwa yayin da ake tunkarar sauyin yanayi. (Mai fassara: Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A wani samame na kwanaki hudu na hadin gwiwa na yakar shaye-shayen miyagun kwayoyi da tashe-tashen hankula a kan tituna, rundunar hadin guiwa mai wanzar da zaman lafiya da farfado da matasa ta jihar Kano, ta kama wasu mutane 78 da ake zargi a manyan wuraren da ke jihar. A wata sanarwar manema labarai da jami’in hulda da jama’a na hukumar NDLEA a Kano Sadiq Mohammad Maigatari ya fitar, ya ce rundunar ta yi aiki tare da hadin gwiwar hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA da kuma rundunar ‘yan sandan Najeriya. Wannan farmakin dai ya shafi fitattun wuraren da ake aikata miyagun laifuka da suka hada da Mariri Yan’itace, Fagge, Badawa,...
Da yake magana a gaban babban zauren majalisar dinkin duniya Yarima mai jiran gado na kasar Kuwait shaikh sabah khalid al-hamad Al-sabah ya bayyana yanayin da ake ciki a yankin gaza a matsayin babban bala’I, yace alumma faladinu da basu da wani mai basu kariya suna fuskantar wahalhalu mafi muni a tarihi. Har ila yau ya kara da cewa abin da ke faruwa a Gaza kisan kare dangi ne,da kuma share kabilu, don haka wannan ba zai tafi da yin shiru ba, kana ya yi tir da harin da HKI takai kan kasar Qatar kuma yayi barazanar cewa kai hari kan daya daga cikin mambobin kungiyar hadin kan kasashen larabawa, kamar kai hari ne akan dukkansu baki daya, Yarima yayi...
A yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa da ya yi hobbasar gina Xinjiang na zamani mai ra’ayin gurguzu da ke kunshe da hadin kai, da kwanciyar hankali, da samun wadata, da arziki mai albarka, da raya al’adu da kyautata muhallin halittu, inda jama’a za su ci gaba da rayuwa da aiki cikin zaman lafiya da samun wadata. Yayin da yake sauraren rahoton ayyukan kwamitin jam’iyyar JKS a yankin Xinjiang da gwamnatin yankin a yau 24 ga wata, shugaba Xi ya jaddada cewa, wajibi ne a kafa tubalin samar da albarkatu da masana’antu, da yin nazari sosai a game da turbar samar da ci gaba mai inganci da ta dace...
Kuri’ar Jin Ra’ayoyi Ta CGTN: Mutane Sun Yaba Da Gina “Tsarin Xinjiang” A Turbar Zamanantarwar Kasar Sin
Yayin da ake cika shekaru 70 da kafuwar yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa a bana, CGTN ta gudanar da wani bincike na kuri’ar jin ra’ayoyi a duniya a kwanan baya tsakanin mutane 7,446 daga kasashe 38. Sakamakon binciken ya nuna cewa masu bayyana ra’ayoyinsu sun yaba da nasarorin da aka samu a ci gaban tattalin arziki da zamantakewar yankin na Xinjiang. An amince sosai da cewa, tsarin gudanar da mulkin Xinjiang da kasar Sin ta yi amfani da shi ya gano hanyar da ta dace wajen daidaita ci gaba da bangaren tsaro a yankunan kan iyaka, da kara kaimi ga amfani da zamanantarwar kasar Sin a yankin Xinjiang, da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa...
Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya ce a matsayin Sin na babbar kasa mai tasowa dake sauke nauyin dake wuyanta, ba za ta nemi wani sabon matsayi na musamman, ko fifiko yayin tattaunawar cimma matsaya ta yanzu, da ma ta nan gaba, dangane da harkokin kungiyar cinikayya ta duniya WTO. Li, ya yi wannan tsokaci ne yayin taron manyan jami’ai dangane da shawarar nan ta tsarin shugabanci da Sin ta gabatar, a gefen babban taron MDD karo na 80 dake gudana yanzu haka. A yau Laraba, ma’aikatar cinikayya ta Sin ta kira taron manema labarai, inda mataimakin ministan cinikayya na Sin Li Chenggang, ya bayyana wannan muhimmiyar matsaya ta Sin, a matsayin alkawari dake mayar da hankali ga yanayi da...
Babban magatakardar malajisar koli ta tsaron kasar Iran Dr. Ali Larijani ya bayyana cewa; Batun sake kakabawa Iran takunkumi yana nuni da gajiyawar kasashen turai. Dr. Ali Larijani wanda tashar talabijin din al’mayadin’ta yi hira da shi, ya kara da cewa, matakin da kasashe uku na Faransa, Birtaniya da Jamus, su ka dauka akan batun sake kakabawa Iran takunkumi, yana sake yin nuni ne da tsohuwar gabar da kasashen turai da Amurka suke da ita akan al’ummar Iran. Haka nan kuma ya ce wannan tsohuwar gaba ta yi tasiri mai girma a cikin siyasar mulkin mallaka ta kasashen turai da yadda suke son Dannen sauran kasashe. Dr. Ali Larijani ya kuma ce, wanann irin kiyayya da siyasa tana cin karo...
Kuri’ar Jin Ra’ayoyi Ta CGTN: Guguwar Amincewa Da Kasar Falasdinu Ta Nuna Yadda Amurka Da Isra’ila Suka Zama Saniyar Waren Da Ba A Taba Gani Ba
Ya zuwa ranar 23 ga watan Satumba agogon Beijing, kasashe 152 cikin 193 na Majalisar Dinkin Duniya sun amince da Falasdinu a matsayin kasa. A cikin kasashe biyar masu kujerun dindindin a kwamitin sulhun MDD, Amurka ce kadai ba ta amince da kafuwar kasar Falasdinu ba. Wannan guguwar ta amincewa da kafuwar kasar Falasdinu ta sanya Amurka da Isra’ila sun zama saniyar ware a fannin diflomasiyya game da batun rikicin Falasdinu da Isra’ila. Wata kuri’ar jin ra’ayoyin jama’a da CGTN ta gudanar a duniya ta nuna cewa kashi 78.2 cikin 100 na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu sun yi imanin cewa, babbar hanyar warware matsalar Falasdinu ita ce aiwatar da shawarar “kafa kasashe biyu”, wadda kuma ita ce ginshikin samar da...
Xi Jinping Zai Halarci Bikin Murnar Cika Shekaru 70 Da Kafuwar Yankin Xinjiang Na Uygur Mai Cin Gashin Kansa
A ranar Alhamis 25 ga watan nan, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci wani babban taro a birnin Urumqi, babban birnin yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa, domin murnar cika shekaru 70 da kafuwar yankin. An shirya fara bikin da shugaba Xi zai halarta da karfe 10:30 na safiyar Alhamis, kuma babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) da dandalin shafin intanet na kamfanin dillancin labarai na kasar Sin (Xinhuanet) za su watsa shi kai-tsaye. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta yi wa tsohon Ministan Shari’a kuma Antoni-Janar na Gwamnatin Tarayya, Abubakar Malami, tambayoyi a kan harin da aka kai wa ayarin motocinsa a Jihar Kebbi. An gudanar da tambayoyin ne a ofishin hukumar na Birnin Kebbi a ranar Litinin, inda Malami ya bayyana cewa an yi masa tambayoyin cikin ƙwarewa da mutuntawa. A ranar 1 ga Satumba, 2025 ne aka kai wa ayarin motocin da ke rakiyar Malami hari a Birnin Kebbi, bayan ya dawo daga gaisuwar ta’aziyya ga iyalan marigayi Babban Limamin Masallacin Dakta Bello Haliru Jumu’a. Shaidu sun bayyana cewa an lalata motocin rakiyarsa kusan guda 10, sannan da dama daga cikin magoya bayansa sun jikkata. Burkina Faso, Mali da Nijar...
Rahotanni sun bayyana cewa kimanin kaso 8% na mambobin majalisar dinkin diniya ne suka sanar da amincewarsu da kasar falasdinu, a daidai lokacin da Isra’ila take ci gaba da kisan kare dangi a Gaza kuma take kara fadada mamaye yankuna a gabar yammacin kogin jodan. Kasaashen faransa, luxambourg , malta da manako ne suka sanar da amincewa da yankin falasdinu a matsayin kasar a wajen taron babban zauren majalisar dinkin duniya, prime ministan kasar kanada marka caney ya fadi cewa amincewar tana da muhimmanci sosai, kana yayi gargadin cewa an shafe batun yancin cin gashin kai ga yankin falasdinu. Sai dai duk da amincewa da yankin na falasdinu a matsayin kasa, amma ta’addancin da Isra’ila ke yi a yankin gaza...
Ana ci gaba da takaddama a duniyar kwallon kafa kan wa ya fi cancanta da lashe kyautar Ballon d’Or a matsayin gwarzon dan wasan duniya na bana. A ranar Litinin din na za a bayar da Kyautar Ballon d’Or ta shekarar 2025 a birnin Paris na kasar Fasansa, ga wanda alakalai suka zaba a matsayin Gwarzon Dan Wasan Kwallon Kafa na Duniya. Ballon d’Or ce kyauta mafi girma ta shekara-shekara ga ’yan wasan kwalllon kafa saboda bajintar da ya nuna ga ƙungiyarsa da ƙasarsa. Gasar ta bana ta kasance mafi zafi duba da yadda alkaluma ke nuna irin zakakurancin kowanne daga manyan ’yan wasan da ake hasashen za su iya lashe kambin. An rufe sansanin NYSC da kasuwanni saboda rashin...
Ana ci gaba da takaddama a duniyar kwallon kafa kan wa ya fi cancanta da lashe kyautar Ballon d’Or a matsayin gwarzon dan wasan duniya na bana. A ranar Litinin din na za a bayar da Kyautar Ballon d’Or ta shekarar 2025 a birnin Paris na kasar Fasansa, ga wanda alakalai suka zaba a matsayin Gwarzon Dan Wasan Kwallon Kafa na Duniya. Ballon d’Or ce kyauta mafi girma ta shekara-shekara ga ’yan wasan kwalllon kafa saboda bajintar da ya nuna ga ƙungiyarsa da ƙasarsa. Gasar ta bana ta kasance mafi zafi duba da yadda alkaluma ke nuna irin zakakurancin kowanne daga manyan ’yan wasan da ake hasashen za su iya lashe kambin. An rufe sansanin NYSC da kasuwanni saboda rashin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wanda zan iya tunawa za su kai goma haka. Ko akwai wani fim wanda bayan fitar sa ka samu ƙalubale daga dangi ko wajen masu kallo? Gaskiya a fim dai har yanzu ban samu wani ƙalubale ba, saboda duk abin da nake fitowa a rol na malunta ne. Kawai dai akwai wata waƙa da na yi bidiyonta a kanta ne gaskiya na fuskanci ƙalubale sosai, dan akwai wanda ya taɓa kira na yana hawaye ya ce min me ya ja min wannan harka haka har na fito ina rawa da jaruma?. To, sai na ji ban ji daɗi ba a lokacin, dan akwai gidajen TƁ da suka karɓa suke haskawa, nayi sauri na hana a haska ɗin. Sai kuma wani...
A cewar Atiku, wannan kalmomi (ƙabilanci da yanki) an tanade su ne don raba kan jama’a da nufin cimma burinsu na siyasa ta hanyar roƙon ’yan ƙabilarsu da kada su zaɓi wani ɗan takara wanda ya fito daga wata ƙabila’ maimakon tantance shi da kyawawan halayensa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kungiyar Hizbullah ta fitar da wata sanarwa ta gayyata domin halartar taron tunawa da zagayowar ranar shahadar Sayyid Hassan Nasrallah wanda za yi a ranar 27 ga watan nan na Satumba. Tunawa da Shahid Sayyid Hassan Nasrallah da sauran wadanda su ka yi shahada a lokacin, kamar su Shahid Sayyid Hashim Safiyuddin, zai kasance a wani gagarumin taro a birnin Beirut da kuma sauran garuruwan Lebanon a ranar 27 ga watan Satumba da misalin karfe: 4;30. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Hamas...
Shugaba kuma Babban Jami’in Gudanarwa na Matatar Man Fetur na Kamfanin Dangote, Aliko Dangote, ya bayyana cewa tun bayan fara samar da man fetur a shekara guda da ta gabata, matsalar dogon layin man fetur da ta shafe shekara 50 ana fama da ita ta zama tarihi. A lokacin wani taron bita da aka gudanar don murnar cika shekara ɗaya tun bayan ƙaddamar da samar da man fetur daga masana’antar dake samar da ganga 650,000 a kowace rana, Dangote ya jaddada cewa Ƴan Nijeriya sun sha fama da dogon layin mai tun daga 1975, amma wannan matsala ta fara zuwa karshe tun lokacin da masana’antar ta fara aiki a ranar 3 ga Satumba, 2024. Dangote ya yi nuni da kalubale...
Wata mata ta haifi jarirai huɗu — maza biyu da mata biyu — a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Tarayya ta Kimiyyar Kiwon Lafiya (FUHSTHA) da ke Azare, a ranar Alhamis, 18 ga Satumba, 2025. Sakataren yaɗa labarai na asibitin, Abdu Mohammed, ya shaida wa Aminiya cewa Malama Hauwa ta haifi yaran ne ta hanyar tiyata, kuma tana ci gaba da jinya tare da ’yan huɗun. A washegarin haihuwar, Hajiya Halima Garba, matar shugaban asibitin (CMD), ta ziyarci mai jegon tare da mijinta da manyan ma’aikatan asibitin. Ta taya iyalan murna tare da addu’ar samun lafiya cikin gaggawa. ’Yan bindiga sun kashe basarake, sun tarwatsa mutane a Sakkwato Kwalara ta kashe mutane 58, wasu sun kamu a Bauchi Kamar yadda ta...
A baya, ƙasashe biyu kawai na Afirka ba sa shigo da man fetur, amma abin takaici, yanzu sun koma shigo da kaya. Wannan yana da illa ga Afirka,” in ji shi. Dangote ya bayyana cewa aikin masana’antar ya kasance mai haɗari sosai. Ya ce ya samu gargaɗi sau da dama daga masana harkokin mai, masu zuba jari, da jami’an gwamnati na cikin gida da waje, waɗanda suka yi jayayya cewa irin wannan aikin masana’antar mai girma manyan ƙasashe ne kaɗai ke iya yi, ya amince cewa da aikin ya gaza, zai rasa dukiyoyinsa ga masu ba da rance. “Yanke shawarar gina masana’antar ba abu ne mai sauƙi ba. Idan ya gaza, masu ba da rance za su daka wawa a...
An Rufe Makarantu 6 Masu Zaman Kansu A Kano Saboda Karin Kudin Makaranta Da Tilasta Iyaye Sayen Littafai
A ci gaba da kokarin da take yi na tsaftace harkar ilimi, wata kotu a Kano ta bayar da umarnin rufe wasu makarantu masu zaman kansu nan da nan, 6 saboda saba ka’idojin jihar da suka hada da kara kudin makaranta da kuma tilasta iyayen yara sayan litattafai na dole da sauran tsarabe-tsarabe da suka dorawa iyayen yara. Sakataren zartarwa na hukumar kula da cibiyoyi masu zaman kansu da sa kai na jihar Kano (KSPVIB), Kwamared Baba Abubakar Umar ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai. A cewarsa, makarantun da abin ya shafa sun hada da Prime College, Darul Ulum, Gwani Dan Zarga College, Unity Academy, Dano Memorial Academy, da Auwa Academy. ...
Tawagar gwamnatin jihar Jigawa ta shiga sahun sauran kasashe da suka halarci taron kasa da kasa na Halal da ke gudana a Malaysia (MIHAS), domin neman jari da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa na tattalin arziki. Tawagar karkashin jagorancin Kwamishinan Harkokin Kiwo, Farfesa Abdurrahman Salim Lawal, ta hada da Dr. Saifullahi Umar, Darakta-Janar na Hukumar Zamanantar da Harkar Noma ta Jihar Jigawa, da kuma Hajiya Aisha Sheik Mujaddadi, Darakta-Janar ta Hukumar Inganta Zuba Jari ta Jihar. Tuni dai tawagar ta halarci taruka daban-daban yayin isar su kasar ta Malaysia, ciki har da taron Halal Certification Convention, taron kasuwancin Halal na duniya, da MIHAS Power Talk kan zuba jari ta hanyar Halal, da kuma zaman tattaunawa kan kasuwar Halal da bada shaida....
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya ziyarci iyalan tsohon Shugaban Ƙasa, marigayi Muhammadu Buhari a Jihar Kaduna bayan halartar ɗaurin auren ɗan tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari. Da zuwansa, Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, da ɗan marigayin, Yusuf Buhari, tare da wasu suka tarbe shi. Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Game Da Bunkasa Ci Gaban Mata An Dakatar Da Shugabannin Makarantun Sakandire 6 A Sakkwato Kan Rashin Bin Dokokin Aiki Shugaba Tinubu ya gana da uwargidan marigayin, Aisha Buhari, da sauran ‘ya’yansa, inda ya sake yi musu ta’aziyya. Ya kuma tabbatar wa Aisha Buhari cewa zai ci gaba da kula da ayyukan alheri Buhari ya bari. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da...
Matatar Dangote ta sanar da dakatar da tsarin ɗaukar mai kai tsaye daga matatar, inda ya ce wannan mataki zai fara aiki daga ranar Alhamis, 18 ga Satumba, 2025. Sanarwar ta bayyana cewa matakin zai hana masu siye marasa rajista shiga wajen saye kai tsaye tare da ƙarfafa amfani da tsarin kai wa kyau bayan saye (Free Delivery Scheme). A cewar kamfanin, wannan sauyin wani gyaran aiki ne don inganta tsari, tare da tabbatar da cewa manyan cibiyoyin lafiya da muhimman wurare suna ci gaba da samun isasshen mai. Matatar Dangote ta kuma umarci a dakatar da dukkan biyan kuɗi da ya shafi ɗaukar mai kai tsaye, inda ta ce duk wani kuɗi da aka biya bayan wannan rana ba...
Sashen Raya Kimiyya Da Fasaha Na Sin Ya Kai Babban Matsayi Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-biyar Karo Na 14
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sabuwar mutum-mutumi ta fasahar AI da aka kirkira kuma aka nada mukamin minista a ƙasar Albania ta yi jawabi a karon farko a gaban majalisar dokokin kasar. A ranar Alhamis ce dai ministan ya bayyana gaban majalisar, inda ya kare rawar da zai taka a gwamnati, yana mai cewa, “Ban zo don na maye gurbin mutane ba, sai dai don taimaka musu.” Yadda jariri ya rasu a bayan mahaifiyarsa yayin tsere wa harin ’yan bindiga a Neja Gwamnatin Tarayya ta raba wa talakawa N330bn — Ministan Kuɗi Wannan minista ta AI wacce aka sanya masa suna Diella, ma’ana “rana” a harshen Albania, ita ce ministar gwamnati ta farko a duniya da aka ƙirƙira ta hanyar fasahar AI. Firaministan Albania, Edi...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN: Baje Kolin Sin Da ASEAN Ya Fadada Matsayar Bai Daya Ta Cudanyar Sassa Daban Daban
A yau Laraba ne aka bude bikin baje koli karo na 22, na Sin da kasashe membobin kungiyar ASEAN ko (CAEXPO), da kuma taron dandalin kasuwanci da juba jari na Sin da ASEAN ko CABIS, a birnin Nanning na jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kai dake kudancin kasar Sin. A shekarun baya bayan nan, Sin da kungiyar ASEAN, sun ci gaba da cimma manyan nasarori tare a fannin bunkasa dunkulewar tattalin arzikin shiyyarsu, da fadada damar bai daya ta cudanyar mabambantan sassa, a gabar da ake fuskantar yanayin tangal-tangal a duniya. Wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar, ta shaida yadda kaso 92.8 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyi suka amince...
Ma’aikatar shari’ar kasar Iran ta sanar da zartar da hukuncin kisa kan wani ba’iraniye dan leken hukumar Mossad ta Isra”ila A safiyar yau Laraba ne ma’aikatar shari’ar kasar Iran ta sanar da zartar da hukuncin kisa kan Babak Shahbazi, dan leken asirin Mossad da aka samu da laifin hada kai da yahudawan sahayoniyya a fannin leken asiri da kuma harkokin tsaro da kuma musayar bayanai da jami’an Mossad. An zartar da hukuncin kisar ta hanyar rataya a safiyar yau bayan kammala matakan shari’a kuma kotun kolin kasar ta amince da hukuncin. Babak Shahbazi, dan Rahmatullah, ya yi aiki a matsayin dan kwangilar kere-kere da sanya kayan masana’antu ga kamfanonin da ke da alaka da cibiyoyin tsaro, sojoji, da cibiyoyin sadarwa...
Sun jaddada cewa dole ne manyan kafafen sada zumunta su kare ‘yancin yin magana. Sun kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya, ‘yan jarida, da masu fafutukar kare haƙƙin bil’adama su tashi tsaye don hana abin da suka kira yunƙurin mayar da Nijeriya “mulkin kama-karya a intanet.” Lamarin ya biyo bayan wa’adin sati guda da DSS ta bai wa Sowore da ya goge wasu wasu rubuce-rubuce game da Shugaba Bola Tinubu, wanda ya ƙi amincewa. Hakan ya sa hukumar ta shigar da shi ƙara a kotu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya...
Falasdinawa 78 ne aka kashe a yau a Gaza, mafi yawansu a birnin Gaza a yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare a kasa da kuma umarnin tilastawa mazauna Gaza yin kaura. An bayar da rahoton karin mutuwar mutane uku sakamakon yunwa da killace yankin. Mazauna Gaza sun bayyana tashin bama-baman a matsayin abun tashin hankali da kuma yunkurin shafe wata al’umma. Sojojin Isra’ila sun zafafa kai hare-hare a birnin Gaza, inda suka kai hari kan unguwannin da ke da yawan jama’a. Katangar da Isra’ila ta kakaba mata da kuma karancin abinci na ci gaba da zurfafa rikicin jin kai. Yakin da Isra’ila ta kwashe watanni ana yi a Gaza ya janyo hasarar rayukan fararen hula da dama....
Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Ondo ta tabbatar da kama wata mata mai suna Iluyemi Bosede bisa zargin kashe yayarta, Tewogboye Omowumi, a Akure, babban birnin jihar. A cewar sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, Olayinka Ayanlade, ya fitar a ranar Talata, ya ce lamarin ya faru ne a ranar shida ga Satumba, 2025, bayan wata sa’insa da ta kaure tsakanin matar da marigayiyar kan Naira 800. Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya Jami’in ya bayyana cewa Bosede ta ture ’yar uwarta har ta faɗi ƙasa, lamarin da ya haifar da mutuwarta. Ya ce, “Binciken farko ya...
Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar SDP a zaben 2023, Adewole Adebayo, ya ce Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ba shi da burin da ya wuce na tara haraji tun yana Gwamna a Legas. Adebayo ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels. Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya A cewarsa, “Kowa ya san cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu sananne ne wajen karbar haraji. Amma wannan tsarin karbar haraji ya fi tsarin da ya tarar da shi wanda ba shi da tsari. “Ya yi hakan a Legas, sannan ya zo Abuja domin ya dora daga...
Ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomin Jihar Yobe (ALGON) ta karrama Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, da lambar yabo ta karramawa bisa himmar ayyukan raya ƙasa da gwamnatinsa ke gudanarwa a faɗin jihar. Karramawar, wacce aka bayyana a matsayin irinta ta farko a tarihin Jihar Yobe, shugabannin ƙananan hukumomi 17 na jihar suka ba da ita ga gwamna. Gwamnatin Kano ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tajul-Izzi kan shirya muƙabala Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno Da yake jawabi, shugaban ƙungiyar ALGON a Jihar Yobe, kuma shugaban ƙaramar hukumar Damaturu, Alhaji Bukar Adamu, ya yaba da yadda Gwamna Buni yake gudanar da harkokin mulki na bai ɗaya. Ya ce nasarorin da aka samu sun haɗa da fannoni na...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Mohammad Islami shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya na Iran ta fadi a bayan taron da hukumar ta IAEA dake gudanarwa a Vienna yanzu haka cewa yana neman hukumar ta IAEA ta goyi bayan kudurin da ta fitar kuma ta yi Tir da harin wuce gona iri da hki ta kai kan tashoshin nukiliyarta. Wakilai guda 180 a hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ne suka hallara abirnin viyana daga ranar 15-19 domin gudanar da taron kasa da kasa karo na 69 da hukumar ta duniya ke shiriya a hedkwatarta dake Vienna na kasar Austeria Yace mun bayyana cewa alummar Iran basu da rauni wajen fuskantar duk wata barazana, kuma basu da niyyar mika wuya, ,ya kara da cewa...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Matakin hana malaman da ba su da rajista hawa mumbari a Neja yana ci gaba da yamutsa hazo a ciki da wajen jihar. Yayin da wasu suke ganin wannan mataki bai dace ba, wasu kuwa gani suke faduwa ta zo daidai da zama, wato matakin ya zo a daidai lokacin da ake bukata. NAJERIYA A YAU: Yadda Wasu Al’ummomi Suke Kare Kansu Daga Barnar Ambaliyar Ruwa DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa Nayi Yunkurin Kashe Kaina Har Sau Uku Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kan tanadin Dokar Kasa game da wannan batu. Domin sauke shirin, latsa nan
Adadin mutanen da suka yi shahada sakamakon kisan kiyashin da ‘yan sahayoniyya suke yi a Gaza ya doshi 65,000 Adadin mutanen da suka yi shahada sakamakon yakin da yahudawan sahayoniyya suka kakaba wa Falasdinawa a yankin Zirin Gaza ya karu zuwa shahidai 64,871 da kuma jikkatan wasu 164,610 tun daga ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023. Bisa kididdigar baya-bayan nan da ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta fitar a zirin Gaza a ranar Lahadin da ta gabata, mutane 12,321 ne suka yi shahada yayin da wasu 52,569 suka samu raunuka tun bayan da gwamnatin mamayar Isra’ila ta sake komawa yaki kan Falasdinawa a ranar 18 ga watan Maris. A cikin sa’o’i 24 da suka gabata, Falasdinawa 68 ne suka yi...
Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Barcelona ta koma matsayi na biyu a kan teburin gasar La Liga ta Sifaniya bayan ta lallasa ƙungiyar Valencia a filin wasa na Johan Cruyff da ke birnin Barcelona. Fermin Lopez, Raphinha da Lewandowski ne suka zura ƙwallaye shida a ragar Valencia a wasan da aka buga da misalin ƙarfe 8 na dare agogon Nijeriya. Da wannan nasara, Ƙungiyar da Hansi Flick ke jagoranta ta tara maki 10 a cikin wasanni huɗu da ta buga a gasar. Kano Pillars Ta Samu Nasarar Farko A Gasar Firimiyar Nijeriya Ta Bana Rashford Na Dab Da Komawa Barcelona A Matsayin Aro An yi tsammanin Barcelona za ta fara buga wasan gidanta a sabon filin Spotify Camp Nou da aka...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ramezan sharif wani babban jami’I yace idan gwamnatin HKI ta yi kuskure kan kasar Iran, za ta fuskanci mayar da martani mai tsananin, yace ba zamu jira taimakon kowa ba wajen kare kasarmu domin muna da karfi wajen kare kasa. Da yake Magana a gaban manema labarai a wajen bikin cika shekaru 2 na ambaliyar alaqsa wanda dakarun gwagwarmayar yanto palasdinu suka kaddamar kan HKI,yace harin ya fantsama alamarin falasdinu a duniya, Har ila yau ya kara da cewa harin na 7 ga watan oktoban shekara ta 2023 ya nuna cewa isra’ila ba ta da wahalar yin galaba akanta, kuma al’ummar Palastinawa sun kuduri aniyar ci gaba da gwagwarmaya da gwamnatin mamaya da ta shafe shekaru tana aiwatar da kisan...
Bayan kwashe makonni manyan ‘yan takara a jam’iyyun adawa da sauran jiga-jigan ‘yan siyasa na tuntubar juna domin ganin an fitar da dan takara daya tilo, da yammacin ranar Asabar 13 ga watan nan na Satumba, 6 daga ciki sun amince da tsohon minista kuma mafi kusanci ga gwamnati tsawon shekaru 16, wanda ya taba zama mai magana da yawun gwamnati a matsayin wanda zai fafata da Paul Biya na jam’iyyar RDPC wanda ya kwashe sama da shekaru 42 ya na mulkin kasar da ke tsakiyar Afirka. An zabe shi ne daga cikin ‘yan takara na jam’iyyun adawa 6 cikin 12 da hukumar zabe ta tabbatar da su a matsayin wadanda suka cancanci takara, karkashin inuwar gamayyar Union du Changement....
Liɓerpool ce mai riƙe da kofin kuma na 20 jimilla da ta lashe a kakar da ta wuce, iri ɗaya da yawan wanda Manchester United take da shi a tarihin gasar premier ta ƙasar Ingila. Ga jerin ƙungiyoyin da suka ci ribar kasuwancin sayen ƴan ƙwallo da waɗanda suka yi hasara a cikin ƙungiyoyin da suke buga gasar Premier League ta bana. Ƙungiyoyin da suka ci riba; LIVERPOOL Ƙungiyar ce kan gaba a yawan kashe kuɗi wajen sayen ƴan ƙwallo a bana, wadda karo biyu ta ɗauki ƴan wasa a matakin mafi tsada a kakar nan. Ta fara da sayen matashin ɗan wasa Florian Wirtz kan fam miliyan 115, sannan ta ɗauki Aleɗander Isak kan fam miliyan 125 ranar da...
Misali, ya sauya lokacin da aka tsara yin wasan sada zumunta da ƴan ƙasa da shekara 20 na ƙungiyar Flamengo a lokacin da Leɓerkusen ta je atisaye a Brazil. An buga wasan kwana biyar kafin ranar da aka tsara tun farko, inda Leɓerkusen ta sha kashi da ci 5-1. Haka nan a kusan wannan lokacin ne Ten Hag ya yanke hukunci kan batun tafiyar Granit Ɗhaka, inda ya ce ya kamata ya tsaye saboda Leɓerkusen ta rasa manyan ƴan wasa da yawa. Sai dai tuni ƙungiyar ta sanar cewa Ɗhaka zai iya tafiya idan aka samu tayi mai kyau. Daga baya ya tafi Sunderland. Haka nan kuma Ten Hag ya soki ƴan wasansa tare da cewa ba su da kuzarin...
Amurka Ta Ce; Harin Isra’ila Kan Birnin Doha Ba Zai Shafi Kawancenta Da Gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya Ba
Amurka ta bayyana cewa: Harin da Isra’ila ta kai wa Qatar ba ya barazana ga kawancenta haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya fada a ranar Asabar din nan cewa: Harin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai a Doha babban birnin kasar Qatar a makon jiya ba zai shafi dangantakar Amurka da Isra’ila ba, duk da rashin gamsuwar da shugaba Donald Trump ya yi da yakin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke ci gaba da yi da kungiyar Hamas a Gaza. Kafin ya tashi zuwa birnin Tel Aviv na Isra’ila, Rubio ya jaddada cewa, gwamnatin Amurka na ci gaba da tallafawa yahudawan sahayoniyawa, yana mai cewa a wasu lokuta ana samun aukuwar lamarin da kan iya...
Jiragen yakin HKI sun rusa dogon gini kuma gidajen mutane Annoor dake unguwar Tel Hawa na birnin Gaza, a shirinta na rusa dukkan dogayen gine gine a birnin Gaza. Tashar talabijibijin ta presstv ya bayyana cewa sojojin yahudawan sun tilastawa dubban mutane a wasu unguwanni a birnin na Gaza kauracewa gidajen nasu a dai dai lokacin yahudawan suke ci gaba da rusa dogayen gine gine a birnin. Labarin ya kara da cewa manufar yahudawan a wadannan rushe-rushe sun hada da korar falasdinawa daga gidajensu, daga karshe korarsu daga kasarsu. Tun watan da ya gabata ne gwamnatin natanyahu ta fara aiwatar da wannan inda sojojinsa suke amfani da makamai masu karfi don cimma wannan manufar. Ya zuwa yanzo dai sun kashe...
Wani mahaifi, Mande Achagh, ya ce matsalar ta fi yin ƙamari a gundumarsa ta Agagbe, a ƙaramar hukumar Gwer West inda yawancin waɗanda basu da matsuguni suka samu mafaka, a wurare na musamman, makarantu, da kuma wasu gundumomi na al’umma. “Matsalar tafi matuƙar lalacewa a Gwer ta Yamma abin kuma ya shafi makarantu sosai. Ina fatan gwamnati zata kalli lamarin domin ta ɗauki mataki, wajen samarwa mawaɗanda suka rasa matsuguni wuraren zama ta haka ‘ya’yanmu za su iya koma harkar karatu ta amfani da azuzuwansu. “Irin matsalar da su yaran namu suke fuskanta dangane da karatunsu ba abinda za ayi wa riƙon sakainar kashi bane. Abin yana matauƙara ɓata mani rai, saboda wasu wuraren yara suna karatu ne a ƙarƙashin...
Babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ya amince da gagarimin rinjaye da “Sanarwar New York” da nufin farfado da shawarwarin samar da kasashe biyu a Gabas ta Tsakiya wato Isra’ila, da kuma Falasdinu a daya bangare – amma ba tare da kungiyar Hamas ba. Kasashe 142 ne suka amince da shi, yayin da 10 suka nuna adawa da shi (ciki har da Isra’ila da Amurka) sai 12 da suka kaurace kada kuri’ar. . Bayan shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, kasashe da dama sun bayyana aniyarsu ta daukar irin wannan matakin a babban taron Majalisar Dinkin Duniya da za a bude ranar 22 ga watan Satumba, ana kallon wannan tsari a matsayin karin tursaswa Isra’ila ta kawo karshen yakin da take ci...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhakan, sharbin bayan labarammu a yau zasu yi magana dangane da ‘yiyuwar gwamnatin kasar Qatar ta nemi maye gurbim Amurka a bangaren tsaron kasarta, bayan cin amanan da Amurka ta yi a ranar talatan da ta gabata. Kamfanin dillancin labaran Parstoday, ta nakalto wani shafin labarai na yanar gizo a Amurka ‘Axios’. A ranar Alhamis da ta gabata ce, shafin yanar gizo na Acios na labarai ya nakalto Firay ministan kasar Qatar tana fadawa fadar white House kan cewa, bayan saba alkawalin da Washington ta yi, dangane da hare-haren da HKI ta kaiwa birnin Doha, Qatar zata sake duba yarjeniyar tsaron da ke tsakaninta da Amurka ta kuma nemi sabon abokin aiki a wannan...
Akalla Falasdinawa 64,756 sukayi shahada a kisan kiyashin da Isra’ila ta yi a Gaza tun daga watan Oktoban 2023, in ji ma’aikatar lafiya a yankin Falasdinawa da ke kewaye. Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta ce an kawo gawarwakin mutane 38 da suka hada da biyu da aka zakulo daga baraguzan gine-gine a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, yayin da mutane 200 suka samu raunuka, wanda ya kawo adadin wadanda suka jikkata zuwa 164,059. Ma’aikatar ta kuma bayyana cewa, hare haren Isra’ila sun kashe Falasdinawa 14 tare da raunata wasu 143 yayin da suke neman agaji a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, lamarin da ya kai adadin Falasdinawa da aka kashe yayin da suke neman agaji zuwa 2,479,...
Mai ba da shawara ga Jagora kan harkokin kasa da kasan ya jaddada ccewa; Dole ne duniya ta daina yin shiru game da zaluncin ‘yan sahayoniyya Ali Akbar Velayati mai ba da shawara ga jagora kan harkokin kasa da kasa ya yi Allah wadai da wuce gona da irin da yahudawan sahayoniyya suka kai a kasar Qatar, yana mai cewa: Dole ne duniya ta daina yin shiru kan zaluncin yahudawan sahayoniyya saboda ba su san iyaka kan laifukansu ba. Velayati ya bayyana a shafinsa na twitter game da harin da gwamnatin ‘yan sahayoniyya suka kai wa kasar Qatar yana mai cewa: Keta dokokin kasa da kasa da keta alfarmar kasashe ya zama al’ada ga ‘yan sahayoniyya, kuma dole ne duniya...
A yau da safe, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya gudanar da jerin tarukan manema labarai mai taken “Kammala shiri na 14 na shekaru biyar-biyar na raya kasa mai inganci”, inda aka yi karin haske kan ci gaban da aka samu a fannin kafa tsarin shari’a a kasar Sin a wa’adin gudanar da shirin. An bayyana yayin taron cewa, a wa’adin shirin, hukumomin shari’a sun ci gaba da inganta tsarin kasuwanci bisa shari’a, da cibiyoyin kula da lafiyar jama’a a matakin gundumomi, kuma sun fara aiki gaba daya, kana an hukunta manyan laifuka bisa doka. Taron ya kuma bayyana kasar Sin a matsayin daya daga cikin kasashen da aka amince da su a duniya a...
“Gwamnatin Jihar Kaduna ta shirya tsaf domin ɗaukar matakin gaggawa kan kowanne yanayi da ka iya tasowa sakamakon wannan hasashen yanayi. An umurci KADSEMA da ta yi aiki tare da dukkan hukumomi masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cikakken shiri. Ana roƙon jama’a da su bi dukkan umarnin kariya, su share magudanan ruwa, kuma su guji wuraren da ambaliya ke yawan faruwa a wannan lokaci,” in ji Maiyaki. Hakazalika, sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna (KADSEMA), Dakta Usman Hayatu Mazadu, ya jaddada muhimmancin kasancewa cikin shiri da kuma bin matakan kariya da ke cikin sanarwar. “Hasashen yanayi ya nuna cewa za a samu guguwar iska da ruwan sama mai yawa musamman a ranakun Laraba...
Gwamnatin Kano ta ayyana gobe Juma’a, 12 ga watan Satumban 2025, wadda za ta yi daidai da 19 ga watan Rabi’ul Awwal na 1447, a matsayin ranar hutun Takutaha. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Sakataren Ofishin Shugaban Ma’aikatan Jihar, Salisu Mustapha, ya fitar a ranar Alhamis. Sanarwar ta bayyana cewa hutun yana cikin girmama ranar bakwai ga haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W). Daruruwan magoya bayan NNPP sun tarbi Kwankwaso a Kalaba Kotu ta yanke wa jagoran Ansaru hukuncin ɗaurin shekaru 15 “Mutanen Kano sun shafe shekaru suna bikin wannan rana a matsayin Ranar Takutaha. “Bikin Ranar Takutaha wani tsohon tarihi ne da aka shafe shekaru aru-aru ana gudanarwa.” Gwamnan ya buƙaci al’ummar jihar da su yi amfani da wannan...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran tayi Allah wadai da harin ta’addanci da hki takai kan ginin ma’aikatar sadarwa guda biyu a kasar Yaman da ya kai ga shahadar wasu yan jaridar guda biyu. Har ila yau tayi tir da hari da isra’ila takai kan muhimman wurare a kasar yamen da yankunan farafen hula ,da haka yayi sanadiyar shahadar wasu mutane kuma ya shafi wasu fararen hula na daban, don haka tayi kira ga kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya data dauki matakin gaggawa na dakatar da laifukan yaki da HKI take tafkawa. Ta ce gwamnatin Isra’ila tana ci gaba da kai hare-hare a kasashen yankin, tare da ci gaba da kisan Karen dangi a Gaza, da hakan ya sabama dan...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa, sabuwar yarjejeniyar da Iran ta kulla da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, kan batun dawo da hadin gwiwa, za ta ci gaba da wanzuwa matukar dai ba a dauki wani mataki kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba, ciki har da yunkurin mayar da takunkumin da MDD ta kakaba mata. A ranar 29 ga watan Agusta ne, kasashen Faransa, Jamus, da Biritaniya (E3) suka yunkura ganin an sake dawo da takunkumin Majalisar Dinkin Duniya da manyan takunkumin banki da na ruwa a kan Iran. Iran ta yi Allah-wadai da wannan matakin, inda ta ce kasashen uku sun bi sahun Amurka, wadda ta fice daga yarjejeniyar nukiliyar Iran a...
Shugabannin kasashen Afirka sun kammala taron kwanaki 3 kan sauyin yanayi na Afirka a babban birnin kasar Habasha a jiya Laraba tare da amincewa da sanarwar Addis Ababa, inda suka yi alkawarin mayar da nahiyar ta zama cibiyar samar da makamashi mai safta da kuma hanyoyin magance sauyin yanayi a yayin da suke neman kudade na gaske. Shugaban kasar Habasha Taye Atske Selassie, wanda ya rufe taron, ya ce taron ya nuna cewa Afirka ba ta shiga cikin rikicin da ba ta haifar da shi ba. ” Mun himmatu wajen samar da wata nahiya mai wadata,” in ji shi. “Zalunci ne cewa sama da ‘yan Afirka miliyan 600 har yanzu suna rayuwa ba tare da samun wutar lantarki ba. Dole...
Hukumar Zaɓen Nijeriya INEC ta amince da jam’iyyar ’yan haɗaka ta ADC, ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban Majalisar Dattawa, David Mark. Wannan tabbaci na zuwa ne bayan hukumar ta wallafa sunayen shugabannin jam’iyyar a shafinta na intanet, abin da ya kawo ƙarshen dogon jira da aka yi tun bayan ayyana ta a matsayin jam’iyyar haɗin kan ’yan adawa a ranar 2 ga Yuli. Masu zanga-zanga sun ƙone matar tsohon Firaministan Nepal Yadda zanga-zangar adawa da rashawa ta rikiɗe zuwa tarzoma a Nepal Tun a watan Yulin ne dai gamayyar ’yan adawa suka ayyana David Mark a matsayin shugaban jam’iyyar, tare da tsohon Gwamnan Osun, Rauf Aregbesola, a matsayin sakatarenta na ƙasa. Sai dai kafin yanzu, INEC ba ta sanya sunayensu a...
Babban Layin wutar lantarki na Najeriya ya sake faɗuwa. Wannan matsala ta haifar da katsewar wuta a wasu sassan ƙasar, wanda ya jefa masu amfani da lantarki cikin damuwa. Kotun Ghana ta ɗaure ’yan Najeriya 3 shekaru 96 saboda satar mota Mamakon ruwan sama ya hallaka mutum 3 a Zariya Bayanan da Hukumar Gudanar da Wutar Lantarki, sun nuna cewa wutar ta ragu daga megawat 2,917 zuwa megawat 1.5 daga tsakanin ƙarfe 11 na safe zuwa 12 na ranar Laraba. Kamfanin rarraba wuta na Abuja (AEDC), ya tabbatar da faruwar matsalar a saƙon da ya aike wa kwastomominsa. Ya ce wutar ta ɗauke ne sakamakon matsalar da aka samu daga layin ƙasa da misalin ƙarfe 11:23 na safe. “Saƙonmu zuwa...
Mark ya ce haɗakarsu na da burin “ceto Nujeriya, gina dimokuraɗiyya”. Manyan ‘yan siyasa a haɗakar sun haɗa da Atiku Abubakar, Peter Obi, Nasir El-Rufai, Rotimi Amaechi, Dino Melaye, Solomon Dalong. Sauran sun haɗa da Dele Momodu, Gabriel Suswam, Ireti Kingibe, Emeka Ihedioha, da Air Marshal Sadique Abubakar (ritaya). Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Babban Layin wutar lantarki na Najeriya ya sake faɗuwa. Wannan matsala ta haifar da katsewar wuta a wasu sassan ƙasar, wanda ya jefa masu amfani da lantarki cikin damuwa. Kotun Ghana ta ɗaure ’yan Najeriya 3 shekaru 96 saboda satar mota Mamakon ruwan sama ya hallaka mutum 3 a Zariya Bayanan da Hukumar Gudanar da Wutar Lantarki, sun nuna cewa wutar ta ragu daga megawat 2,917 zuwa megawat 1.5 daga tsakanin ƙarfe 11 na safe zuwa 12 na ranar Laraba. Kamfanin rarraba wuta na Abuja (AEDC), ya tabbatar da faruwar matsalar a saƙon da ya aike wa kwastomominsa. Ya ce wutar ta ɗauke ne sakamakon matsalar da aka samu daga layin ƙasa da misalin ƙarfe 11:23 na safe. “Saƙonmu zuwa...
Tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta buga kunnen doki da takwararta ta Afirika Ta Kudu da ci 1-1 a filin wasa na Toyota dake birnin Bloemfontein dake kasar Afirika Ta Kudu. Kyaftin din Nijeriya Troost Ekong shi ne ya ci gida a minti na 25 da fara wasan kafin nan dan wasan bayan Nijeriya Calvin Bassey ya farke kwallon dab da za a tafi zuwa hutun rabin lokaci. Wannan sakamakon ya sa Super Eagles din rasa tikitin kai tsaye da zai kaisu gasar Kofin Duniya, amma kuma suna da wata damar, idan sukayi kokarin karewa a mataki na biyu a rukunin C. Zuwa yanzu kasashen Moroko da Tunisia ne kawai kasashen da suka samu nasarar zuwa gasar ta Duniya da...
Sau da dama mukan ji labarai na mutane da suka ɗauki rayukansu saboda damuwa, talauci ko kuma rashin samun mafita a cikin rayuwa. A cikin wannan shirin, za mu kalli batun kisan kai daga wani ɓangare na daban, ba wai kawai daga alkaluma ba, amma ta hanyar jin labarin wani da ya taɓa yunkurin kashe kansa har sau uku. NAJERIYA A YAU: Tasirin Takaddamar NUPENG Da Dangote A Kan Tattalin Arzikin Najeriya DAGA LARABA: Yadda Matan Da Ke Auren Gwaji Suke Yamutsa Hazo ko wadanne irin matsaloli ne suka tunzura wannan bawan Allahn yunkurin daukar ransa da kansa har sau uku? Domin sauke shirin, latsa nan
Zuwa yanzu kasashen Moroko da Tunisia ne kawai kasashen da suka samu nasarar zuwa gasar ta Duniya da za a buga a kasashen Amurka, Mexico da Canada. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da su tashi tsaye wajen kare rayuka da dukiyoyin ’yan ƙasa, tare da tabbatar da cewa doka ta yi aiki a kan kowa ba tare da nuna bambanci ba. A cewarsa, hare-haren da ake kai wa jam’iyyun adawa barazana ce ga makomar dimokuraɗiyya a Nijeriya, don haka dole a yi magana a kai kafin abin ya zama al’ada. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kungiyar gwagwarmaya ta Hamas ta yi tir da shiru da kasa tabuka komai da majalisar dinkin duniya ta yi musamman ma kwamitin tsaro game da ci gaba da kisan kare dangi da HKI take ci gaba da yi kan alummar falasdinu. Wannan mayar da martani mai zafi daga hamas yana zuwa ne bayan da fira ministan isra’ila Benjamin Natanyaho yayi barazanar rusa manyan gine –gine dake gaza, da hakan ya haifar da yin kaura daga gidanjensu. Haka zalika kungiyar Hamas ta yi kira ga dukkan alummomin duniya masu yanci da su kara kaimi wajen yakar yan ta’adda yahudawa yan fashi da makami , da kuma tilasta mata dakatar da laifuffukan yaki da take tafkawa ba dare ba rana kan alummar...
Melaye ya kuma yi zargin cewa an ƙara kasafin kuɗin majalisar dokoki don yi wa shugaban ƙasa biyayya Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
An bude taron sauyin yanayi na Afirka karo na biyu a birnin Addis Ababa, na kasar Habasha mai manufar samar da hanyoyin magance matsalolin yanayi a nahiyar. Wannan taro na tsawon kwana biyu, wanda Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Afirka da gwamnatin Habasha suka shirya, na samun halartar wakilai 25,000 da kuma shugabannin kasashe 45. Haka kuma, taron na neman karfafa murya guda daya ta Afirka a fagen duniya kan rage illolin sauyin yanayi, tare da bunkasa tsare-tsaren da ke da amfani ga kasashen Afirka kafin taron COP da za a gudanar a Brazil a watan Nuwamba mai zuwa. Bayar da kudi da tabbatar da adalci na yanayi a na daga cikin ajandar babban taron. Bankin raya kasashen Afirka ya...
Kayayyakin da aka samu daga hannun wadanda ake zargin sun hada da wukake adduna almakashi, tabar wiwi, shisha, da sauran haramtattun abubuwan maye. “Ana kan binciken dukkan wadanda ake tuhuma kuma za a gurfanar da su a gaban kotu bisa laifin aikin dabanci,” in ji Abiodun. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jarin Da Sin Ta Zuba Kai Tsaye A Kasashe Cikin Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Ya Karu Da Kashi 22.9% A 2024
A yau Litinin, wasu rahotanni na cewa, yayin wani taron manema labaru na musamman kan zuba jari ga sassan ketare da aka gudanar a taron tattauna harkokin cinikayya da zuba jari na kasa da kasa na Sin karo na 25, cewa a shekarar 2024 adadin jarin da kasar Sin ta zuba kai tsaye a kasashen da suka shiga shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” ya kai dalar Amurka biliyan 50.99, adadin da ya karu da kashi 22.9 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokaci na shekarar 2023. A dai yau din, ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin, da hukumar kididdiga ta kasar, da hukumar kula da musayar kudin waje ta kasar, sun fitar da sanarwar “kididdiga ta shekarar 2024 kan...
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada yin kira ga al’ummar Musulmi cewa: Wajibi ne kasashen musulmi su yanke alakarsu da ‘yan sahayoniyya Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa: Dole ne kasashen musulmi su yanke duk wata huldar kasuwanci da siyasa da gwamnatin ‘yan sahayoniyya azzaluma tare da mayar da ita saniyar ware. Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Dole ne a fuskanci bala’o’in da muguwar gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta haifar a Gaza. Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya yi tsokaci kan mummunan halin da ake ciki a zirin Gaza inda ya ce: Dole ne kasashen da suke gudanar da zanga-zangar a yau musamman kasashen musulmi su yanke duk wata huldar kasuwanci...
Rundunar sojin Yeme ta sanar da kai hare-hare guda 8 da jirage sama marasa matuka ciki kan muhimman wurare a Isra’ila Dakarun sojin Yemen sun sanar da yammacin jiya cewa, sun kai wasu manya-manyan farmakin soji ta hanyar amfani da jiragen saman yaki marasa matuka ciki guda takwas a kan wasu wurare da dama a yankunan Falasdinawa da aka mamaye. An kai hare-haren ne kan filin jirgin saman Ramon da muhimman wurare da na sojoji da suka hada da Negev, Umm al-Rashrash, Ashkelon, Ashdod, da Jaffa. Domin jaddada goyon baya ga al’ummar Falastinu da ake zalunta da ‘yan gwagwarmayarsu masoya, da kuma mayar da martani kan laifukan kisan kiyashi da kakaba yunwa da makiya yahudawan sahayoniyya suke aikatawa kan ‘yan...
Aƙalla mutum bakwai ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu 11 suka jikkata a wani sabon hari da ’yan bindiga suka kai ƙauyen Wake da ke gundumar Agunu, a Ƙaramar Hukumar Kachia ta Jihar Kaduna. Hari ya faru ne da misalin ƙarfe 5:55 na safiyar ranar Lahadi, lokacin da ’yan bindigar suka mamaye garin, inda suka yi ta harbe-harbe. Harin Borno: Dole ’yan Najeriya su haɗa kai su fuskanci Boko Haram — Atiku Ambaliyar Ruwa: NEMA ta ceto mata 2 da jaririya a Kaduna Har ila yau, sun yi garkuwa da wasu mazauna garin, duk da cewa har yanzu ba a tantance adadinsu ba. Waɗanda suka rasu a harin sun haɗa da: Elisha Paul, Japhet Bitrus, Obadiah Joshua, Luka Augustine,...